← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 64 OF 247

Sashe 64

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature _________________________________E21 A tsanake salsabeel ya arasa ba su labarin yana duban fuskokin su, wa anda suka ji e sharkaf da ruwan hawaye, sautin koke koken su ya cika falon, ta ko'ina shesshe ar kukan su ce, Ni kaina bazan Iya misalta zunzurutun farin cikin da ya mamaye zukatansu ba, saboda baya fa uwa abun sai wanda ya gani da idanunsa, kamar an ruke kafafuwansu sun kasa motsawa su arasa ga junansu, sai kallon an uwansu suke yi kamar yarda suma suke kallon su, ashe rai kan rai? Ashe da rabon zasu gana da junansu? Muryar na rawa suka soma ambaton sunayensu Deeja Eve Yasmin, Rubina, Hibba, Sarah Mubeen, la66ansa na kerma suke ambaton sunayensu, gaba aya rayuwar su ta prison ta dawo masu sabuwa fal acikin zukatansu wani irin tsantsar tausayin an uwansu ne ya kama su jin irin azabtuwar da su ka yi a daji. "Ba kuka yakamata kuyi ba, Allah Ya kamata ku gode mawa, da ya sake ha a ku da yan uwanku da ransu da lafiyarsu..." tun kafin Taj Ya arasa maganar, cikin sagewar gwiwa gaba aya suka zube kan gwiwowin su atare su ka yi Sujudash shukr, khadeeja ce ka ai ba tai sujjadar ba, hannayenta ru e da takalmanta da ta rungume a irjinta sai faman zare idanunta ta ke yi tana yafta su, hatta yanayin fuskanta ya canza ga dukkan alamu walwarta ce ke arin tariyo mata wani abu da ta yi loosing din shi sai dai kash ta asa tunawa sai ma kanta da ya fara juya mata. Lokacin da suka ago daga sujjadar suna yiwa Allah kirari ha i da yi mashi godiya, fuskokinsu sunyi jawur da su saboda kuka, da sauri suka fara rungumarsu a jikinsu kamar zasu mayar da su cikin su, aya bayan aya suke hugging dinsu hadi da sumbatar kuncinsu, sautin muryoyinsu masu dauke da tsantsar annurin farin ciki sun cika ko'ina na dakin, Haris sai faman tambayar deeja yakeyi wai fa bai gane ta ba, ba shi ba hatta Unaisah tambayar deeja takeyi suna ta fadin Ina deeja take bamu ganta ba .... salsabeel da ke sauraronsu dariya ce kumshe a bakinshi, Da hannu ya nuna masu ita tare da cewa"Gatanan tana kallon ku, sai kunyi hakuri da yar uwar taku, ba lallai ta gane ku ba..." tunkafin Salsabeel Ya karasa yi masu bayani haris ya nufe ta da gudu aikuwa ta watsa aguje kamar wadda taga wani mugun abu, bawan Allah kamar zai fashe da kuka saboda agarar da yayi na son ganinta, Muryar shi da shesshekar kuka yace "Deeja na kin manta ni? Ni ne fa haris dinki na gidan kurkukun addara!..." fashewa tayi da kuka, hankali ya dawo kanta murya na rawa take fadin"wallahi ba kai bane Haris dina ba, arya kake yi min ni bansan ka ba, Haris dina ba i ne ba fari ba, kuma shi ba siriri bane' gaba aya suka sanya dariya ga hawaye akan faces dinsu "Deeja ni fa baki gane ni ba"? Unaisah ce tai maganar, tana nuna mata kanta da yatsa, ma e mata kafa a khadeeja tayi"wayyo Allah ni wallahi ban san su wa ne ne ku ba, Wai ya salsabeel ba cewa kai wurin gasar kyau zaka kaimu ba to su wadanda su wanene ni sun wani tsareni da idanunsu" tana kuka ta fa "Khadeeja baki gane su ba? an uwanki ne fa" salsabeel ne ya fada yana kokarin fahimtar da ita watakil silar hakan ta dawo hayyacin ta. "Deeja haris dinki ne fa, abokin kukan ki me share maki hawayen ki, dan Allah ki tuna ni deeja, wallahi bakisan haukan rashinki da nayi ba, nayi kewarki deeja kamar zan zauce, har jinya nayi saboda ke" ta6e mashi baki tayi. "Wallahi bakai bane haris dina ba, ay shi ba haka yake ba" Dafe kan shi yai da hannu aya zuciyar shi ajagule yace "Na fahimce ki, nasan na canza kema kin canza khadeeja, Ki kalle ni da kyau ni ne dai wannan haris din naki" harara ta watsa mashi tana faman zumbura bakin ta. magiya suka dinga yi mata a karshe da sukaga bata da niyar bari su ta6a ba, aiko da gudu suka nufeta gaba daya suka auke ta suka aga ta sama suna jujjuyata, tuntana kuka tana fadin su sauke ta asa, Har dai ta fara ti ar dariya ba don ta gane su ba, sai don jin dadin abun da sukeyi mata, sauke ta kasa sukai da sauri Haris ya rungumeta ajikinshi suka ame juna, ta yi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya kamar tana son ta tuna shi sai dai takasa. o hannun Mubeen Angel tayi acikin nata, idanunsu cike tab da walla suke kallon juna, ta ji tausayin shi, ba zata ta6a manta abun da ya faru lokacin da zasu bar kurkuku addara ya yanke jiki ya fa i haka suka haura kafa suka barshi, bawan Allah ashe har ciwo yayi, Huggin dinsa tayi a kirjin ta, hannayenta daddafe da bayan shi, shima ya dafe ta cike da kaunar junansu, Hankalin danish bai kai kansu ba, ya basu ya baya, hannayen sa suna acikin na salsabeel sai faman sakar ma juna murmushi sukeyi, wani irin dadi ne Ya lullu6e kowannan su "Kaine silar komai danish" salsabeel ne ya fada yana dan bubbuga shoulder din sa alamar jinjina Duk wannan abun dake faruwa akan idon sheikh imam babu wanda Ya lura da shi, Shigowar sa kenan falon Ya taras da abun farin cikin dake faruwa hakan yasa shi tsayawa abakin kofar yana kallon abunda yai matu ar faranta ransa. Hatta Taj da big guy murmushi ne auke akan fuskokinsu, kamar wa anda akai wa albishir da gidan Aljanna babu wanda basu burge ba acikin su, sun tausayawa rayuwar su, ga wani irin son yaran da kaunar su da ya mamaye zuciyoyin su. Ummin america dake ta kallon su, idanunta sun yi jawur saboda kukan da tasha, dama ba ta jima da gama yin shi ba, gaba aya idanunsu na akan prisoners dake ta tsalle tsallen farin ciki a tsakar falon suka rurru e hannayen junansu tare da kewaye kawunansu suka ha asu guri guda gwanin ban sha'awa yadda kasan fararen furanni a garden tsabar kyan da sukayi..... Cikin Harshen Larabci sheikm Imam Ya fara karanto masu addu'o'i yayin da yake arasa shiga cikin falon gaba aya hankali ya dawo kan shi, da sauri suka raba kawunansu tare da aga hannayensu sama suna amsa mashi da ameen ameen, mutun ayane baya amsa addu'ar sheikh imam wato Danish, har Yanzu bai matsa daga gefen Salsabeel ba. Bayan ya gama jera masu addu'o'in kowan nan su Ya shafa akan fuskarsa. Kafin su sauke hannayen su, sautin takalman mutanan da ke shigowa falon taja hankalin su ga duban su Chefs din dake girka abincin gidan ne suka shigo hannayen su ru e da aton Cake stand mai hawa bakwai an awata shi yayi matu ar jan hankulan su. Bayan sun sauke masu cake din akan glass table, ba su tafi ba, tsayawa sukai don ayi shagalin da su. Cikin harshen turanci aya daga cikin chef din yace"muna tayaku murnar ha uwa da an uwanku, kuma muna tayaku murnar samun an ci arayuwar ku, sannan muna yi maku fatan Allah ya dawwamar da farin ciki arayuwarku" gaba aya suka ha a baki wurin yi masu godiya. "Bismillah, wannan na ku ne, chief ne Ya bada Umarnin A ha a maku Cake, saboda ku ji da in yin shagalin murnar ganin yan uwanku" aya daga cikin chefs dinne Ya fa a, bayin Allah saboda farin ciki hawaye ne suka cicciko idanunsu wa anda suka kumbura saboda kukan da suka sha. Hannayen su ru e cikin na juna suka kewaye Cake din, Lokaci aya wani abu ya fa o masu aransu wanda ba komai bane face farkon zuwan Sabbin prisoners gidan kurkukun addara, ba zasu ta6a mantawa da lokacin ba har abada, ranar da giants suka kawo masu cake sunata murnar yanka shi akarshe majnoon yayi ajalin shi. cikin shesshe ar kuka jemimah tace"Genie Ina majnoon ina? shi bai dawo ba? Yakamata shima Yazo tun da su deeja ma da suka mutu sun tashi" kumatunta jawur tayi maganar, gaba aya ta karya masu zuciyoyin su. "Jemimah wanda ya mutu ba ya dawowa sai dai idan dama kwanansa ne ba su are ba, Majnoob Ya mutu ba zai ta6a dawowa awannan duniyar ba, amma in sha Allah zamu ha u da shi agidan aljanna" yayin da Unaisah take yin maganar bakomai take tunawa ba face fuskar majnoon da unaizah, hakika ba zasu ta6a mantawa da farkon zuwanta gidan kurkukun addara ba, lokacin da ta sauko kan stairs cikin shiga ta school uniform red colour, ar gayu da ita wayayya ta goya back dinta abayanta. muryarta ce ta soma yi ma unaisah gizo a kunnanta. _Hi, Am unaizah ar gidan daddy, can i know u_ _that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school in ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci_ Runtse ido unaisah tayi yayin da take jin wani irin kewarta a zuciyarta, tayi fatan ace gaba ayansu ne suka rayu sai dai kash Allah baya barin wani dan wani yaji dadi. Siraran hawaye ne suka wanke fuskar Sajeed tunawa da yar uwarsa Gabriella wadda a halin Yanzu ba shi da tabbacin tana araye kota mutu, lokaci aya sautin muryarta ya soma cika kunnuwansa farkon kasancewarsu agidan kurkukun addara lokacin da za'a raba su da junansu tana kuka tace _ My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka_ Kowa da abun da yake tunawa aran shi, ganin jimamin nasu bame arewa bane yasa sheikh Imam Yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ya dinga jawo masu ayoyin kur'ani Yana fassara masu har saida yaga sun samun nutsuwa tukunna Ya dakata... "Waye zai fara Yanka mana cake din"? boss ne ya fa a yana kallon su don jin za6in su, Har suna hada baki wurin furta"Unaisah" Idanunta
Chapter 64 · 0% Book details