Sashe 48
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra Best gifts for your loved ones An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ Shesshe ar kukan su ta cika akin, babu mai lallashin wani a cikin su, tsananin tausayin taj ne ya kamasu jin irin kalubalen da ya fuskanta, A hankali unaisah ta aura tafukan hannayenta dake kerma kan fuskarshi ta share mashi hawayen shi, cikin sanyin murya tace"daddy, ka yi ha uri, ka daina zubar da hawayenka, bana son ganin su, kallonta yai da rinannun idanunsa muryarsa na an rawa yace"My Angel, ni nawa aluban dana fuskanta bakomai bane akan naku! Ku ne kuka ga rayuwa, ku yakamata a jajanta mawa, a kuma tausayama rayuwarku....." gaba aya hankulansu Sajeed na akanshi, da ru ani unaisah tace"daddy, kasan abun da ya faru dani bayan na gudu daga rugar su danejo"? Lumshe idanunsa yai hawaye na sintiri ya an jinjina kanshi kafin ya motsa la66ansa"na san abun da ya faru dangane da rayuwar kullan da ku ka yi a GIDAN KURKUKUN ADDARA, da kuma irin ba ar izayar da suke yi maku, ranar da mu ka fara ji daga ni har chief duk irin juriyarmu sai da muka zubar da hawayen mu saboda abun ya aga hankulanmu, ya razanar da mu, bazan iya misalta maku halin da muka shiga a lokacin da muka ji labarin abun da ake aikatawa a GIDAN KURKUKUN ADDARA. Kallon kallo Su Naufal suka soma jifar junansu da shi idanuwan kowannansu sunyi jawur da su, saboda kukan da suka sha, bakomaine yasa su kallon juna ba face mamakin yadda akai daddyn Angel Yasan abun da ake aikatawa agidan kurkukun addara, Unaisah ce kadai batai mamaki ba saboda tasan dama sun sani watakil abakin salsabeel suka ji komai. Murya na rawa Batool Tace"daddy dama kunsani? Meyasa baku kawo mana dauki ba? Kunsan kuwa irin untatar rayuwar kullan da mukayi a gidan kurkukun addara? Ta fada hawaye masu umi suna sintiri akan kuncin ta, muryarsa a raunace ya furta"mu kan mu ba mu jima da sani ba, da ace tuntuni mun san da zaman ku da har rayukanmu zamu iya sadaukarwa don mu ceto rayuwarku" Ummin dake kallon batool jikin ta har tsuma yakeyi saboda tsabar agara da son jin tarihin rayuwarsu babban burinta taji menene ma'anar gidan kurkukun addara da taji sunata ambato a bakunansu. Jan numfashi batool tayi kafin ta aura da cewa"mun rayu tun kafin mu mallaki hankulanmu, bamu ta6a ganin hasken rana ba, babu shige babu fuce, a aki aya muke a kulle, kullum cikin uniform aya, abinci sau aya arana, bamusan dadin rayuwar duniyar nan ba, duk wani hakkinmu na rayuwa an tauye mana shi, mu bamu san dadin iyaye ba, sannan babu mai jin kukanmu, balle a kawo mana dauki, anjuye mana tunaninmu balle musan cewa muma mutane ne masu an ci kamar kowa.... ..." bata arasa maganarba saboda kukan daya tokare makoshinta, tamkar zatayi kakarin amai. Cikin karyayyar murya Unaisah tace"tsohuwa tamira ta ta6a fada min cewa na jininmu ne kadai zai Iya sadaukar damu, har yau nagaza yarda da maganar na n, Ina kokwanton tayaya za'ay iyayen da su ka yi silar zuwanka duniya ko wani naka ya sadaukar dakai inda za'a azabtar da rayuwarka? Daddy wanene ya sadaukar dani A matu ar ru e ta jefa mashi tambayar tana kallon shi. Cikin sanyin murya yace"unaisah ni kaina a rude nake, bansan wa zan zarga ba Allah shine yasan wanene mugun da yayi maki wannan aika aikar" Muryar ummi araunace tace"dan Allah ku fahintar dani, tun azu inata magana kunki bani amsa! Inaso naji meya faru da ku? Sannan Ina ne GIDAN KURKUKUN ADDARA"!? yar Unaisah ta lallashi zuciyarta dake yi mata radadi, kafin ta aura idanunta akan fuskar ummi"zan fada maki komai da kikeson ji aunty ummi" A hankali ummi ke kallon fuskar unaisah Lokacin da tafara bata labarin rayuwarsu wata irin zuface ta soma wanke fuskar ummi, jikinta ya hau yin kakarwa saboda razanar da tayi, ko a mafarki bata ta6a jin labari mai matu ar firgitarwa irin wannan ba tuni hawaye sun soma yar tseral kan kuncinta. Abunda yafi tsaya mata arai cikin labarin da Unaisah ta bata shine mutuwar Unaizah yar gidan daddy, ba ita ba harta taj Jikin shi Ya gama mutuwa saboda bakomai suka sani ba dangane da rayuwarsu saida unaisah tafara basu labari, chief dake atsaye bakin door yana sauraron su kasa jurewa yayi, wani irin jiri jiri Yake gani acikin idanunsa, zuciyarsa har wani tafarfasa take yi tamkar zata kone kanta tsabar 6acin rai da fusata, jijiyoyin wuyansa tuni sun fito rudu rudu kan goshinsa, juyawa yai da sauri Yabar kofar dakin, A hanzarce big guy yabi bayansa gudun kada zuciya ta debe shi Ya je yai ma kanshi Illa. Zuciyar ummi dake hauhawa tana harbawa da wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali tama rasa ina zata jefa kanta taji dadi gaba aya taji ta tsani rayuwar duniya, Hakika Labarin su Unaiza Ya karya mata zuciya, ya ara mata karfin imani sai yanzu ta gane babban kuskuran da tayi nagaza daukar addarar rayuwarta, cikin shesshekar kuka mai ha e da gunjin kuka ta furta "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wannan wata irin musibace? Ku fadamin Tayaya akai har kuka Iya jure wannan ukubar da ananun shekarun ku batare da zuciyoyinku sun buga ba? La66anta na kerma ta fada tana dubansu kafin taci gaba da cewa "Zuciyata tagaza yarda da abun da kunnuwana suke jiye min! hankalina Ya tashi! Zuciyata ta karaya! Wannan wani irin zaluncine? Su wanene wadannan Fasikan mutanan mugaye azzulamai marasa imani da tausayi, wadanda basu auki ran dan adam abakin komai ba, wai su wanene su dan uban su? Wasu irin dabbobine su jahilai, Masu matattar zuciya, Anya kuwa suna da zuciya a kirjinsu? Anya kuwa mutanene su kamar kowa? Ina kokwanto akansu..." gaba daya ummi ta burkice masu sambatu kawai takeyi kamar sabon kamu ahauka, da alama abun ya razana kwakwalwarta. Rashin imanin da akai ma yaran ya aga hankalin ta, fashewa ta kuma yi da kuka kafin taci gaba da fadin"sun manta cewa zasu mutu su koma ga Allah? Wai su basa tunanin makomar su ne? Duniya ka ai suka sa agaba, ko Sun manta cewa duk wani abu da suka mallaka aduniyar nan zasu barshi? Daga su sai halin su za'a binne su!?...." aya bayan aya take kallon su jemimah dake ta kuka aranta ta ayyana yanzu gaba dayansu nan an lalata rayuwarsu har da yan ananan cikin su wani irin yunkurin amai ne yazo mata da gudun gaske ta mike ta fuce daga dakin, Har batool ta yunkura zata bita taj yai saurin ru e hannunta, "ku barta tayi kuka ta hakanne zata samu saukin abunda take ji aranta" jiki asanyaye batool ta zauna. Shi kanshi bazai Iya misalta irin kunar da zuciyarshi take yi mashi ba Cikin muryar lallashi Yace da su"Idan na ce kuyi hakuri kamar na cuce ku ne, saidai ba yadda zakuyi hakurin nan dai shine yakamace ku, Allah Baya barin hakkin wani akan wani, wadanda suka azabtar da rayuwarku In sha Allah za su ga mummunar sakayyar da Allah zai masu tun agidan duniya zasu fara ana kudarsu kafin su koma ga mahaliccinsu su fuskanci makomarsu......." da yar Ya samu ya shawo kansu, kafin ya bi su daya bayan daya yayi huggin dinsu duk don ya kwantar masu da hankalin su, sai da ya tabbatar ya share masu hawayensu tukunna yace "Dan Allah kada ku sanya damuwa aranku, ku kwantar da hankulanku in sha Allah komai yakusa zuwa karshe, yanzu ku koma dakunanku ku yi wanka ku kwanta ku huta, nasan baza a rasa masu fama da ciwon kai a cikin ku ba, zanyi magana akawo maku breakfast har bedroom dinku" muryoyin su adisashe suka amsa mashi da toh, kafin suka mike kamar wadanda aka zarewa laka haka suka nufi kofar dakin suka fuce. Bayan fitarsu Ya rage daga Unaisah sai batool sai kuma Taj, Mikewa batool tayi jikinta tamkar na wadda tayi zazza6i ganin ta nufi kofar dakinne Yasa taj yi mata magana"Ina zaki je ne"? akin Aunty Ummi" amsa mata yai da okey, bayan ta fuce ya maida dubanshi ga unaisah, janyota yai tare da kwantar mata da kanta kan kirjinsa hannunsa akan kafadarta "Ina fata yanzu babu abunda ke maki ciwo"? muryarta kasa kasa tace"eh daddy," Da yar zolaya yace mata"ya rashin ji ko da yake naga kin daina Yanzu"? ara shige mashi tayi tana yar dariya, bubbuga bayanta yai da hannunshi, kafin ya janyeta, ya mike kan gwiwowinsa ya fuskanci alkibla yakai goshinsa kasa yai sujjada murmushi tasaki tana kallon shi, da sauri itama tayi sujjadar kamar yadda yayi, tsawon mintuna kafin suka dago da kansu fuskar kowan nan su dauke da annurin farin ciki "Daddy fada min me ka ce acikin sujjadarka" Numfasawa yai kafin yace"nayima Allah godiyane da ya bayyanar min da ke da ranki da lafiyarki" "Nima haka" murmushi suka kuma saki gaba dayansu, "Daddy Inaso na tambayeka, tayaya akai ku ka hadu da su salsabeel? Ko ya fada maku yadda akai suma suka ku6uta daga kurkukun addara"? Shiru ya anyi kafin yace"ki bari idan yazo sai ki ji daga bakin shi, yanzu nafiso ki kara samun kwanciyar hankali" amsa mashi tayi da toh "ki tashi mu shiga toilet ki wanke fuskarki kizo mu ci abinci" Ya fada tare da ruko hannunta suka shiga toilet, bayan sun wanke fuskokin su suka fito atare A gefen gado suka zauna Ya bude masu abincin tray din da suka ajiye kan table Cikin kulawa yake bata abinci abaki tana ci, tsabar dadi kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, wai yau gata ga daddynta "Daddy, Ina aunty Aneelerh da babynta"? Murmushi Yasaki kafin Yace"suna nan cikin koshin lafiya, kwanakin baya nabibiyi layin wayarta amma ba'a aga ba sai wata rana dana ci sa'a aka daga wayar kinsan wanene ya daga" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace" aninki baby junaid," waro idanu waje tayi da tsantsar farin ciki tace"daddy sunan shi junaid" daga mata kai yai alamar eh "baki ga yaron ba kyakkyawa dashi, ga wayau sai ma in yana surutu.." cike da zumudi tace"daddy inason ganin shi tare da aunty aneelerh, dan Allah ka kaini wurin su nayi missing dinta"