Sashe 168
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba. abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba. "Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.." ta fada tare dakai hannu ta an bubbuga afar Unaish shiru bata farka ba, "Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta. Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta. Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta mi e da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya ha iya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta ago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta. dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya.. "Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..." dakyar ta iya bu e idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi Wani irin ciwon kaine Ya far mata... Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.." Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba. "I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai aga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya an kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne. "Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi azu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne" cikin kwantar da murya ya fa Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"! Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish "Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta mi e zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..." Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice". gabanta ne ya an fa i duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai.. "Daddy, wani irin Umarni ne? Ka fa a min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta fa a cike da jin fargaban amsar da zai bata.. Ido cikin ido su ke kallon jun. "ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun addara..." wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay... "Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na? ya fa a yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta. Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger" Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya ha e rai sosai saboda yana son ta auki maganar shi serious "Unaisah, karna kuskura na ara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da addara ba? Ko kuwa arancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi "Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar addarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun addara? Kin ta6a tunanin zamu sake ha uwa? Ikon wanene yin hakan"? In a weak voice tace"Allah" "Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi mu addari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata addarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...." nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi... "Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba" ta fa a hawaye na bin fuskarta... Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ru e su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa" "Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"! "Wace alfarma"? "Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta an sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana aya daga cikin members na kurkukun addara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali. Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj mi ewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai" "Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay a mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu.. _________________________________ Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta! babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai da ile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa. Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga.. Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi? Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita _________________________________ Har wuraren arfe sha aya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin ha ari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta. *CHIEF OWAIS* Bacci ya auracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne wa anda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba.. untata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan