← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 187

Sashe 71

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Danejo ba tare da fargaba sanin da gaskiyarta tabi bayan Uwaliya zuwa bangaren Hajiya Zinnia
Muje zuwa
GA MAI BUKATAR
AN TAGWAYE DUKA GUDA BIYAR 1500
GUDA HUDU 1300
GUDA UKU 1000
GUDA BIYU 700
GUDA
AYA 400
_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)
_*MUN
O*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)
_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)
_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana
iso & Jiddah Aliyu)
_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)
ACCOUNT NUMBER
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
KATIN WAYA
+234 706 528 3730
Zee Yabour
Ayusher muhd
(MAI HAKURI.....)
AYUSHER MUHD
ZEE YABOUR
Meenal abubuwa sun caku
e mata, yayin da komai baya mata dadi ta rasa mafita ko hanyar da zata bi wurin shawo matsalar da ta kunno mata kai, tana cikin tsantsar nadama na zuwanta kasar nan ba tare da ta tabbatar da wacce kasa Araab yake ba, tana kuma tsinewa Farouq tana cewa duk laifin sa ne, sam ta kasa maida hankali kan karatun, ba zata iya zama tsawon shekara a kasar ba tare da taji daga Araab ba ko ta gansa ba, kafin ta koma ma kila Mun
o ta haihu, tana tuno haka sai taji tans neman zaucewa da kishi, dan sam bata so ko mu
amalar aure ma ta shiga tsakanin su, balle har aje maganar ciki da haihuwa, ita take so ta fara haifarwa Araab magaji, tunanunka haka ke hana zuciyarta sakat da natsuwa.

Gaba
aya ta canza, damuwa da ba
inciki sun ishe ta abin takaici ma wai data
ira Farouq tana fa
a akan abinda ya mata, ce mata yai "Matsalarta ce shi ai bashi ya sata ba sannan Arab ko ya ganta ba kulata zai ba dan haka ta kyale shi taji da kanta." Tun daga nan bata sake neman shi ba abin mamaki shima bai sake nemeta ba.

Ga Mumy ta garga
eta akan in ta dawo sai ranta ya
aci, haka nan ta zauna ba abinda ke mata dadi a kasar sannan karatun ma bayi takeyi ba, sai sanda taga dama take shiga lectures, bata ta
a tunanin rayuwa zata juya mata baya haka ba.
*******************
Bilal yau kwanaki uku kenan baya gidan ya tare a gidan wani abokin sa da basu da aiki sai shaye shaye,
Baaba ya kamata yau na leka gida nasan gyatuma na nemana, dan ban ta
a kai kwanaki haka ba." Abokinshi ya zu
i tabar wiwi yana gyara zama yace
Yayi BG, sai ka dawo."
Bilal ya fito yana tangal-tangal,
ayan abokinshi ne ya saukeshi gida dan a mayen sa yake, Salame wacce duk irin rashin damuwa da shige da ficen yaranta ta shiga damuwa na rashin ji daga Bilal har na tsawon kwana uku, ta
ira wayarshi har ta gajj, shi bai saba yawon kwana haka ba.

Gashi dan wulakanci Jauro tana mai magana yana tambayata wai laifin waye?

Yau ma zaune take falo tamkar ruwa yaci ta, sai kwance wa da warwarewa takeyi akan yanda zatai Bilal ya dawo gida, kamar daga sama ya shigo falon ba sallama.

Zumbur ta mi
e tana sake kallansa,kafin ta zabga masa wata muguwar harara ganin lafiya yake, dan ita duk tsoronta kartaji wani mugun abu ne ya sameshu, rai a
ace tai taku biyu kafin tace
Gidan uban wa ka tafi har kwana uku?"
Kafa
a ya
aga yace
Inda na saba zuwa tun ina yaro, gun da bakya tambaya." Maganar tasa taji ta daketa amma ta basar tace
Ina kulolina da blender?"
"Na gaya miki ai dubu ashirin aka siya, ku
in abokina da na baki bashi ki dauka a maimakon su." Dakuwa ta masa tace
ubanka lalattace kawai, ku
i nace ina so ko kulolina dubu ashirin din banza, kasan nawa na siyesu ne?"
(Iyaye ku kula da irin furucin da kuke wa yaranku musamman uwa, bakin uwa kan kama yaranta, ya zama ko fa
a zaki ma yaro kisan irin kalaman da kike masa amfani)
Bilal cikin mayen sa yace
Kuloli sun riga sunci kasuwa, dan Allah Umma ki daina ya wa." Salame kallon sa take cikin mugun takaici tana jin kamar tayi ta zabga masa mari, ya wuce ciki ya barta a kufule, bata san ya zatayi dashi ba, ta koma ta zauna tana fa
Jauro duk ka jaza mun wannan masifa da ka wadatamu da kudi yaushe yaron nan zai
aukar mun kuloli amma ka barmu cikin talauci, kai Allah wadaran auren talaka." Tayi mugun tsaki tana karka
a kafa tamkar mai shirin dambe.

Gashi tana tsoron ta takura wa Bilal karya sake barin gida.

Tsaki ta sake ja ta cigaba da ka
a kafarta.
******************
BAYAN WATA SHIDA
Kwanaki sun wuce, awanni sun shude, inda a kwana a tashi ba wuya a wurin Allah, yanzu watan Araab shida da tafiya, yau suka kammala course
in, wanda yayi sa cikin nasara da karin ilimi sosai.

Ya ha
a dukkan takardun sa da muhimamn abubuwansa ga takardar certificate na shaidar gamawa da yai wanda zai taimaka masa gun sana'arsa.

Bayan ya koma apartment
insa ruwa ka
ai ya watsa, ya saka shirt da wando, ya fito balcony ya zauna, nan ya soma duba flight a ipad
inshi yana so yayi booking, ya samu jirgin jibi a take yayi booking yayi making payment dan zai riga Khamis komawa shi sai next week, Araab bayan ya kammala ya kira Ummy.

Tana zaune kan sallaya ta idar da sallar la
asar tana azkar na maraice, kiran ya shigo, ta dauka tare da yin sallama.

Ya amsa yace
Ummy ina wuni?

"Lafiya lau Araab, ya kasar taku?

Yace
Alhamdulillah jibi ma zamu baro ta."
"Mashaa Allahu, Allah ya dawo da kai lafiya."
Yace
Amin Ummy, akwai abinda kukeso na siyo muku ne?"
Ta girgiza kai alamamun a'a kafin tace "Ba komai burin mu ka dawo lafiya."
Yayi shiru kamar mai jira tace wani abu, itama tai
an shiru, sai kuma yace
Sai anjima."
"Toh Araab Allah ya cigaba da maka jagora." Yace
Amin
.

Ta kashe wayar.

Sauke wayar yayi daga kunnen sa yana sauke ajiyar zuciya, yau tsawon kwana hudu kenan sam bai ji daga Mun
o ba, idan ya kira karfe 9 da Ummy ta saka masa doka har tayi ringing ta gama ba
auka, yau kuma yayi mamakin da Ummy bata masa zancenta ba ko tace gata su gaisa,
Ko ta ma Ummy magana ne bata son ka a raba auren?" Cewar wani sashe na zuciyar sa, yayin da yace
Data taimaki kanta dan banasan na koma na cigaba da zama da ita, wanda nai da ya isa haka nan." Ji yai kuma ranshi ya
aci, fuska a ha
w yace "Ni ya kamata nace banayi ba ita ba, har yaushe takai?"
Sai kuma ya tuna shi ya bukaci ta fa
a wa Ummy, numfashi yaja ya sauke, ya jinginar da bayansa jikin kujera ya
an kwanta ya lumshe idanunsa yana shiga wata duniyar tunanin dashi kanshi bai sani ba.
******************
So cuta ne musamman ga mai son masu wani, Meenal ta shiga damuwa ba yar
kadan ba kuma kullum karya takewa Alhaji Hussain kan cewar suna tare da Araab har ta fara samun hankalin sa wanda hakan ba karamin dadi yake masa ba, itama Mumy ta kasa masa bayanin komai ta barshi a haka saboda tsoron hukuncin da zai biyo baya, Alhaji Hussain kullum tsara burinkan sa yake yana ganin ya kusa warkewa kasuwar sa ta kusa warware wa, dan da anyi auren Araab da Meenal yasan yasha kwana, hakan yasa yake kashe ku
i fiye da da, Mumy kullum cikin zullumi take, tana son masa magana ya rage kashe mata ku
i amma tana shakkar kar ya gano wani abun.

Kaninsa Alhaji Kabiru da Alhaji Sunusi mijin Layla har mamakin yadda yake kashe ku
i yanzu suke, nan suka fara tunanin ko ya samu wata hanya ce ta samu ku
i basu da masaniya.
**********************
o sosai ta canza kamar ba ita ba, kama daga maganarta zuwa tafiya, dressing, da komai ya canza, girki ma ta gwanance.

Fatar ta kuwa wani sheki take saboda mayuka masu tsadan da take amfani dasu da kuma wankan da take sosai yanzu, ya zamar mata jiki ma duk dare sai tayi ko da akwai sanyi sai tayi take jin da
in bacci.

Ta sake cikowa dirin ta ya fito, dukiyar fulaninta sun sake cika, dan har bra ta soma sakawa, idan ka ganta zaka rantse chanjin shekaru ne ta samu ba na watanni ba, ita kanta idan ta kalli kanta takan ce ashe na dade a duhun kauyanci da jahilci, lallai ilimi ma wani abu ne
Haka sai yanzu take jin Najah taimakonta tayi, dan da rayuwa take wata irin bahaguwa da babu tsari sam dole ma kowa ya raina ta, shiyasa Yaya Araab yake mata wani gani-gani, da gangan a kwanaki biyun nan ta tsiri rashin daukar wayar sa dan a ganinta babu amfanin cigaba da maganar su tunda rabuwa zasu yi.
Chapter 71 · 0% Book details