← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 237 OF 247

Sashe 237

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

hakan, nasan yanzu kinyi danasani, saboda kin gane gaskiya" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh. "Ki gode ma Allah Unaisah, mommyn ki jaruma ce, I've wondered who gave birth to this remarkable child, cos you're different, with a sharp mind and loving, Ina alfahari da mommynki, saboda tayi bajinta, tayi abunda ya cancanta a jinjina mata..." tun daya fara magana ta an sassauta da kukan sai shessheka da ta ke yi, Kalaman Chief Sun ara sa ta jin wani irin masifaffan son mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan. "Uncle din mommynki Shine silar komai daya faru, shine munafukin dake ulla makirci atsakanin su, bayan haka muna zargin yana da sa hannu a kungiyar matsafan kurkukun kaddara, yanzu haka mun fara bin diddiginsa nan bada jimawa ba zai shigo Hannu" In a low voice tace" I think he's the one who sacrificed me, kuma ina zargin yarinyar Aunty Ummi daya dauka in dai basu kashe ta ba, zai iya yiwuwa tana a cikin fursinonin kurkukun kaddara, watakil ma tana atare da mu" "Tunanin mu yazo aya Unaisah ..." "Amma, Ina jin fargaban mommy na ta i kula ni" "Zata kula ki Unaisah, a yanzu haka jiran ki ta ke yi, na fada mata zaki neme ta da kanki, ki kira ta awaya ki bata hakuri sannan ki nemi yafiyarta hakan zaisa taji dadi acikin zuciyarta" cike da zumudi ta juya zata tafi yai saurin dakatar da ita"ina zaki je" Fuskarta a yamutse tace"i wanna call her" kayataccen murmushi Chief ya dan saki"Okay, ga kayanan ki tafi da su" ya fada tare da nuna mata suitcases din dake ajiye gaban Couch, arude take kallon su a lokacin harya juya ya nufi ofar da zata kai shi gym room dinsa Ya shige ciki. Kasancewar akagare take da ta kira mommynta, bata tsaya yin wani dogon tunani akan akwatinan ba, cikin sauri ta nufe su, taja handle din daya ta f uce da shi. ______________________________ Tana shiga Bedroom dinsu, ta aura akwatin saman gadon su, Ta dauko wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta danna ma layin da tayi saving da Aunty Benazir kira, saboda zumu i sam ta kasa zama sai zarya ta ke yi a tsakar dakin, almost 3 times tana kira ba'a picking, jikinta ne yayi sanyi saboda ta yi zaton fushi take yi da ita shiyasa bata daga ba. _Message ta tura mata mommy, dan Allah ki daga kirana akwai abun da nakeso In fada maki_ Ba'afi minti biyu data tura sakon ba, sai ga kiran Aunty Pretty ya shigo wayar ta, kwata kwata batayi farin ciki da ganin kiran ba, saboda a halin yanzu bata son ganin kiran kowa in ba na Aunty Benazir ba, har ya katse batayi picking ba, sai da aka ara kira, ta ha e rai ba annuri ta aga kiran tayi shiru batayi mata sallama ba. On the Other hand jin tayi Shiru yasa Benazir tace"daughter, kin bukaci kina son yin magana dani, kuma na kira kinyi shiru"? Waro idanu waje ta yi saboda rudanin da ta shiga, sai da ta fara janye wayar daga kunnanta ta duba number in da kyau taga ta aunty pretty ce da sauri ta shiga messages ta duba number in data tura ma sa on, taga ba kuskure tayi ba Aunty Benazir ne ta turamawa amma ya akai Aunty Pretty ta kira ta sannan tace taga sakon ta? Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewa zai iya yiwuwa mutun ayane ke amfani da layi biyu, Ras taji gabanta Ya dan fa i, labban na kerma ta furta"Aun.. Aunty pretty, dama kece Mommyna Aunty Benazir"? Sautin Dariyar Benazir ce ta ratsa kunnanta, cike da nishadi tace"ni ce mana, layin da kika turama sako na Uncle din ki ne da nake amfani da shi, bayan na kar6i contact dinki agurin Aneelerh, ina saka number din Unexpected naga sunan da nayi maki saving ya bayyana akan screen din wayata nayita mamaki nace ashe da daughter dina nake waya batare da sanina ba, daga nan na yanke shawarar kiran ki da layin ya shureim saboda bana so ki gane ni ce...." wata irin kunyace ta kama Unaisah, tayi shiru tana zare idanun ta. "Kin daina fushi dani..."? Benazir ce ta tambaya akagare da son jin amsar ta. Kwatsam taji ta fashe mata da kuka kamar ranta zai fita, Hankalin ta ba karamin ta shi yayi ba, muryarta na rawa tace"Unaisah lafiya kike kuka? Meke damunki ne? Waya taba min ke"? Cikin shesshekar Kuka tace"Forgive me, Mommy I realize my mistake I apologize for hurting you, I love you more than anything in this world, I want Daddy to remarry you and bring you back to me, cos I need you in my life...." tana jiyo muryar Benazir dake ambaton Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mini ranar da nake ta jiran zuwanta Unaisah dagaske Kina sona yanzu? Kina son mommynki ta dawo kusa dake"? Jinjina kai tayi kamar tana agabanta tace"seriously, I love you so much, i want you to take care of me, I thought since Daddy had done everything for me, bazan bukace ki ba amma ayanzu na gane ke ce cika makon farin cikin rayuwata, bani da tamkar ki har abada..." Bata karasa maganar ba sautin kukan Benazir ya cika kunnan ta, hankalinta ne ya tashi da rawar murya tace"dan Allah ki daina kuka, bana son ji, pls, Allah zaiyi fushi dani idan kina kuka akaina..." cikin shesshekar murya Benazir tace"ba kukan bakin ciki bane Unaisah, kukan Farin Ciki ne, kin faranta raina, Kin sani jin kamar nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yanzu bani da sauran damuwa, Mijina ya daina fushi dani, yata ma ta daina guduna, Alhamdulillah..." "Ba ki ce kin yafe min ba"? Benazir bata bata amsar tambayarta ba, sai taga ta canza call din zuwa Video Call, picking tayi lokacin da idanunta suka sauka akan fuskar Benazir wata irin kunyace ta lullube ta, fadawa tayi kan gado wayar na a hannunta tayi saurin janyo pillow da dayan hannun ta lullu6e fuskarta tana dariya, itama Benazir din dariya take ma yi. Cike da zolaya tace"rasa kunyan 6eran taka, Lemme see your face, kin tuna karyar da kikai min, Kina zuwa school sannan a kano kike da zama uhum"? yalewa tayi da dariya ba tare data furta kalma ba. "Oh ni Benazir, mamaki nake wai ni ce na haifi zanka iyar balarabiyar nan tubarkalla kamar hurul ain" fashewa ta kumayi da dariya, Hakan ba karamin faranta ran Benazir ya yi ba, dama tayi ne donta saka ta farin ciki ganin ta damu sosai. "Aneelerh ta bani labarin kuruciyarki, yadda kasan ni agari, nima haka nayi kuruciyata amma fa ban kaiki rashin ji ba, gaskiya ni ban taba sa an kai daddyna cell ba" ta fada tana kallon Unaisah data kare fuskarta da pillow sai dariya ta ke yi. "Taya zamuyi magana bayan kinki bari inga fuskarki uhm? Pls let me see your face, " A hankali ta zame pillow din, ta matso da screen din wayar saitin fuskarta suka zubawa juna ido gwanin ban sha'awa. "Wow, ata tafi ta kowa kyau, launin idanunki irin na Ammin mu ne ta eygpt, kinsan me har yanzu tana araye ta tsufa tukuf..."murmushi Unaisah ta yi tana faman sauke ajiyar Zuciya. "Fadamin waya sa ki kirani awaya"? "Chief ne, shine ya fada min komai daya faru da ke" "Mutumin kirki, ya taimake ni, Allah ya saka sa masa da mafificin Alkhairin sa" Ta amsa mata da ameen.. "Kina da saurayi" cike da jin kunyarta tace"shine ai" "Wa"? "Zan fada maki ba yanzu ba" "Okay, abun da nakeso dake, Ki manta da komai daya faru, na yafe maki Unaisah, kuma ba laifin ki bane, rashin sanina yasa kika ulla ce ni aranki, amma ni ban ruke ki a cikin zuciyana ba, in ma akwai mai laifi to ni ce Unaisah, duk da nima bada son raina na tafi nabarki ba, amma naji dadi da ban tafi dake ba, watakil da yanzu baki araye tunda bana acikin hayyacina zan iya jefar dake akan titi...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan dake kokarin balle mata, cikin karyayyar murya Unaisah tace"pls kada kiyi kuka mommy, bana son ganin hawayen ki,..." jinjina mata kai tayi"bazan yi ba tun da bakya so....." sun dade sunayin waya akalla sun shafe awa daya da rabi a hakan ma basu gaji da yin wayarba, sai da Benazir tayi mata alkawarin zata zo gidan tukunna ta hakura su ka yi sallama da junansu. ewa tayi tsaye kan gadon, ta dinga tsalle kan matress din fuskarta dauke da murmushin Farin ciki. Shigowa dakin Batool tayi, jikinta asanye da kayan bacci riga da wando ko mayafi babu akanta. burki ta ci ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Unaisah ke daka Tsalle tana dariya kamar karamar yarinya. Baki asake da mamaki tace"Sis Meke damunki ne? Meyasa kike yin tsalle akan katifa sai kace karamar yarinya"? Bata amsa mata ba, ta duro daga kan gadon ta nufe ta, tare da rungume sosai, Batool duk ta rude ta rasa gane kanta fatanta Allah yasa ba tabin hankali ta samu ba. "Sis meyasa ki farin ciki ne uhm"? Ta fada tare da raba jikinta daga na Unaisah Fuskarta dauke da annurin farin ciki tace"Batool ki tayani farin ciki, na gano wacece mommyna wadda ta haife ni" waro idanu Batool tayi"are you serious? Ta ina? Wacece"? Murmushi tayi"Aunty Benazir, mai kama dake, Itace Mommyna, kuma itace Aunty pretty da mukeyin waya da ita.." farin ciki ne ya lullu6e Batool"ina tayaki murna sis, Kinji dadin rayuwarki, Mommynki da daddynki suna nan, Baki rasa kowa naki ba..." maganar Batool ta taba zuciyarta, jikin ta ne ya yi sanyi sosai, tsananin tausayinta ne ya kama ta, su da basu taba sanin dangin su ba. "Sis amma kin yafe mata laifin da tayi maki ne? Kuma taya akai kika gane itace mommynki uhum"? Ta fada akagare da son amsar ta. "Shekaran jiya bana baki labarin Aunty Benazir da Aunty Aneeleeh sunzo ba"? "Eh na tuna, ay time din na fada maki aunty ummi bata jin dadi, atare ma bacci ya dauke mu adakin ta.." an girgiza kai Unaisah tayi"baiwar Allah, Aunty Ummi, ta bani tausayi, naji labarin rayuwarta ashe kawaye ne su, da
Chapter 237 · 0% Book details