Sashe 177
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
kan Mirror chair din with respect ya gaishe da ita, da fara'a ta amsa mashi Kafin Ya nutsu Yana jiran jin me zata ce ma shi "Ina fata kun fara shirye shiryen kawo farmaki"? shiru ya yi baice mata uffan ba. Yanayin dake a kan fuskarshi ta nazarta nan take ta fahimci baida matsaya Yar dariya tayi"jikana, fa amin ba, me ake Ciki ne"? dakyar Ya labarta mata abinda ke faruwa bai boye mata komai ba Girgiza kai tay"yaro man kaza, Har yanzu Jinin Elders ne a jikin ka, amma Alhamdulillah naji dadi da Allah Ya bani ikon ganawa dakai a karo na biyu, saboda na fahimci ka na bukatar in wayar maka dakai, in kuma yi maka karatun ta nutsu ta yadda zaka fahimci su wanene Elders da kuma dalilin dayasa suka raine ka..." aru e Yake kallon fuskarta... "Kasan wacece ni, ka kuma san matsayina agidan kurkukun kaddara, nafi ka sanin komai Danish, duk wani abu da suke aikatawa a tafin hannuna yake" ta fa a tana nuna mashi tafin hannun ta. "Abu na farko da baka sani ba, Elders Mayaudara ne, Maha'inta, maciya amana, bansan ko ka san da labarin nan ba, amma inaso ka sani tun kana jinjirinka cikin tsummanka suka sace ka daga wurin iyayenka, suka rabaka da su batare da saninka ba, sannan suka sadaukar da kai zuwa gidan kurkukun addara, Ni nasan su wanene Iyayen ka, wallahi basu san kana araye ba, an yaudare su ne da sunan ka mutu...." dafe kanshi yayi da hannu aya zuciyarshi cike fal da ru anin maganarta, bazai ce tayi karya ba sai dai kokwanton da zuciyarshi keyi bazai bari ya aminta da ita ta cikin sau "Bani da isasshen lokacin da zan yi maka bayani, amma atakaice ka zauna kayi nazari Danish, kai ganau ne ba jiyau ba, kasan komai, har yau zubda jinin mutane suke yi kamar kwari, Laifin me suka yi masu? Ahaka zaka rufa masu asiri uhyum? Ita kanta yarinyar da kake gudun rabuwa da ita ba zasu kyale ta ba, wallahi in har baka bada goyon baya an kawo karshen su ba, da kai da ita sai kun salwanta, saboda suna nan suna shirin yadda zasu kashe ku.." waro idanun shi waje yayi jin abinda tace. Murmushin gefen fuska ta saki tare da jinjina mashi kai"hmm wai kana tunanin Suna kaunarka? To wallahi ko aya basu ta6a kaunarka ba, sun raineka ne don biyan bukatar kansu, idan kai me hankali ne ga misali nan, Yanzu da suke ganin sunci moriyarka amfaninka ya kare kana neman tona masu asiri ba ga shi har sun auke mukamin da suka baka na garkuwarsu ba, sun ba Jeremiah, kai kuma nema suke su salwantar da rayuwarka saboda kai kadaine kasan sirrinsu dakai kadai za'a iya farmakarsu...." wani irin gumin tashin hankaline Ya wanke fuskarshi, Maganar tsohuwa khala tayi matu ar yin tasiri a zuciyar shi. Kusan sau uku Tana ambaton sunan shi bai amsa mata ba, saboda zuciyarshi ta lula duniyar tunani Har saida tayi mashi gyaran murya kafin ya dawo hayyacin sa "Ina Gabriel? Ya rayu ko ya mutu"? ya anyi mamakin jin ta tambayi gabriel ko a ina ta san shi"? "Yana adakinsa, bacci yakeyi" "Masha Allah, Naji dadin jin hakan, sai dai, Yar Uwarsa daya bari agidan kurkuku tana acikin mawuyacin hali..." "Who's she? ya tambaya don sam ya manta da cewa Gabriel Yana da sister. "His twin sister Gabriella...." a takaice ta labarta mashi ra shin imanin da tsohuwa inno tasa giant yayi mata, tsabar 6acin rai jikinshi har tsuma yakeyi "ta rokeni akan Tana son ganin an uwanta, nayi mata alkawarin ko zan rasa raina ne in dai muna da tsawaicin kwana zan ha a ta da an uwanta" cikin rauni na murya tayi maganr tare da mikewa daga kan kujerar da take, ta haske mashi Gadon da Gabriella take akwance kamar babu rai a jikinta, sai jan numfashi take dakyar dakyar "Nayi zaton ta samu lafiya, amma wani abu ya faru jiya wanda Ya aga hankalina, tana daga zu unna tayi aman Jini, ta dafe ciki tana fa in Yan hanjinta suna konewa, Inaji araina Inno ce tayi mata asiri, nadai yi kokarin yi mata yan dabaruna ahaka Jikin da sau i amma tana bukatar taimakon gaggawa daga gare ku idan ba haka ba da wuya ta rayu.." Jikin shi yayi sanyi saboda tsantsanin tausayin yarinyar daya kama shi, yanzu ya tuna ranar farko da aka kawo su har tsohuwa Zafreen tasa aka raba su. "Danish Ahaka zaka rufa masu asiri? Shikenan babu wani wanda zai kawoma bayin Allah dauki! Haka zamu barsu su cigaba da azabtar da rayuka? Ba zamu auki mataki ba"? Sam ya kasa magana saboda raunin da zuciyar shi tayi *Da wata irin kakkausar murya ta firta"YA RAGE NAKA GARKUWA, DOLE AYA CIKIN BIYUN NAN YA FARU! KO DAI KA BADA GOYAN BAYA AKAWO MASU FARMAKI, KO KUMA SU SU KAWO MAKU FARMAKI SU GA BAYAN KU..."* Sau Uku ta maimaita Hakan, kafin ta cigaba da arfafa mashi gwiwa daga bisani bayan ta ara jaddada mashi kwanan watan da zasu yi black night, ta bashi wasu muhimman bayanan da zasu amfane su, daga nan ta 6ace ma ganin shi, kifa kanshi yayi gaban mirror in Zuciyar shi cike fal da damuwa, anan wani wahalallan bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi. Lokacin da Batool ta farka daga bacci taga babu Unaisah adakin, bata damu ba, bayan tayi sallar asuba, taji shiru bata dawo ba, hakan yasa ta mi e ta fito daga dakin tafara neman ta, sai da tabi akunan Yan uwansu duka ta duba taga babu Unaisah, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba,. Da sauri ta nufi akin Aunty Ummunsu, tayi knocking almost 3 times, kafin ta samu Ummi ta bu e kofar, tana mi a hadi da yin hamma ko kayan baccin jikinta bata kaiga cire wa. "Babe, Har kin tashi"? Daga mata tayi"Aunty Ummi sister tazo nan? Na farka banganta ba" Girgiza kai Ummi tayi"Bata zo ba, kin duba ko'ina"? "Eh," ta fada da damuwa "Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta fa a tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh. Bayan shigar su akin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop inta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka. Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri. auko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen in bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba.. Da karan banin ta tayi picking call in kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi ka ai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru ta i furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan aton. "Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta.. Jin motsin bu e kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje. Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a garga inta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso. Koda Ummi ta fito bata fa a mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin. Har wuraren arfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time in Yin breakfast dinsu ya yi gaba aya yan uwansu sun hallara a dining ita ka ai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish. Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya mi e zaune Yana kallon ta da idanunsa wa anda suka kumbura. A hankali ta mi e zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet inshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya. Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar akin. takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya mi e ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi "Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta fa a tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce Cikin sauri ya ru o Arm in ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar "I want to ask you one question." shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi "baki tsoron ki rasa ni"? "Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka aya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai" "Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwa ayin ka mutu a filin ya i, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu yalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun addara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun" duk