← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 16 OF 247

Sashe 16

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

murmushi. Karatun kur'ani benazir ta kunna a wayar, saboda ta fahimci Kiran wayar da akayi mata sautin karatun kur'ani ya fita shine silar da Aljanin daya sha eta ya gudu, Gefenta ta ajiye wayar, ta kwanta tare da jan bargon da zeenatu ta lullu6a da shi, itama ta lullu6e kanta, zuciyarta acike fal da annurin farin ciki, Harta kosa gobe tayi, kodan ta kira Yarinyar su ara gaisawa, ita kadai take ta tufka da warwara har ta yanke shawarar zata ha a yarinyar da zeenatu su dinga zumunci, in yaso ita sai ta kar6i layin maman yarinyar suna gaisawa da wannan tunanin wani baccin ya kuma daukarta. Bayan Unaisah ta kashe Kiran, wani irin da i take ji, aranta ta ayyana meyasa nake farin ciki akan matar da bansan wacece ita ba, wata'kil ma maman Sajeed ce, dole gobe in fada mashi munyi waya da matar dake a ru e da layin wayarsa, bata koma bacci ba sai da ta kara zuwa dakin danish cikin daren ta le a don ganin koya farka, kamar yarda suka barshi haka ta same shi, addu'o'i ta ara tofe shi da su ta ru o dogayen yatsun hannayensa ta sumbace su, tasha kuka a yayin da take agefen gadon shi ta ro i Allah akan ya ba man dinta lafiya tamkar zatayi hauka ita kadai a dakin sa ko tsoro bata ji, raba dare tayi tana gadinsa har bacci yafara kokarin daukarta sai da aka fara kiran sallar Asubahi tukunna ta baro dakin tana sharar kwalla.............. *FRIDAY MORNING* *Hajjaty the head maids* Sautin ringing in wayar pravin ne ya katse mata baccin ta, A hankali ta bu e idanunta masu dauke da bacci ta kalli ceilling na tsawon mintuna kamar mai nazarin wani abu, sam ta manta da abun da ya farkar da ita daga bacci har saida aka ara kira tukunna ta mi a hannu saman mattress ta janyo wayar ta karata a kunnanta ba tare da ta duba sunan mai kira ba. Banka o kofar toilet da akayine ya firgitar da ita kafin tayi wani yunkuri taji ya fisge wayar daga hannunta, har sai da gabanta ya fa i ganin kumfar sabulu a jikin shi, Ko sutura babu haka ya fito daga bathroom zindir haihuwar uwarsa, duk dan kada ta aga mashi waya' juyawa yayi da sauri ya koma toilet, hajjaty dake kallon shi da tsantsar mamaki ta mi e zaune tare da jingina bayanta jikin headboard tana jiran fitowarshi Badajimawa ba pravin ya fito daga toilet waist dinsa daure da towal, fuskarshi babu walwala tunkafin tayi mashi magana yai saurin tarar umfashinta da cewa"Karki kuskura ki ara gigin aga min waya idan an kira ni, babu ruwanki da wayata" lamarin ya aure mata kai adabarbarce ta furta"laifine idan an kiraka na daga? Anya pravin kana da gaskiya kuwa saboda kawai na aga wayarka shi ne ka fito tsirara daga toilet da ruwan kumfa a jikin ka"! Harara ya galla mata"wannan bai shafe ki ba, Nidai ina ara jan kunnanki babu ruwanki da wayata, ban yi maki iyaka da komai nawa ba, amma banda wayata," Kallon tuhuma take jefa mashi, ba tun yau ba ya tsani yaga ta ta6a wayarshi kamar ta tsunkuli ranshi ne. "Kallon Ya isa haka, ki tashi kije ki yi wanka" ta6e baki tayi kafin tace"ba yanzu ba, sai zuwa anjima idan zamu je dinner din Hateem" aure fuska yayi babu annuri ya furta"ay na fa a maki, bazan bari ki halarcin dinner in nan ba" "Amma dai dawasa kake min ko"? "Na ta6a yi maki wasa irin wannan"? "Amma meyasa zaka hanani zuwa bayan na riga dana kwallafa raina"? fuskarta a yamutse ta jefa mashi tambayar Shiru yai bai tanka mata ba, taci gaba da cewa"bazaiyiwu ba pravin, matan family din nan gaba aya zasu halarci taron sai ni kadai zaka hana zuwa"? Gaban mirror ya tsaya yana gyara jikin shi, "Dakai fa nake magana"? Sai da ya mula yasha iska tukunna yace"abun da nakeso ki fahimta, zuwanki dinner din baida amfani! Saboda matan family din nan ba kaunarki su ke yi ba, iyakaci suci maki mutunci su zazzageki ni kuma abun da banaso kenan, sannan ni ina kishin kije wadannan dattawan masu gemu su kalle min ke" Kwantar da kanta tayi jikin pillow "Wannan ba hujja bace pravin, meya kawo maganar cin mutunci a taron bankwana da hateem kaima in banda abun ka, sannan kishi da kake ji ay bani kadai bace matar da zanje dinner din ba muna dayawa...." kafin takare magabar ya tari numfashinta da cewa"Amma ay ke kadai ce ba'asan da igiyar aure akanki ba, kowa kallon bazawara yake yi maki, uwa uba kuma surar jikin ki dake jan hankalin su" Saukowa tayi daga kan gadon ta nufe shi, ta tsaya daga bayanshi tare da aura kanta saman bayanshi. "Hubbyna, dan Allah kada ka hanani zuwa, wallahi na wallafa raina akan dinner din nan, ka taimaka min pls nayi maka alkawarin zan kare mutunci na, indai ka yarda dani pravin kabarni inje' da shagwa6a ta are maganar tare da zagayo hannayenta kan waist dinsa tuni yafara jinshi a wata duniyar, ta san duk wata hanya da zata canza mashi ra'ayin shi. Lumshe idanunshi yayi, yayin da yake kallonta ta cikin mirror, tsantsar sonta da kaunarta yake ji, ago dakanta tayi daga bayanshi ta daura kan kafadarsa ta hagu. Suka ci gaba da kallon juna. "Inaso ka fa amin tsakanin ni da kai waya fi kama da an mu" Shiru yayi tamkar baison furta maganar ya ce "kin fi kama da shi" Murmushi tasaki har dimple dinta ya lotsa "Allah ya ji an shi" ya amsa mata da ameen. Sumbatar wuyanshi tayi, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba "Zaka barni inje babyna"? Baiyi niyar barinta taje ba, amma yanayin da tayi mashi maganar yasa shi amincewa batare daya shirya ba. Wani irin farin cikine ya lullu6eta shi kanshi ya shaida hakan "Atare dakai zamu je ne"? "No,ni ba lallai naje ba," "Amma yakamata kaje kaima zaiji da i, kaga daga yau shikenan gobe ba lallai ka samu danar ganawa dashi ba may be tashin asuba jirginsu zai lula" Janyo hannunta yayi ya dawo da ita ta gabanshi, yadda zaiji dadin kallonta dakyau "Nima zanje in sha Allah" "Bari na taimaka maka ka idasa shiryawa, nasan hajiya Saratu tana can tana dakonka, daga zuwa sallar asuba ka gudo dakina" "Matar da bata damu dani ba, ni fa banda amfani awurinta... " bata bari ya karasa maganarba ta rufemashi baki, don bata son yana aibata hajiya saratu awurinta. Shirye shiryen sun kankama, Don tun wuraren arfe tara na safe Zungureriyar motar kamfanin su zahra mai auke da tambarin Zahra World of beauty ta karaso estate din, kafin shigar motar sai da Security officers su ka yi mata wankan tsarki ciki da bai suka bincike komai da na'urorin tsaro, hatta Interior designers din dake a cikin ta an matasa mata sai da Sojoji suka bincike su from head to toe, suka tabbatar ba su shigo da wani abun cutarwa ba, kafin suka bar motar ta shiga ciki, Hajiya saratu ce ta tsara lokacin da za'a fara aikin decoration din dakin taron saboda friday ne kurarran lokaci kwara ay komai da wuri acewar ta Masu aikin gidan kuwa tun asuba suka fara aura girke girke, saboda uban aikin dake gare su, abinci ne za'a girka kala kala, Na abilu daban daban, kafin kace me cikin anin lokaci amshi ya gauraye ko'ina na gidan baba obie, don anan ake aikin girkin.... Hajiya zahra kuwa yau tsabar murna kamar wadda akaiwa albishiri da gidan Aljana, tun jiya akayi mata saloon da kunshi na jan lalle kamar amarya, taci buri akan dinner din nan kamar ranar auranta, Saboda son ta dau gayu na kece raini motar Aneelerh ta ara da yake tafi tata motar tsada da kyau, Tuni taba mahboob motar ta hada shi da an canji ya tafi kai ta wurin da za'a wanke ta don ta ara kyau, kowa na gidan sai da yasan da zancen zuwan Zahra Obie estate saboda ta addabi kowa duk bayan an mintuna sai ta kalli agogo burinta lokaci kawai lokaci ya ci ka.... arfe 9 na safe, Zeenatu tana a zaune kan mirror chair, tana an shafe shafen ta, bata jima da fitowa daga wanka ba, jikin ta sanye da bathrobe mai kyan gaske, ta aure gashin kanta Fitowa benazir tayi daga toilet da alama itama wankan tayo, ta yi daurin gaba da towel, fuskarta babu walwala ta kumbura jawur da ita saboda kukan da tayi adaren jiya da abun nan ya faru Ganin zeenatu dake ta shafa powder yasa ta an saki face din ta da zolaya tace"uhum su baby shuriem wa ake ma kwalliya" kunyar maganar Benazir yasa tayi kamar bata ji me tace ba Gyaran murya benazir tayi still bata ago ba, saima ta auki jan baki tana shafawa "Wato kinyi imanin sai kin zautar min da yaya na"? Cak zeenatu ta tsaya da shafa jan baki, cike da jin kunyar benazir ta sunnar dakai "Duk hasken da Allah yayi maki zeenatu har sai kin ara da powder in ban da asara, so kike ki koma zabayyana ne'? dariya ce ta kubce ma zeenatu har fararen hakoranta suka bayyana masu kyau da tsari Muryarta asa asa tamkar ta mai yin ra a ta furta"aunty benazir mommy ma tana shafa powder in zata ma daddy kwalliya, shiyasa nima nake shafawa" dariya benazir tayi hadi da an girgiza kanta.. Wucewa wurin closet din dakin tayi domin shirya kanta, within minutes benazir ta fito asanye da riga da skirt sun an kama jikin ta Gaban madubin ta tsaya daga gefen zeenatu tana fadin"naga abun naki bamai karewa bane, ki tashi ki je ki sanya kaya, kafin darling din naki ya farka daga bacci" cike da jin kunyar maganarta, zeenatu ta mi e tana faman sakin murmushi sai da tafara daukar hijab dinta dake ajiye bisa gado kafin ta nufi hanyar fita dakin don taje nata dakin ta sanya kaya Fitarta ke da wuya suka yi kici6us da dr shureim wanda ke kokarin doka sallama, tun da ya sauke idonshi akanta ya kasa janye su, cikin jin kunyarsa ta sunnar da kanta kasa tana faman no e kai ta furta"yaya shurem ina ina
Chapter 16 · 0% Book details