← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 36 OF 247

Sashe 36

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

"Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya fa a tare da mi e ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya mi a ma Hateem wayar, Cike da zumu i ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi Har saida gabanshi ya an fa i ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka dam i waya. da sauri ya dago suka ha a ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske. Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya. "Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba. Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne. Bugu uku Chief yayi picking call din "Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"? "Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun azu ya i yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"? muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar. Da bu ar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki. "Babu, Mu ka aine"! "Uncle ka sanya sojoji su yi maku awanya saboda yaron ba shi aya bane, bana so asamu matsala" "In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais. "Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka auka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ara ha uri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran. Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ru e da faffa an faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu bu aci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci. anyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba. Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu fa asa. "Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"? Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfi ar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi. ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message. _I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_ Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata" Tuni amshin soye soyen da aka kawo masu ya bu e hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba. Farantin farko yana dauke da ban ararrun kaji anyi masu jar suya sai mai o sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, ayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun ha o masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu bu ata...... 'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman ha iyar yawu. Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us. Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,. Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya an bu e kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya ha iye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya ebo sakwarar ya mi a mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba... Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya fa o masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane. Bu e baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su... Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne auke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna... Bayan sun gama da plate din sakwarar, Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna. Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan coconut milk da fresh juice. Sauke farantan hateem yayi can gefe aya asa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi aya dafe da bayan shi, ayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu wa anda zai dinga gani yana ebe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba aya hakan ba karamin aga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma asa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya bu e idanunsa, dakyar ya samu ya an bu e su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma ya iya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai an tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani an cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma. Kafin ya gama auke auken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ame shi da hannayensa da farko ya an ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai da i yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya amesa kamar wani yace zai wace masa shi. Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda da in da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa. Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar ra a yayi mashi magana. "Do you feel what I feel about you?" Ya fa i hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa. Kamar daga saman yajiyo dadda ar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think" wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai ha iye sa. "Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ara jin muryar shi. "No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba "Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara
Chapter 36 · 0% Book details