Sashe 99
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
atare dani, bansan awani hali take a ciki ba, nayi jiran hajiya laurat shiru har yau bata neme ni ba..., bana jin zan iya barin kasar nan in har ban hadu da ita ba....." Tsananin tausayin shi ne Ya kama Daddyn nasa, "Meyasa baka fada min ba tun farkon zuwan ka"? "Banyi tunanin yin hakan ba, na bari sai in na hadu da ita sai in sanar dakai..." Murmushi sir mubarak yayi aranshi yana mai mamakin zaki, mutumin da bai ta6a ganin wata a mace Ya nuna yana son ta ba, Aikinsa kadai Yasa agaba, al'amarin so da girma ya ke... A hankali Yasa hannu ya zaro wayar shi daga aljihu, ya an daddanata, zaki dake kallon shi bai son me zaiyi ba. Kara wayar yayi a kunnansa, kafin Ya furta"Assalamu alaikum mutumina, Ina fata kana lafiya"? On the other hand muryar mutumin ta amsa masa da cewa"wa'alaikum salam! lafiyalou, Ina fata kaima haka"? "Alhamdulillah, naji muryarka kamar daga bacci ka tashi .." "No na jima da tashi, ya iyalin naka"? "Suna nan lafiya lou...Tambaya ce nake so inyi maka..." gaba daya zaki ya nutsu yana kallon sir mubarak, baisan dawa Yake magana "Ina sauraronka..." "Yar wurin Yayanka benazir da ta bace, ta dawo gida ko hanyar yanzu ba labarin ta .."? "Meyasa ka tambaye ni? "Ka fara bani amsar tambayar da nayi maka..." "Ta dawo gida..." azabure Zaki Ya mi e tsaye da alamun rudani yake kallon daddyn nashi "Nagode mutumina, Idan muka hadu zamuyi magana" "Okey saina jika" katse kiran yayi, fuskarshi dauke da murmushi Ya kalli zaki, zubewa yayi agaban daddyn nashi, ya dafe gwiwowin kafafunsa da tafukan hanneyansa "Daddy wanene ka kira a waya.. "? "Uncle dinta ne Alhaji musa, baka san cewa shi mutumin mu bane, ay da tunfarko ni ka fara tuntu6a da maganar ta, da baka sha wahalar yi ma hajiya laura magana ba..." wani irin annurin farin cikine ya bayyana akan fuskar zaki, "Idan har kana so In ha aka da ita, sai ka bani cin hanci" ya fada da zolaya "Daddy me kakeso na baka? Ka fada min koma menene...." dariya sir mubarak yayi "Farin cikin ka da kwanciyar hankalin ka nakeso .." dariya zaki yayi "Ka bani mamaki son, ji bi yadda soyayya ta jigata ka, kamar ba dan sir mubarak ba...." sunnar da kanshi kasa yayi cike da jin kunyar daddynsa "Ni kamarma na ta6a ganin yarinyar? Halan 6oye ta kake yi idan naje canada don kada na ganta ." girgiza kai yayi"a'a daddy, bana 6oyanta zaka iya saninta, duk wanda yaje gida sai yayi tsammanin yar aiki na ce, shiyasa baku ta6a lura da shakuwar dake atsakanin mu ba..." "Gaskiya zanso inji meya faru da ita? Meyasa ta gudu tabar Yarta? Amma kaima da laifinka, fisabilillah ina maka kallon uztaz ashe har mace kake 6oyo agidanka, almost 16years haba zakina! Kunyi ma kanku adalci kuwa? Da hankalin ka ka ajiye matar aure kuma kasan guduwa tayi daga gida bakayi yunkurin neman danginta ka fada masu ba!meyasa"? Ya fa a fuskarsa adaure alamar baiji dadi ba "Daddy sonta ne Ya rufe min ido na, nasan na aikata babban kuskure amma nayi nadama, kuma ni harga Allah ban ta6a neman ta ba, abun dayasa ban nemi kowa nata ba saboda ta fa amin ta tsani danginta, bata son ta dawo Nigeria, nayi kokarin shawo kanta donta amince in dawo da ita amma sai tace idan na matsa mata zata kashe kanta ne, shiyasa na kyale ta, daga baya mijinta ya turo mata sakon saki ta wayarta, daga ganin hakan saina kara samun kwarin gwiwar killace ta agidana saboda in mallake ta........." cikin sanyin murya ya kare maganar yana kallon daddyn nasa, "Kayi kuskure da baka sanar dani ba, ay da nayi maka hanyar auranta, yanzu koda ka hadu da ita zata iya bijire maka ta koma ma tsohon mijinta...." dafe kanshi yayi da hannu aya"daddy ka tayani da addu'a, Allah yasa rabona ce..." "In sha Allah zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ka samu abunda kakeso.." ajiyar zuciya ya sauke, kafin wani ya kara magana a cikin su, Sallamar hajiya turai ta katse su, atare suka amsa mata, ta shigo fuskarta dauke da murmushi"i'm sorry na katse maku firarku, my son barka dai, fatan ka tashi lafiya" da fara'a ya amsa mata"lafiyalou mommy, Kallon sir mubarak tayi"na kammala shirya mana breakfast, ka taso muje kaci kada ka makara" ruko hannun zaki yayi acikin nashi atare suka mike suka nufi dining din Adai dai lokacin, dr Jazz ya fito sanye cikin black trouser da shirt, Ya daura lapcoat akan kayansa, idanunsa manne da farin glass "Barka da safiya daddy..." "Yawwa Son, Harka shirya kenan" "Eh," Ya fa a tare da samun wuri kan dining chairs suka zauna, turai ta fara yin serving nasu "Big bro Ina kwana.." murmushi ya sakar mashi kafin yace"lafiyalou, ina fata kaima haka" ya aya masa kai alamar eh, Har sun fara cin abinci, Ibad Ya fito daga shi sai an short, "Mommy ni an manta dani, shine ba a kirani inzo inci abincin ba . " ashagwa6e yayi maganar Turai tace"sorry babyn zaki, Ay nayi zaton zaka jira ne Ya kammala in ya rage sai ka ci.." murmushi sukayi "Oh wai har yanzu bai daina wannan abi'ar ba"? Sir mubarak ya tambaya yana kallon zaki "Daddy bai daina, abun nasa kullum ara gaba yakeyi, bansan ya zanyi da shi ba, har friends dina sun gane halinsa, Na cin sauran abincin da na rage...."kallon shi sir mubarak yayi da sauri ya juya baya yana faman noke kai "Daddy pls kada kamin fa a, ni wlh na saba, kuma nafi jin dadin cin ragowar abincinsa, da i Allah" dariya suka sanya gaba dayansu "Calm down Your mind, kai fa last born ne, shalelan mommy da daddy, ba wanda zaiyi maka fa a, kayi abunda kakeso" yaji dadin maganar turai, "Zo ka zauna in zuba maka abinci.." da sauri ya samu guri ya zauna, Yana satar kallon daddyn su da jazz wanda tun ya zauna, hankalin shi baya atare da su, gangar jikinsa ce kadai atare da su ruhinsa yana wurin faryat daya kwallafa rai akai. "Jazz kaci abinci mana! Salon sai ka makara ko"? Cikin kulawa Sir mubarak yayi masa magana Kamar baisan cin abincin Ya dauki cuf of tea mai zafi Ya an kur6a "Daddy dan Allah kace ma yaya zaki mu koma toronto, ko dan saboda karatuna, in ba haka ba zaija amaida ni baya..." da damuwa akan fuskarsa yayi maganar Harara zaki ya dan watsa mashi"kada na sake ji kayi magana!..." Sir mubarak ya katse shi da cewa"ba haka yakamata kace mashi ba.." ya fa a tare da maida dubansa ga ibad wanda Ya ha e rai. "Next month zaku tafi, in sha Allah" Murmushi ibad yayi"yawwa daddy thank you.." "Wato na lura gudunmu kake Yi ibad.. "No momy wlh saboda school, kuma na manta bibina a gida..." Yana nufi magensa, mi ewa jazz yayi"zan wuce" atare suka ha a baki wurin yi mashi Allah kiyaye hanya, sai da yabi kowan nan su ya manna masu peck kafin ya tafi...... ________________________________ Tun da garin Allah ya waya, Aneeleeh ta rasa kwanciyar hankalin ta, ta kasa tsaye taka zaune kamar mai fama da ta6in hankali, tayi matu ar kagara ta kosa hajiya Saratu ta kira zahra, duk bayan yan mintuna sai ta le a dakin zahra don ta ji ko ta kirata shiru har yanzu babu wani labari, kamar yadda ta matsu haka hajiya layla ta matsu suzo da yarinyar, itace ta fara farkar da ita daga bacci da sanyin safiya ta kira ta awaya, tana kara jaddada mata akan kada ta manta tayi kokari su yi magana da iyayen yarinyar, ta rasa ya zatayi gaba daya ta daura ma kanta damuwa, daren jiya dakyar ta runtsa.. "Aunty Aneelerh"muryar zahrce ta ratsa kunnanta, Jiki na rawa ta juya da sauri ta nufi zahra dake shugowa dakin, tana sanye da hijab, hannunta ruko da wayarta... "Zahra ta kira? Ko har yanzu"? shiru zahra tayi fuskarta babu walwala.. Hakan ba karamin aga hankalin Aneelerh yayi ba "Kinyi shiru baki ce komai ba"? fuskarta dauke da matsananciyar damuwa ta furta"muyi hakuri aunty Aneelerh, ta kira tace wai yarinyar ba unaisah inmu bace....." "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Hankali atashe Aneelerh ta zabga salati tare da aura hannayenta biyu akanta "Nashiga uku zahra! Ya zanyi? Ga shi nayi masu alkawarin yau zanzo da yarinyar, dan Allah ki taimaka min zahra, ki nema mana alfarma awurin hajiya saratun su bamu aronta...." gaba daya tabi ta aga hankalin ta... "Aunty Aneelerh, ki kwantar da hankalin ki, tace muje gida mu same ta yanzu watakil ko zasu ba mu aronta ne.." nauyayyar ajiyar zuciya Aneelerh ta sauke, jiki na 6ari tace"bari na shirya sai mu tafi, mahboob Ya dawo ne"? "Bai kaiga dawo ba" amsawa tayi da toh, da sauri ta nufi toilet ta shige don tayi wanka Fitowa zahra tayi daga dakin, jikin ta duk yai sanyi, Bayan sun kammala shiryawa,sai da suka fara zuwa dakin mami suka sanar da ita kiran da hajiya saratu tayi masu, mami tace Allah Yasa muji alkhairi, idan kun isa komai ake ciki ku kira ku sanar dani,suka amsa mata da toh... Da matsakaicin gudu motarsu ta haura kan titi, Aneeleerh ce ke driving dinsu, zahara na zaune gefen ta.. "Auntyna ki bi a hankali mana, naga sai zura uban gudu kike kamar zamu tashi sama! "Ba zaki gane ba Zahra, wallahi ji nake kamar inyi fiffike in karasa estate din, gani nake kamar bana sauri, ni dai burina Allah yasa su taimaka su bamu yarinyar..." zahra ta amsa mata da ameen, Lokacin da motarsu ta karaso estate din, da sauri Aneelerh ta rage gudun motar, sunyi tsammanin security officers din zasu dakatar da su irin na jiya amma abin mamaki suna isa, da hannu sojojon suka yi masu alamar su wuce, gaba daya suka sauke ajiyar zuciya Bayan sunyi parking din motar, suka fito daga ciki, adai dai lokacin Hajiya saratu ta fito daga entry hall na gidan, ta dauki wankan leshi, idanunta sanye da farin glass Cike da zumudi suka nufeta, with respect suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu kafin tace"bismilla muje" ta nuna masu motarta da hannu, su biyu suka shiga