← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 173 OF 247

Sashe 173

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

sauri ya ago ya kalle ta, zumbur ya mi e tare da ambaton sunan ta "Benazir!" Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba.. Gaba aya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ru e akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta. Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce," Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi. Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi. "Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya fa a fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ru o hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare. Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya bu e back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka urama juna ido kamar yau suka fara ha uwa, sunyi kewar junan su sosai. "Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?" Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan sha uwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita.. "Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba? "Ka manta wayata tana a hannunka?" "Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a asar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?" Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta asa, tasan bata kyauta mashi ba.. "Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina aunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba aramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta. yar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake bu e su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ureta jikin murfin motar . Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin ha e bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba aramin aga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi. "Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi ha uri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka ka a nan da nan suka fara yin ja... "Kin ha u da mijin naki?" aga mashi kai ta yi alamar eh, Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce arara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita.. "Tayaya akai ka gano inda nake?" yar ya furta, "Uncle inki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan. A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..." iris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke fa i mata, tayi mamakin zurfin cikin shi... o hannayenta ya yi acikin nashi. "Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da aunarki, shiyasa koda kika fa amin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki fa a ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar asar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika fa amin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima aruwa...." dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji da i, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya ha a komai da mace zata bu ata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban arta. Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina sa on ya sake ni?" Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta an ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata... "Daddyna ya bani goyon bayan in nemi soyayyarki, In har kika amince min zai yi magana da iyayenki, on friday za'a aura mana aure, Next week zan koma dake Canada, na yi maki al awarin ba zaki ta6a danasanin aure na ba, kin riga da kinsan wanene ni kin san halina, kuma ko bayan auren bazan hana yarinyarki ta zo inda kike ba, har shi kanshi ex-husband din naki bazan raba zumuncin dake tsakanin ku ba..." Kuka ne ya kubce mata, hakan ba aramin aga hankalinshi ya yi ba, bazai juri kallon hawayen ta ba, da sauri yayi hugging dinta, halin da take a ciki ya hana ta kwace kanta daga gare shi. Cikin shesshekar kuka ta ce,"In har da gaske kana so na kuma kana son farin cikina, to ka barni in rayu da mijina, wallahi bazan iya rayuwa da wani a namiji in ba shi ba, ba dan addara ta raba ni da shi ba, babu abunda zaisa na juya mashi baya, ko dan darajar ar dake tsakaninmu bazan Iya rabuwa da shi ba..." kusan suman zaune yayi jin maganar ta, raba jikinta ta yi daga nashi, fuskarta ta ji e sharkaf da hawaye taci gaba da cewa, "Ka taimaki rayuwana, ka rufa min asiri, in har taimakon da kayi min kayi ne don Allah, toh ka ha ura da ni, mu cigaba da zumunci har arshen rayuwarmu, amma maganar aure babu ita tsakanin mu..." Maganganunta sun karya mashi zuciya, wani irin zafi ne ya mamaye jikinshi, duk da sanyin A.c din motar hakan bai hana shi fitar da gumi ba. kifa kanshi ya yi kan kafa arta yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan min ha..." sambatu ya ci gaba da yi kamar ya fara zaucewa.. Tasan irin radadin karya zuciya ba kowa ke iya jurar shi ba, fargabanta kada tayi silar da Zaki zai rasa rayuwarsa amma ya zata yi? Bata da mafita da ya wuce ta lallashe shi taci gaba da bashi hakuri... "Yayana nakaina, matsayinka bazai ta6a canzawa agurina ba, bazan ta6a juya maka baya ba, ina jinka tamkar an uwana na jini, ina mai takaici in amsa bukatarka, bawai don baka kai in aureka ba, wlh kowace mace zata yi burin ta auri namiji jajirtacce nagari irinka, saboda ka ha a duk wasu kyawawan dabi'u da halaye wanda zaisa mace ta so ka, sai dai kash Allah bai kaddara kaine mijina ba, muyi ha uri mu rungumi kaddara, zan tayaka da addu'a Allah ya baka mace tagari, wadda zata ma ye maka gurbina...." cikin karyayyar murya ya furta, "Benazir bazan Iya rayuwa batare dake ba, zan ro i Allah ya dauki raina in huta da radadin rasa ki da nayi" da sauri ta ce,"In sha Allah bazan zama silar da zaka mutu ba, sai dai in zama silar farin cikin ka na har abada, zan tayaka da addu'a Allah ya baka ikon cinye jarabawar soyayyata, Allah ya cire maka sona acikin zuciyarka..." cikin rawar murya ta arashe maganar. shiru yayi bai ara magana ba, sai bugun zuciyarsa da take ji a jikinta. "Alfarmar da zan ro a a gurinka, don darajar manzon Allah SAW, ka rufa min asiri yayana nakaina, kada ka fa ama Daddynka komai da ya faru tsakanin mu, saboda zai iya sanar da Uncle ina shi kuma zaiyi min dole ne, nasan bazaka so abunda zai 6ata raina ba..." wani irin zazza6i ne ya lullu6e jikin shi, kamar ya fasa ihu haka yake ji, So bala'ene, duk maganganunta akan kunnanshi sai dai ya kasa furta kalma. Shafa sumar kanshi tayi da tafin hannunta cikin sigar lallashi ta ci gaba da kwantar mashi da hankali maimakon yaji sau i a ranshi saima yaji kamar tana ara rura wutar sonta a zuciyar shi.. Tayi fatan ace zata iya share mashi hawayenshi ta aminta da auren shi sai dai kash bazata Iya ba, kamar yadda yake jin azabar sonta itama haka take jin azababbiyar soyayyar Taj, duk namijin da zai aure ta sai dai ya auri gangar jikinta amma ruhinta yana agurin Taj. Bayan wani lokaci, ta fito daga cikin Motar, da gudu ta nufi cikin gidan tana shiga daki bata iske Zeenatu ba, saman gado ta fa a ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai ita. Hanky ya zaro daga front pocket dinsa ya share fuskar shi, saboda baisan daddynsa ya gano abinda ya faru da shi, saboda yayi
Chapter 173 · 0% Book details