Sashe 161
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba "Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta fa a tare da zukunnawa gaban prayer mat din "Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi" jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba. "Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo" dakyar ta bu e idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta. fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki auka ko ina sanya maku ido ne" shiru tayi bata tanka mata ba. "ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..." bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta mi e tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta "Ina zuwa"? "Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa. ________________ Chief Owais Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish. Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya fa o mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din "My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"? Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa" Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..." Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki. "Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri" "Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"? "Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"? "Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai aga ba sai a kira na hudu yayi picking. Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"? On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba. "Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin " "Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su" "Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki. *Unaisah Angel* Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar akin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba. Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa. A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ofar ta bu e ta, dira afarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta. dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matu ar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar akin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da asan hijab dinta dake ja da kasa gaba aya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife asa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata. Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin bu ofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ame a durkushe ta kasa agowa yayin da walwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske. amshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin Dadda ar muryarsa ta katse zancen zucin ta "Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta mi e, gaba aya ta fa a kan broad chest dinsa ta ame shi, cikin shesshekar murya take fa a mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta. Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba. "Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?" Batare data ago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa," "Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa. yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya auka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta aya dafe da saitin zuciyarta. "Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..." yawu ta ha iya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh. har ya aga afa zai nufi toilet din Yaji ta dam o upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta. Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you" murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba. "Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka ji u da ruwan hawayen ta. i sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba. e mashi kafada tay kamar aramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik" A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ofar A hankali ta bu Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matu ar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi. _Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers in gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_ Da tsantsar ru ani ya furta"Danish! Is that you?" *DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________ "Danish is that you"! Ya fa a yana bin fuskar shi da kallo, babu alamun yaji maganar shi, babu inda ke motsi a jikin shi in ka cire numfashin shi dake fita cikin nutsuwa.