← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 3 OF 247

Sashe 3

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

"Me zai hana Mu yi magana dangane da matayen da muke da burin aure"? Acewar ziyad. kallon Harara Captain Ya watsa mashi"mu yi magana kan abu mai mahimmanci, Idan ba haka ba zan ja baki na nayi shiru"! "Aure shi yafi komai mahimmanci domin kuwa Sunna ce mai karfi ta Manzon Allah SAW, Allah Ya bamu komai da zamu bu ata, Kowannanmu Yana da aikin yi, Aure shi ya rage mana yakamata ku yi tunani yanzu fa lokaci ne da zamu more rayuwarmu, mu ma yi aure mu hayayyafa kamar yadda Iyayen mu suka yi.... " Ziyad ne ya kora masu jawabi. "Look, Ni aure baya a gabana yanzu, har yau banga macen data kwanta min arai na ba, tun lokacin dana rasa wadda nake da burin aure naji matan ma sun fitarmin araina" Justice Nadeem dake kallon Captain Ya saki murmushi tare da cewa"Ai ba ita kadai bace mace a family dinmu ba, Kai ma kaso ka wahalar da kanka, Ai ni tun lokacin dana fahimci macace mai izza da ji da kai, na sanyama zuciyata salama, saboda bana son macen da namiji bai isa yayi iko da ita ba, ba zata yi dadin zaman aure ba, kwara wadda zaka Iya juyawa son ranka ba wadda zaka dinga jin fargaban tunkararta ba" Ziyad yace"ka fa i gaskiya mutumina, ita fa gaba aya namiji ma baya agabanta, bata da burin yin aure, kai ma mai yaja maka yin dakon soyayyarta? Bayan Ga matasan an mata nan masu jini a jika a family namu.... " kafin Ziyad ya are maganar, Zaki yai gyaran murya tare da cewa"wai kuna Nufin Nazli"? aga mashi gira Nadeem yai, matashin murmushi ya saki kafin yace"Kuna nufin bakusan ala ar dake a tsakaninta da chief Owais namu ba"? Atare suka ha a baki wurin furta meke nan"? Jim ya anyi kafin Ya furta"Uncle Hateem, Ya riga daya mallaka mashi ita, bata da wani miji daya wuce shi a duniyar nan, tun kafin tazo duniya, wannan al awarine dake atsakanin Uncle sharafudeen da uncle Hateem, zasu ha a auran ansu... " da mamaki suke kallon shi Ziyad yace"amma ni banta6a ganin alamun suna kula junansu da sunan soyayya ba, Ko ranar Birthday din grandfa da suka ha u ko kallo ba su wa junansu ba" "Dama taya za'ai su kula juna?bayan kowannansu Yana ji da kanshi daga ita har shi Owais din, duk abunda take ta ama da shi shima Yana da shi, gaskiya Uncle sharafudeen da Hateem basu yi tunani mai kyau ba, bayan sanin cewa Izza A jinin su take, tayaya Nazli zata yi mashi biyayya amatsayin matarshi? Justice Nadeem ne yayi maganar. Captain da ke sauraransa fuskarshi babu annuri babu walwala ya furta"da ace nasan da zancen nan da tuntuni na cireta araina, dama ni ba Iyawa zanyi da ita ba, owais din shi yafi dacewa da ita, suje can su arata," Ya fa a tare da jingine kanshi jikin Sofa. Shiru suka yi na an wani lokaci, babu wanda Ya furta magana sai daga bisani Justice nadeem Ya furta"Zaki Ina budurwarka ta Canada Kyakkyawar balarabiyar nan" Da zolaya ya fa a yana duban shi. Kallo ya jefa mashi mai kama da harara kafin Ya furta"ta koma gidan su" Zaro ido justice Nadeem yayi"me? Kana nufin tabar gidanka" aga mashi gira yai alamar eh, "But why"? Bai cika son tada maganarta ba, saboda hakan Yana fama mashi raunin dake a zuciyarshi. Cikin sanyin murya ya furta"bansan meyasa ba, rana aya ta haukace min ta soma kokarin juya min ba, badan naso ba nabarta ta dawo Nigeria" Justice Yace"banji dadi ba, me zai hana ka nemi gidansu inyaso saika gabatar da kanka wurin Iyayenta"? Murmushin takaicin Zaki yayi"tana da aure har da arta, ban ta6a fada maka bane" Jin wannan maganar Yasa Captain ware manyan idanunshi, hatta Ziyad dake sauraransu saida Ya zaro ido da alamun mamakin kalaman Zaki A ru e justice Nadeem ya maimaita maganarshi"tana da aure har da a? Amma ta zauna a gidanka tsawon shekaru tamkar ma'aurata? Kafin Ya are maganar Captain Yace"tayaya hakan zai yiwu? Nima fa nasan Matar duk lokacin da zanje canada a gidan ka nake taras da ita, nayi tsammanin ar aikin ka ce, shiyasa ban ta6a kawo ma raina wani abu ba," Girgiza kai Zaki yayi"ba ar aikina bace, Taimakon ta nayi, na ru e ta agidana saboda ta nuna min bata da kowa bayan mun fara sha uwa take bani labarinta, Hankalina Ya tashi jin cewa tana da aure, amma agidana mijinta ya tura mata da sakon saki, ganin hakan yasa muka cigaba da yin rayuwarmu, naso ta amince min in aure ta saboda bani da burin daya wuce na mallake ta, nasan tana sona sai dai tafi aunar takomama mijinta saboda arta da tabar mashi" Gaba aya sun lura da canzawarshi, hakan Ya ara tabbatar masu da irin kaunar da yake yi mata. ewa yayi da sauri Ya nufi bedroom dinshi, Da sauri justice Yabi bayanshi, Yana Shiga Ya zura hannayenshi cikin aljihun short dinshi, Yayin da zuciyarshi ke cigaba da tafarfasa "Bana so hakan Ya dame ka, Yarinyar nan ko tana so ko bata so, Kai ne mijinta, Saboda kafi cutuwa, Tsawon shekara goma sha shidda kuna rayuwa agida aya tamkar ma'aurata? Ka raineta ka kashe mata ma udan kudi, Idan har ta butulce maka Allah ma bazai barta ba" Justice ne yayi maganar, yana daga tsaye abayanshi "Duk abunda nayi mata nayi ne don Allah..." kafin Ya are maganar justice yace"nasan don Allah kayi mata amma wallahi bazan bari ta karya maka zuciya ba, tun da nake da kai baka ta6a nuna kana son wata a mace ba, sai akanta, don haka dole ta aure ka, shi kuma mijinta Ya ha ura ya nemi wata, nasan ma yayi auranshi tun da jimawa" Juyawo Zaki yayi idanunsa akan justice Yace"nagode da kulawarka agare ni, amma mubar maganar, saboda hakan bamai yiwuwa bane, Ni bazan tursasa mata akan ta so ni ba, ta auke ni tamkar yayanta tana girmamani, tun da nake da ita ban ta6a nuna mata inasonta da aure ba itama haka " "Ita ai ba makauniya bace, in ba kaiba wani namijine zai dauki dawainiyar baligar mace kamarta almost 16years, idan bazan manta ba, lokacin da naje gidanka a canada, ina lura da duk wani motsinku, Idan ka shiga daki da dare zaka kwanta tana binka bata fitowa har saita tabbatar da kayi bacci take fitowa, kaima kuma haka, sannan baka Iya cin abinci idan ba atare da ita ba, itama haka, kana nufin wani abu bai ta6a shiga tsakaninku ba"? ya fa a yana bin sa da kallon tuhuma. "Nadeem, Ba abunda kake tunani bane, nasan nayi kuskure na ajiye macen da ba muharramata ba a gidana, amma wallahi ban ta6a shigarta ba..... " muryarshi na rawa ya are maganar, wani irin yanayi yake jin kanshi tunawa da rayuwarshi da ita. Numfashi yaja kafin yaci gaba dacewa"Ta saba min da kanta, komai ita take yi min, bansan menene so ba sai akanta, ban fara muradin yin aure ba sai akanta, ashe ita din ba rabona bane...." "Da ace ku i zasu Iya siyamin ita, wallahi har dukiyata zan iya salwantarwa saboda ita, bana tunanin zan samu macen da zata Iya maye min gurbinta, Ni ita kadai nakeso Nadeem" kwallar dake taruwa a cikin idanunsa har sun fara kokarin gangarowa saman kuncin sa. Hankalin Justice Ba aramin tashi yayi ba, ko a mafarki bai ta6a tunanin mace zata Iya tan wara zuciyar Zaki ba. Dafa kafadunsa yayi da hannayenshi "Inaso ka fa amin shi mijinta tsawon shekara nawa su ka yi atare"? In a low voice zaki Ya furta" asa da 2 years, ta fa a min aranar data haifa mashi baby tabar gidan badan bata son shi ba, kawai taji ya futar mata arantane" "Kasan mijin nata"? "Taya za'ai nasan shi? ni ko sunan shi ban ru e ba, saboda kishinta da nake ji" Murmushi justice yayi tare da ruko hannun Zaki, suka zaune gefen gadon shi. "Iyayenta masu hali ne"? ya jefa mashi tambayar. "Yeah, mahaifinta ya ta6a ruke mukamin Governor a jihar joss, amma bai jima a mulkin ba ya sauka sakamakon ciwon kafar dake damun shi, bayan haka anin Mahaifinta Former president ne Na nigeria, Alhaji Musa wadata, Yayan Matar Uncle sharafudeen Hajiya Laurat, nima a wurin ta naji labarin ta" jinjina kai justice yayi" ar masu Hali ce, Alhaji musan nan Yana aya daga cikin wadanda suka fi kowa ku i a africa bayan family dinmu, amma nayi mamakin da har ta gudu tabar nigeria basu nemo ta ba, meyasa tabar mijinta da arta? Shine abun tambayar" "Naikaina Labarinta Yajima Yana aure min kaina, Sonta ne Ya makantar dani shiyasa ban mayar da ita ga Iyayenta ba, saima na taimaka mata wurin 6oye kanta agidana, naci gaba da bata kulawa" Justice ya ce Labarinta Akwai ru ani Acikinsa, Ta fito daga babban family, ga ta kyakkyawa da ita amma ahaka har ta gudu daga gidan mijinta? Akan wani dalili? Me ta nema tarasa?" Ya fa a yana kallon Zaki, "Nayi kokarin nemanta don inji ya ta koma gidansu? Iyayenta sun kar6eta ko kuwa? Shine fargabana sai dai bani da hanyar da zan Iya kiranta, tabar min wayarta a hannuna, bansan kowa nata ba, in ba hajiya Laurat ba" Numfasawa Justice yayi kafin yace"kada ka damu an uwana, zan iya yin komai akanka, gobe Idan Allah yakaimu a family dinner zanyi magana da hajiyar laurat din dangane da ita Yarinyar," har cikin ranshi yaji dadin maganar justice, ya kwantar mashi da hankalin shi sosai harya fara tunanin yadda haduwarsu zata kasance da ita, sun jima adakin suna tattaunawa daga bisani suka dawo falo wurin su Captain. ______________________ A hankali Motar Dr Jazz Ta araso bakin Entry Hall na shiga gidan baba Obie, Bayan yai parking inta ya fito ya nufi cikin gidan, A katafaren Main Falo din gidan Ya taras da Twins zaune saman sofa tare da wani matashin saurayi kyakkyawan gaske kallo aya zaka yima fuskarshi ka shaida an uwan Justice ne, gaba ayan su wankan suit ne a jikin su, Cike da jin fargabansu Ya nufe su, Cikin sanyin murya yace"barkanku da hutawa" Ko kallo bai ishe su ba, Kamar Yayi magana da bango, kuma
Chapter 3 · 0% Book details