Sashe 210
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
karamin tashi zaiyi ba" ya fada fuskarsa da damuwa jikinshi duk yai sanyi, Zuciyarsa ta karaya, saboda shi kan shi yaso yaron kuma bakomai yafi daga masa hankali ba face kin kar6ar shahadar da baiyi ba. "Sheikh ga Unaisah nan, Har yau bata daina sanya damuwa aranta ba, dakyar muke samu tayi bacci, dan Allah ay mata nasiha.." Taj ne yai maganar. Ya tambayi meye silar ciwonta, Taj ya fada masa komai. Tsananin tausayin su ne Ya kama shi, Cikin sanyin murya ya farayi masu Nasiha har na tsawon mintuna talatin kafin Ya gama gaba daya jikinsu yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu sosai. Har wurare karfe 9 Shiekh Imam yana agidan daga bisani yai masu sallama Chief Ya rakasa Har cikin motarsa sai da yaga tafiyarsa kafin ya juyo. Time daya shigo falon ya tsinkayi muryar Ummi tana fada ma Taj Unaisah taki cin abinci. Da damuwa akan fuskarsa yace"Why Unaisah? Baki so ki samu lafiya ne? Ai ta fama dake akan kici abinci" Muryarta kasa kasa ta furta"Zuciyata ke tashi,duka abincin da naci da safe dana rana saida na amayar da su a toilet, ban fadi maku bane saboda bana son in tada maku hankali, abincin ma bana jin dadin shi ..." Kafin wani ya furta kalma muryar Chief ta katse su. "Gobe idan dr yazo duba ki ki fada masa aman da kike yi, amma bazan bari ki kwana da yunwa ba, Fada min me kike son Ci" ya fada tare da dafe Sofa da hannayensa Yayin da idanunsa ke akan fuskarta. Saboda nauyin shi da take jine yasa ta ce"zan daure naci wanda aka kawo min" "Ina abincin nata yake" Batool tace"yana a daki" "Je ki auko min" mikewa ta yi da sauri ta nufi dakinsu. Jim ka an sai gata ta dawo hannayen ta ruke da tray ta ajiye shi kan rug. Zagayowa yayi tare da samun wuri Ya zauna a gaban tray din, mamakin chief ya rukesu Musamman daya Kira Unaisa Ya nuna mata gaban tray din Yace tazo taci abinci" Ta dan zaro idanu tare da kallon Taj fuskarsa auke da murmushi yai mata alamar taje mikewa tay jiki ba kwari ta zauna tana fuskantarsa, yayin da tray din ya raba tsakanin su. Coconut water ya dauka da sauri ta mika yatsun hannunta dake kerma da niyar ta kar6i Glass din Batai aune ba taji ya kanga mata strawa din a baki, wata irin kunyace ta kamata, adan rude ta saci kallon su ummi da Taj fuskokinsu dauke da murmushi.. Ganin ta ki motsa lips dinta yasa shi furta"ki sha" yawu ta hadiya utt kafin a hankali ta fara zukar shi, abunda tagaza sha dazu sai gashi ta kwankwade shi duka batare da ta ankara ba har saida ya janye straw din daga bakinta. Spoon ya dauka Murya na rawa ta furta"zan iya ci da kaina" ta fada tana kyafkyafta gray eyes din ta Hakan ba karamin Jan hankalin shi yai ba. "Ki bari ya baki mana Unaisah, Baki ga yadda hannunki ke kerma ba taya zaki iya ruke spoon" Ummi ce ta yi maganar aranta ta ayyana Samun wuri. Batool sai faman hadiyar yawu take yi, ba yunwa take ji ba, Amma yadda taga Chief na ciyar da Unaisah yasa taji dama ya bata itama. Taj kuwa Ransa fari fat da farin ciki kamar ya zuba ruwa a asa ya sha, Burinsa yana daf da cika, abun da ya da e yana jira abunda yafi burgesa yadda Chief ya nuna kulawa agare ta agaban shi inaga idan sukai aure? Allah kadai yasan gatancin da zata samu a gurin sa, Shi yasan Unaisah ta gama morewa. Tun tana jin kunyar ya bata abaki har ta dan saji jiki ganin daddynta bai nuna wani abu ba.. duk in ya bata one spoon sai sun ha a ido da juna launin idanunsa da take kallo bakomai yake tariyo mata ba face kyawawan idanuwan Danish kasancewar launin idanunsu daya hatta shape dinsu kamar an zana saboda kyau. "My Angel" muryarsa ce tay mata gizau a cikin kunnanta... Lumshe idanunta ta danyi wasu zafafan hawayene suka taru a cikin su sam bata son kowa ya gani. Nutsuwa ya yi yana kallon fuskarta, tuni Ya dakata da bata abincin ganin halin da ta shiga. "Unaisah" muryarta na rawa tace"Naam" "Pls don't shed your tears"! jinjina mashi kai ta yi. "Na koshi da abincin, Ina so zan shiga toilet" bata jira amsar shi ba, Ta mike har zata fara tafiya taj yace"har kin kammala cin abincin ne"? danne damuwarta tayi"Eh, Inaso zan shiga toilet" Da sauri ta nufi dakin su, Tana shiga toilet taja kofa ta datse, tare da jingina kanta jikin bango wani jiri jiri take gani kamar zata kife kasa, sai faman jan numfashi takeyi tare da zare gray eyes dinta. Har yanzu ta gaza yarda cewa man dinta baya atare da ita, bata taba zaton zata iya rayuwa batare da shi ba. Duk irin burin da ta ci akan shi in sunyi aure zata kyautata mashi saboda halaccin da yai mata yanzu gaba daya plan dinta Ya lalace. Saitin Zuciyarta ta dafe da tafin hannunta"My man, na gaza yarda cewa ka mutu, Ina ji araina kana raye, shiyasa har yanzu zuciyata take harbawa, don da ace baka raye babu makawa saina bika nima" *Mr President* Around arfe shabiyu na dare bai runtsa ba, ya wuni da bakin cikin da owais ya kunsa masa, har ciwon kai saida yai, kayan bacci ne a jikin shi ya zuba hannayensa a cikin aljihunsa wandonsa, Sai sintiri ya ke yi a tsakar katafaren bedroom din Hajiya laura, ya rasa meke masa dadi? Komawa yai window Ya dafe glass din da tafin hannunsa Ya zuba ma sararin samaniya idanunsa da suka ka a jawur.. "Why Owais? why? girgiza kai ya danyi"Ni nasan bayin kanka bane Owais, akwai wanda ke son Ya shiga tsakanina dakai, amma meyasa zaka zargeni kamar bakasan wanene mahaifinka ba"? Bai aune ba Yaji tayi hugging dinsa ta baya tare zagayo hannayenta kan flat tommy insa. "My big boss, pls ka fada min meke damunka? gaba daya yau nakasa gane maka, kwata kwata babu walwala a tare dakai. "Ina da damuwa amma bazan iya fada maki ba kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo min mafita" Kwantar da kanta tayi kan shoulder dinsa"in sha Allah zanyi maka addu'a, amma pls muje mu kwanta, dare yayi sosai kana bukatar hutu" "No kije ki kwanta bana jin bacci yanzu" zagayowa tayi tagan shi tare da jinginar da bayanta jikin window glass din a hankali yake dubanta, Nightgown ce a jikinta shara shara rigar. Kashe murya tayi"ko dai kazo muje mukwanta ko kuma In kira Sarauta In fada mata abun da ke faruwa tunda ni kaki sanar dani" tana fada ta juya zata nufi cikin dakin donta dauko waya da sauri yakai hannu Ya dam i waist dinta Ya janyo ta ta dawo Jikin shi. "Ba sai kin kirata ba, naji zan kwanta" kashe mashi ido daya ta yi"ai da ka bari na kirata, kai kasan me zai biyo baya" Baisan ya zaiyi da laura ba, sometimes indai yana tare da ita koma mashi take yarinya duk da yana jin dadin hakan sosai. Lallaba shi tayi harta samu yabita suka kwanta. ______________________________bayan wani lokaci A kwana A tashi ba wuya wurin Allah, yau Wata daya Cuf dakai farmaki gidan kurkukun Kaddara. meya faru a yan kwanakin nan a kowani Family? A bangaren Aneelerh cikin kwanakin da suka gabata, ta kasance cikin tsananin damuwa abun duniya ya ishe ta, ta rasa ya za ta yi, kullum tunanin ta wa yakamata ta tunkara da maganar? Ga shaida tana da ita a hannu sai dai tasan mawuyacin abune a yarda da ita, bayan haka tana jin tsoron ta sanarma wani maganar ta koma masa, akarshe ta jefa rayuwarsu cikin hadari. tuntana 6oyewa har sai da ta kai ga kowa na gidan Ya fahimci Akwai abunda Ke damunta saboda yawan razanar da takeyi da zarar ankira sunan ta, In tana cin abincin Yatsun hannunta kerma suke kaf kaf, bayan haka takan raba dare bata runtsa ba. Babu irin magiyar da basu yi mata ba akan ta fadi abunda ke damunta tace itafa ba bakomai lafiyarta qalou, Har abie Yasa aka kirata a falo suka zauna duka mutanan gidan Ya matsa mata akan ta fadi meke damunta a karshe tayi masu karya tace dama a kwanakin nan tana yawon yin mafarkin Uzair da Taj shiyasa ta shiga damuwa, har kuka ta yi masu, duk don su auki maganarta Serious, tausayin ne ya kama su, gaba daya suka ha u suna lallashinta hada uncle dan iya shine kan gaba, har ila yau bata ta6a yin kuskuren da zai gane tasan wani abu game da shi ba. ___________________________________ Idan muka koma bangaren Unaisah, sai dai muce Alhamdulillah, jikinta ya fara murmurewa, damuwarta ta ragu saboda gatancin da take samu agurin mutan dake bata kulawa, Aunty Ummi, Batool, Taj uwa uba Chief, cikin kankanin Lokaci Shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, baya gajiya da bata lokacin shi, kulawar shi, soyayyar shi. kullum ne sai sun ha u da juna, mafi yawan lokutta atare su ke yin breakfast da dinner agaban kowa yake bata abinci abaki tun tana jin kunyarsa yanzu har ta saba da wayewar shi ganin Taj bai taba nuna ya damu da hakan ba saima dadi da ya ke ji. a Chief yayi namijin kokari gurin samun lafiyarta, kullum cikin faranta mata rai ya ke yi, Yanzu atare suke motsa jiki a gym room dinsa, bayan haka atare suke yin Kallo a tv room dinsa, har garden din gidan suke zuwa atare su yawata ba karamin nishadi take samu ba, komai ta ke so shi ya ke yi mata, saboda tsantsar kulawar da yake bata ko tari tayi wanda bai kwanta masa arai ba sai ya kira dr don yazo ya duba ta, saboda baya wasa da lafiyarta. duk wani abu da daddynta Ya fada masa wanda tafi so tuntana Yarinya sai da Chief yasa aka kawo mata shi agidan. Saboda kyautatawar da yake yi mata ne yasa ta fara Jin shi sosai a cikin ranta, da tunanin shi take kwana da shi take ta shi, In ta farka daga bacci shine mutun na farko