← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 124 OF 247

Sashe 124

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

da kanshi saman kirjinta, ta shasshafa fuskarshi, muryarta na rawa tace ma zahra ta dauko mata ruwa, da sauri zahra ta fuce daga dakin jim ka an ta dawo hannun ta ruke da bottle water mai sanyi ta mi a ma Anila, yatsun hannunta na kerma ta bu e murfin ta gumtsi ruwan abaki ta watsa mashi saman fuskarshi, wata irin firgita yayi jikin shi ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama...nannauyar ajiyar zuciya anila da zahra suka sauke. Cikin sanyin murya anila ta ambaci sunan shi junaid! Firgigit ya ware idanun shi wa anda suka ka a jawur har saida suka tsorata, Yana ganin fuskar mommynsa Ya ameta ya cusa kanshi cikin kirjinta Ya fashe da kuka mai sautin gaske ya dinga sambatu na fitar hayyaci, hakan ba karamin aga masu hankali yayi ba...lamarin yayi matu ar daure masu kai? Meya faru da shi? Ya akai ya shiga cikin wardrobe ya boye kanshi hatta bugun zuciyarshi bana lafiya bane *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions [14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun addara Takun arshe page 38 Complete by Boss Bature Novels Elite Admin September 02, 2024 Sponsored Link Takun arshe "Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi. banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci aya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da bu e baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta an daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai. Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..." Mikewa Aneela tayi auke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi ya i yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun ka a jawur sai sambatu yakeyi mana" a hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya ma e kafa a ya ara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba aya suka yi mashi awanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai araji, wani irin fa uwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle an iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin Alhamdulillah sun dawo kenan, dama saida raina ya bani wani wurin sukaje, Ina Anan take ne? Me kuma akayi mashi yake kuka.. "? Uncle an iya yace"lafiya kuke kuka?Shima Yana kuka babu mai lallashin wani? Ina ita Anan"? cikin shesshekan kuka zahra ta sanar da su inda suka gano junaid "Abie, junaid baya sauraron kowa, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, kuka kawai yakeyi, mun rasa gane kan shi..." tsantsar tashin hankaline akan fuskokinsu har sun fara murnar ganin shi azatonsu Ana ce ta dawo da shi ashe ba haka bane. "Bani shi nan" abie Ya fada tare da mi a ma Anila hannu, a firgice baby junaid Ya ankameta alamar bazai je gurin abie ba, cikin murya kuka tace"abie ya ki yarda da kowa, su mami sunyi kokarin lallashinshi amma Yaki sauraron su...." Girgiza kai abie yayi tare da ambaton Inna lillahi wa inna ilahirraji'un kafin daga basani ya kalli anila dake ta sharar kwalla, tana jijjiga junaid "Anila ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan, Kina kara aga mashi hankali, je ki zauna ki lallashe shi, ke kadai ce zaki iya shawo kan shi, kiyi mashi addu'a ita yake bukata ayanzu..." amsa mashi tayi da toh, da sauri ta koma gefen gadon ta zauna, tare da sanya hannu ta talla6o kan shi, ta fara yi mashi kira'ar alkur'anin a cikin kunnanshi, su mami sunyi zungudum suna kallon su gwanin ban tausayi, cikin ikon Allah taji ya fara tsaitsayawa da yin kukan kafin a hankali taji yayi shiru ya nutsa kan shi a kirjin ta, fuskarshi tabi da kallo kumtunsa sunyi jawur, la66ansa sun kumbura suntum, hatta warin idanun shi sunyi jajir, siraran hawayene ke ta zarya kan kun cin shi, lokaci aya taji ya fara sauke ajiyar zuciya a jere jere, nunfashin shi ya fara daidaita ba kamar azu ba. bata dakata da yi mashi kira'ar ba har saida ta tabbatar ya daina shesshekar kukan kafin tayi shiru tana duban shi, ajiyar zuciya su mami suka sauke hankalin su ya dan kwanta jin yayi shiru Cikin sanyi murya ta furta sunan shi"junaid" motsa la66ansa yayi batare daya firta kalma ba... "Dan Allah ka daina kuka, kasan bana son 6acin ranka, nasan nice na bata maka rai na tafi anguwa nabarka, ka yi hakuri ka yafe min junaid, wallahi bansan za'a tada ku da wuri ba..." shiru yayi bai tanka mata ba... "Babyna, bazaka mun magna ba? Fadamin meke damunka? Kanka yanayi maka ciwo? Ko kana jin yunwa? Ina Ana? Meyasa ka yin kuka..." duk tabi ta rude sai surutu takeyi mashi, shidai yayi shiru bawan Allah shi kadai yasan bala'in da idanun shi suka gane mashi. "Kada ki takura mashi Aneelarh, tun da mun samu yayi shiru, ki kyale shi Ya huta, Allah kadai yasan meya faru da shi wanda yayi silar rikicewar shi"! Mami ce tayi maganar Ummi tace"ni ban ma san tunanin me zanyi ba wallahi, hankali na Ya tashi! abun da ya aure min kai meya faru da su? Taya akai junaid yayi wayon 6oye kan shi a cikin wardrobe? To ko dai wani mugun abunne Ya faru da su bayan tafiyar mu, gaskiya ina ji araina Ana ce ta boye shi don kada a cutar da shi ko kuma shi ya boye kan shi sakamakon wani mugun abun daya gani, Allah daga ganin halin da junaid yake a ciki bana lafiya bane, Yaga wani abune daya razanar da shi" ta are maganar tana kallon su Jinjina kai uncle dan iya yayi"nima abunda nake tunani kenan, amma taya za'ay mu san ainihin abunda ya faru bayan tafiyarmu? Cikin shesshekar kuka Anila tace"Junaid zai iya fada mana idan Allah yasa ya dawo hayyacin shi" Mahboob daya gama razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayya na saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya. Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba. Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie
Chapter 124 · 0% Book details