← Book details Mundo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 187

Sashe 5

Mundo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar zai yi
magana ya fasa, ba kasafai yake nuna fushin sa ba, balle ga mutumin
da ya girme shi baya wata magana da zata zama tamkar rashin kunya ga wanda aka ma.

Juyawa
yayi ya koma mota, Tare da danna kanta zuwa ciki, Yayi parking a wadataccen wurin da aka tanada dan parking motoci, Hannun sa ya kai kan mab'allun bud'e motar kamar wanda shocking yaja yayi saurin janyewa tare da komawa baya ya jingina da kujera ya d'an runtse idon sa tamkar mai jin rad'ad'in ciwo "DAN MACE" Kalmar da ta kasa barin k'wak'walwar sa tun d'azu, kalmar da duk sanda aka furta masa take wargaza tunani da farin cikin sa na ranar, ta saka masa b'acin rai da k'unci, a hankali ya dunkule hannunsa fuskarsa ta sake ha
ewa.

Fitowa yayi daga mota ya
an furzar da iskar bakinsa kafin ya
au jakarsa, wayarsa dake kara ya ciro daga aljihu, sunan dake jiki ne yasa ya maida ita aljihun sa ba tare da ya
aga ba.

Tun daga harabar gidan zakaga tsaruwar gidan, ga fitilu da suke haske gidan, ciki ya shiga kai tsaye.

Daga cikin gidan kuwa da gudu yan matan suka sauko kasa masu kama
aya da alama 'yan biyu ne.

Wacce ke gaba ta
oye abin hannunta tace "Dan Allah ki kyaleni na gama ba nace zan baki ba?"
"Kinsan Allah bani ai ni Ummy taba ba ke ba."
Kofar da aka bu
ene yasa suka koma sama da gudu
ayar har tana neman fa
uwa.

Wata muguwar harara ya maka musu, ya wuce ciki kai tsaye.

Da gudu suka fad'a
aki suna haki, kallon juna sukayi ta gaban tace "Ikram duk ke kika ja mana wlh kinfi kowa sanin Ya Araab ya tsani fa
an nan namu, yanzu ina zaman-zamana kija a mun fa
a ko rank'washin sa mai masifar zafi".

Cikin tsiwa wacce ta kira da Ikram tace "Dama nasan haka zakice, banda dama kinso masifar kawai dan na
au wayar Ummy sai ki biyoni?

Taki ce?"
"Ko ba tawa bace ai dai ni taba ko?"
"Ko ma dai menene kece kikaja kuma Allah Yaya ya rank'washeni sai na rama a kanki." Ikram ta fa
a tare da fitowa daga
akin cikin sanda.
*****
Cikin sauri ya shigo gida har kafafunsa na har
ewa tun kafin ya karasa shiga ya hau masifa yana kiran "Salame!

Salame!

Ke Salamatu?"
Fitowa tayi daure da zani
aure a kirjin ta tana hamma tace "Nifa na tsani ka dinga kirana haka kamar wacce naci bashi ha'a!

Nace sunana Salmah akan me zaka dinga kirana wata Salame sai kace a ruga?

Kai duk yanda akai dakai sai ka nuna asalinka." Ta karasa tana ha
e fuska.

"Yaran nan ne ya fita yanzu a mota ko?"
Ta sake yin hamma tace "Shine mana menene?

Kai wai kullum nikam abin fad'a kake nema?"
"Haka kika ce?

Yaran nan akansa kowa zagin mu yake, kinaji jiya Ina masa fa
a akan kar ya fita in har dole ne sai ya fita kada ya
aukar mun mota sanin ta'asa da jawo mana magana da yake, ko cika yan' unguwa da yake da kid'a an sha kawo mun k'orafi, amma ke ko a jikin ki wani sa'ili ma ke kika d'auko masa mukullin motar, wacce irin banzar tarbiya ce wannan".

Wata muguwar harara ta mishi tace "Silar wa muka kasance a haka ne?

Kabi ka karar da duka dukiyar mu, gidan da muka siya ka siyar, ka kawo mu nan gida kamar akurkin kaza a hakan kake so a hana shi shakatawa? da me kake so yaji dadin rayuwa bayan ga abokan sa duk suna shanawa?"
Baki ya bud'e yana kallanta yace "Mene?

Na cinye ko d'anki ya cinye?

Ko ni nabashi takardun siyar da gidan?"
D'ankwalin gaban kanta ta sake turawa gaba cikin takaici tace "Da ubansa ya wadatar dashi ai bazai d'auki abinka ya siyar ba, in ka yi zuciya kaje ka amso kudi a kauyenku ai kunada ragowar shanaye da in ka tattaro a kalla zamu samu mu bar zaman dan gidan nan." Ta karasa tana jan dogon tsaki. (Duk wannan cikin hausar su da bata gama fita ba suke yi)
"Ita kuma Fad'ima tana ina?" Takaici yasa ta sake yi mai tsaki ta wuce ciki ba tare da ta amsa mai ba.

Da kallo ya bita ranshi ya kara b'aci, wayarsa ya d'auko ya sake kiran Bilal sai dai har ta katse bai d'auka ba, komawa yayi waje ya zauna tare da dafa kansa, haka zai cigaba da rayuwa?

Yaransa duk babu mai jin maganarsa?

Ita Fad'ima yayi kwanaki bai saka ta ido ba, in yayi magana Salame ta fara masifa akan ya kawo kudi, shi kuma Bilal duk wani arzikinsu ya k'arar a shaye-shaye da bin mata, babban gidansu ma ya siyar sai wannan suka samu suka siya, anya haka zai cigaba da rayuwa?

Ko dai ya koma kauye ya roki Danejo ne akan ta taimakesu da kudi?

Kila in ya samo kudi sosai Salame ta rik'a jin maganarsa ya samu ta sa bakin wurin ganin ya daidaita rayuwar yaran sa, su natsu wuri d'aya tamkar sauran nagartattun yara.
*********
BLUES CLUB
Kid'a ke tashi ta ko'ina wanda ke ratsa har cikin dodom kunne, Ko na kusa da kai baka jin maganar sa idan ba yayi da k'arfin gaske ba, Yan' mata da maza ne cakud'e a wuri, da yawa daga ciki rawa suke cikin bad'ala suna rungumar juna, mazan daga ciki na kama k'ugun mata suna juya d'uwawu, Yayin da wasu kwalbar giya a hannun su suna kwankwad'a, Wasu kuma mazan na gefen rungume da mata suna lalubar juna, har masu shan shisha, wiwi da sigari duka akwai wurin.

'Wa'iyazubillahi'
Matashin saurayi ne mata sun kewaye shi yana taka rawa tamkar zararre, kwalbar giyar hannun sa, ya d'aga kai ya kwankwad'e sauran ya cilar a kasa, rigarsa ya zare ya cilar a kasa yabar vest ya na rawa, Matan suka hau ihu da tafi, Yana sake jin kansa sama yana juyi,
Baya yaji an ja shi da k'arfi, a fusace ya juyo ya kwashe wanda ya jawo shi da mari ba tare da ya tsaya jin dalili(kunsan yan' shaye shaye zuciyar su a wuya take) Saurayin da ya ja shi a fusace shima ya kai masa naushi, Fad'a ya kaure a tsakanin, gefen kwalbar daya fasa ya d'auka a kasa yana neman kaiwa d'ayan bugu.

Da sauri aka rik'e hannunsa, wani ya jijigashi yace "Bilal bakada hankali ne?

Kisa kake son yi?"
Fizge jikinshi yayi cikin maye yace "Ku bar ni na masa tabon da har abada ba zai sake shiga gona ta ba".

Jan shi yayi suka fita waje yace "So kake a kulle ka?

Kai wai meyasa duk sanda muka zo nan sai ka ja mana matsala?

Yanzu sai ka kawo wani abin mu basu dan suyi hakuri su barmu mu sake zuwa."
Kai ya girgiza yana layi yace "Banda komai wallahi kaima ka sani.

Ni yanzu ba wannan ba, Beb d'in ka nake so mu d'an...."
"To kace bakada komai ta ina zata bi ka?"
Hannu yasa ya ciro mukullin mota yace "Ga d'ani ka tabbatar ka dawo da ita gobe ba tawa bace ta tsoho ne kasan da ita yake neman kudi."
Cikin sauri ya amsa yace "Ai karka damu goben nan zan dawo da ita, in na dawo da ita sai na kawo ma Beb d'in."
Kai ya jinjina cikin maye yace "Yanzu ajiyeni a gida sai ka wuce da ita."
Tare suka shiga motar, dadi duk ya kama abokin, suna tafiya yace "To amma ya maganar takardun mota?

Kaga dai kar yan' road safety su kamani su tambayi takardun mota."
Ya ba je akan kujera yana sauke numfashi yace "Ba motata bace, nima banda su wannan tsohon da kake gani wayo gareshi."
Harararsa abokin yayi, suka isa layin yana saukeshi ko jiransa baiyi ba ya ja motar a guje....

Ayusher Ce
Da Zee Yabour
(MAI HAKURI)
Na Zee Yabour
Ayusher Muhd
*TEAM
AN TAGWAYE NOVEL*
Dandano page 5.......

Neman dafa gate yake cikin maye bai ankara ba yaji zai fad'i, yayi saurin mik'eqa yana d'ariya yace "Ah kai kaga wani gayu?" Yayi maganar yana dariya yana tangal tangal.

Gate aka bud'e da sauri Jairo mahaifinsa ya rike shi, ya jijjigashi yace "Yanzu Bilal bazaka ji fad'a ka daina wannan abin ba?

Wuce muje ciki kafin yan unguwa su san abinda kake aikatawa ka ja mana surutu da baki."
Ya tuntsire da dariya yana kallanshi yace "Boss kaine?

Ahhh ashe nazo gida."
Waigawa yayi yace "Ina motar da ka fita da ita?"
Kai ya girgiza yana dariya yace "Na bada aron ta..."
Ido ya zaro cikin tashin hankali ya jashi ciki, gudun maganar sa a wajen ta jawo hankalin mutanen unguwaa.

Tun a k'ofar shiga falo ya soma jijjigashi da cewa "Bakada hankali ne Bilal?

Uban wa kaba motata?"
Bilal yana dariya yace "Kai kuma dadina dakai karanta, Ba nace na bada aro ba a yanda naje
in nan ba class na kasa arar da Toyota bayan nafi karfinta."
Baki ya bud'e cikin kunar rai ya d'aga hannu zai mare shi.

"Kul kar ka sake hannun ka ya kai kan fuskar sa wallahi."
Salame wacce hayaniyarsu ta sata fitowa ta fad'a tana karasowa cikin tsiya da masifa.

Jauro ya kalleta yace "kinaji me yake cewa?"
Ta zabgamai muguwar harara tace "Karya yayi?

Karanta ce mana, motar ma har mota ce?

Bayan duk ta tsufa, meyasa kake tunanin yana shaye-shayen?

Duk ba kai kaja ba?

Da ace hankalinsa a kwance yake ai bazaiyi ba, masifar talauci da babun da muke ciki kad'ai ta isa jefa shi wani hali."
Ta karasa tana kallan Bilal tace "D'an albarka wuce muje karka fad'i." Ta rik'osa tamkar k'aramin yaro.
Chapter 5 · 0% Book details