Sashe 167
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
yace"meyasa zamu wahalar da kanmu akan shi? Yaron nan fa an rainin wayau ne, idan muka ce zamu bishi ta lalama bazai ta6a bamu ha in kai ba, kwara mu bi shi ta arfi da yaji mu ci ubanshi har sai ya mi a wuya..."yana huci ya fa a kamar zai ha iyi zuciyarsa saboda bacin rai.. Chief ya aga mashi hannu badan Ya arasa maganar ba yaja baki yayi shiru fuskar shi a murtuke.. "In har bashi yayi niya ba, ko da zamu rasa damar da muke da ita na zuwa gidan kurkukun bazan bari a tursasa masa ba, itama Unaisah ban amince ayi amfani da ita gurin shawo kan shi ba, cos zai ga kamar ni na sanya ta ne" Salsabeel ya an kalle sa cos shi harya riga daya tuntu6i Unaisah. Cike da takaici Big guy ke kallon chief da yai maganar "Haba Owais, Saboda shi kawai zamu fasa niyar mu"? "Omar, ba ina nufin zan fasa aikin mu bane, sai dai mu nemi wata hanyar..." bai are maganar ba, Big guy ya mike yana huci ya kama hanya zai bar backyard din.. Damuwa ta hana Taj furta kalma baima san me suke cewa ba. ewa chief yayi da sauri yabi bayan Omar, don bazai bari su sabamu sabani tsakaninsu ba dama kwanakin nan yana jin haushin fifita Danish da yake yi. Bayan tafiyar su, ya rage saura Taj da Salsabeel sunyi shiru babu mai magana acikin su. Ganin yadda Taj ya zabga uban tagumi ne yasa Salsabeel furta"Sir are you Okay"? Yamutsa fuska yai"kada ka damu, i'm okay, just banji dadin yadda an uwanka ya i bamu ha in kai ba" ya fada yana kallon Salsabeel "Amma Salsabeel babu dabara da zamu iya yi don mu shawo kan shi"? Shiru Salsabeel yayi yana nazarin maganar shi, wata dabara ce ta fa o mashi arai da sauri Ya dubi Taj "Akwai hanya aya" akagare Taj yace"Ina sauraronka" arka Unaisah, Ita ka ai ce zata Iya sa shi dole yayi..." lokaci aya Taj ya ha e rai, annurin fuskar shi ya auke, saboda zafin maganar Salsabeel daya ji. "Meyasa kace haka"? Murmushi Salsabeel ya anyi kafin ya fara zayyana masa dalilinsa nacewa haka! "in har ta umarce daya je zai je, saboda ya mutu akan Sonta, ba irin magiyar da banyi mata ba akan taje ta rokar mana shi amma ta iya saboda gudun kada ta yi silar da zai rasa ranshi, amma ina da tabbacin in har ka yi mata magana zamu iya cin galaba akan ta saboda kai mahafinta ne, bazata ki bin umarninka ba"... Tun da ya fara magana Taj ya tsare shi da ido batare da kyaftawa ba, bakomai yake tunawa ba face abunda idanun shi suka gane mashi, ari bisa ari ya yadda da maganar Salsabeel saboda shi shaidane akan mahaukacin son da suke ma junan su, duk da ya auke afa akanta amma yana jin zai iya zuwa gurinta don ya jarabata" Har salsabeel ya are maganar Taj bai sani ba, gyaran muryar da yayi mashi ne ya fargar da shi "Pls, ka taimaka koda sau aya ne ka jaraba yi mata magana.." fuskar shi amarairaice ya fada.. Wayar Taj ce tay ringing, kallon Salsabeel yayi"it is Okay, zan jaraba" ya fa a tare da mi ewa Yai picking call din "Sir, ina fata lafiya, naji shiru baku dawo ba" "Boss, Ka sallami Salsabeel ya tafi, kaima zaka iya tafiya..." amsa mashi yai da toh.. "Chief yace ka tafi, zai neme ka" mikewa yayi"pls sir, sai naji daga gare ka" jinjina mashi kai yai batare daya fur ta kalma ba. _________________________________ Su Batool na zaune a falo suna fira kusan su dukkansu in ka cire Unaisah da Danish sai ummi su kadai ke babu a cikin su... Sam basu lura da shugowarshi ba fira taja hankalin su, ganin babu Unaisah yasa shi juyawa ya nufi bedroom din... Adai dai lokacin ta fito daga bathroom, sanye da yar rigar wanka, zuciyarta cike fal da tunanin abunda suka tattauna da Salsabeel Wayar ce ta fara ringing, har zata dauka taji anyi knocking din kofar "Wanene"? "Ki bu e kofar ki gani" ras ta an ji gabanta ya fadi jin muryar daddynta, tana jin shakkar shi yanzu ba kadan ba saboda canzawar da yayi mata. "Unaisah ba zaki bu e min ofar bane"! Jikinta na 6ari ta je ta bu ofar, shigowa ciki yai tare da aza idanun shi kan fuskarta wani irin tausayinta ne ya kama shi. Cikin rawar murya tace"daddy Ina wuni" ta fada tana kallon shi Shiru yayi bai tanka mata ba hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.. Kasa jurewa tayi batasan sa'adda ta fa a kan kirjin shi ta kankame shi tana tana kuka tace laifin me na maka daddy? Meyasa ka canza min? Ka daina sakar min fuska, idan na gaishe ka dakyar kake amsa min idan na kira wayarka baka agawa, daddy don soyayyarka da manzon Allah ka fadamin laifin me nayi maka sai in nemi yafiyarka, wlh bana so kana fushi dani Daddy, kaifa mahaifina ne kasan hukuncin wanda iyayensa ke fushi da shi ...."sambatu taci gaba dayi batare data raba jikinta daga nashi ba.. Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne.. Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya aura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya an shafa bayanta cikin sigar lallashi Kafin ya fara magana "Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi "Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish... Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji "Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...." kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta asa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba an iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina fa a masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matu ar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...." yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba. "Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta an kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in fa a maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta. "Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata are maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!? wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matu aga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne... "Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me ku i? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa? "Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki" an numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..." bata are maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar aga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi.. Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba.. Da kakkausar murya ya