Sashe 96
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
da muke tazurai ba..." da zolaya yayi maganar, harara chief Ya dan watsa masa batare daya furta wata kalma ba Ya mi e Ya nufi kofar fita, da sauri big guy yabi bayansa a tare suka fito daga office din. Tsayawa fasalta haduwar isod headquarter bata baki ne, abun sai wanda Ya gani, lifter suka hau ta sauke su down, ta ko'ina ka kalla Jami'an isod ne sanye cikin kakinsu tun daga senior agents dinsu har izuwa jenior agent, duk inda suka bi cikin girmamawa jami'an suke sara masu, Har suka fito daga headquater din, kaitsaye suka nufi katafaren parking space din su, dankara dankaran motocine makil tare da bikes dinsu killace a harabar. Da sauri wani agent Ya bude masu backseat na motar da zasu shiga, bayan sun shiga kowan nan su Ya zauna, agent din dake jigilar daukar su Ya yi wa motar key cikin warewa Ya fara driving dinsu zuwa gida..... Dai dai lokacin da motar su ta kunno kai cikin gidan, Wayarsa ta fara ringing, lokacin da ya duba sunan mai kiransa yayi mamakin ganin aunt saratu, Cos Ya manta when last Yar tahalikar nan ta kira da sunan tayi magana da shi. Picking call din yayi tare da kara phone din a kunne, Cikin ladabi Ya yi mata sallah tare da gaishe da ita Ko sallamar shi bata amsa ba ta furta"Owais, bayan sallar magbrib, Ka same ni a pool yard, Ina son yin magana dakai"! Cike da bada umarni ta furta, bata jira amsar shi ba, Ta katse kiran. Kurawa screen din wayar ido yayi ba tare da yaftawa ba..." "Yalla6ai, Mun araso"! Big guy ne Ya fargar da shi, sam bai lura sun karaso ba, Fitowa yayi da sauri Ya nufi Cikin main falo din gidan Yana shiga bedroom dinsa, Ya rage kayan jikin shi, Ya shiga toilet domin Yin wanka, *HAJJATY* Safa da marwa Take Yi atsakar dakinta, tun safe take sa ran zuwan pravin shuru bai leko ba, Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, saboda abun da ya faru jiya yayi matu ar daga mata hankali. Yanke shawarar fita neman shi tayi, da sauri ta dauko mayafi ta yafa akanta, Tana kokarin fita suka ci karo da juna har saida ta bangaji kirjin shi, da sauri taja da baya tare da dafe gefen kanta da hannu daya "I'm sorry wifey, Ina zaki je ne"? yayi maganar yayin da yake nufar cikin dakin idanunsa akan fuskarsa From head to toe Ya kalle ta, farat aya ya gane akwai wani abu dake damunta, da alama ko wanka batayi ba. "Baki da lafiya ne" ya yi maganar tare da ru o hannunta suka zauna gefen gadon ta "Baki ji ina magana ba? Fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan kafadarshi Hankalin shi yayi matu ar tashi jin kukan hajjaty, yana daga cikin abunda Ya tsana arayuwarshi..... Cikin shesshekar kuka tace"pravin ina cikin tashin hankali, Saboda akwai mai bibiyar rayuwata, daren jiya bana acikin kwanciyar hankalina, a tsorace na kwana, ko baccin kirki banyi ba, ina ta jira ka dawo shiru baka zo ba..." Tuni yanayin fuskarshi Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, "Fada min meya faru dake a daren jiya? Wani ya shigo ne"?.... agowa tayi da kanta hawaye na sintiri kan kuncinta ta kwashe komai ta sanar da shi... Tafukan hannayensa ya daura kan fuskarta,A hankali Ya fara share mata hawayen ta "Ki yi hakuri, in sha Allah koma wanene ke naman ki da sharri kan shi zai koma, Allah Yana atare dake wani bai isa Ya cutar min dake ba! ...." bai kare maganar ba, tace"bansan ya zanyi ba, wallahi ina jin tsoron ranar da asirinmu zai tonu, pravin bana son abunda zaija mu rasa kimarmu da darajarmu a idon mutanan gidan nan, saboda ina ji araina akwai wanda ke son ya tona mana asiri shiyasa aka fara bibiyana.." ta fa a tana jan numfashi kafin taci gaba da cewa"saboda fargaban abunda Ya faru daren jiya, ko abinci banci ba tun safe har yau kamar mai azumi, wanka ma nakasa yin shi...." are maganar, tana kallon cikin idanunshi "Tuntuni saida naso In siya maki gida daban inda zakiyi rayuwarki cikin kwanciyar hankali, amma sai kika nuna bakison rabuwa da su....abunda nake jiye mana kenan... "Duk laifinka ne, Abunda kayi min awurin dinner din hateem shine Yaja har wasu suka fara zarginmu, kuma ni gaskiya bazan bar gidan nan ba, kawai ka nema min mafita ..." Jinjina kanshi yayi tare da ruko hannayenta acikin nashi"zan tambaye ki wani abu" daga mashi kai tai alamar toh "Idan kika kama 6era adakin ki Yana yi maki 6arna, kuma kinsan zai iya haifar maki da gagarumar matsala wani hukunci zaki masa"? "Meyasa kayi min wannan tambayar"? "Kedai ki bani amsa"! Shiru tayi jim kafin tace"hannayen da yake yin amfani da su wurin yin 6arnar su zan na asa, sannan in murje bakin shi ta yadda bazai iya daukar komai da shi ba...." murmushi pravin ya sakar mata"kin kawo shawara mai kyau.." arude tace"bangane me kake nufi ba" Bai bata amsar tambayarta ba, sai cewa yai muje bathroom In taimaka maki kiyi wankan da kika kasa" Ajiyar zuciya ta sauke tare da mikewa suka nufi toilet atare almost 18 mins Ya fito dauke da ita a hannunshi, dukansu sun daura towel a waist dinsu, Taimaka mata yayi ta sanya kaya, shima ya maida nashi "Tashi ki je kitchen ki shirya mana abinci mu ci atare" amsa mashi tayi da toh, Bayan fitarta da yan mintuna ta dawo hannunta ruke da try na kayan abinci, ta ajiye masu kan rug, saukowa yayi daga kan gadon suka zauna atare suna ci..... ___________________________ Bayan kammala sallar Magbrib, Owais Ya nufo pool yard din gidan baba obie, Jikin shi sanye da farar jallabiya, tunkafin Ya arasa Ya hango Hajiya saratu zaune kan kujera ta aura afa aya bisa aya, Hankalin ta na akan wayar hannunta da take dannawa Cikin kunnanta ta tsinkayi muryarsa"Assalamau alaikum" ba tare da ta kalle shi ba tace"wa'alaikum salam," Zukunnawa yayi daga gaban kujerar da take Cikin girmamawa Ya gaishe da ita, Har cikin ranta taji da in hakan da yayi mata sai dai bata nuna a fuska ba, wai don kada ya raina ta "Lafiyalou My son, ina fata Ka wuni lafiya? Ya aiki"? "Alhamdulillah.." "Bismilla ka zauna" ta fada tare da nuna masa chair din dake facing dinta, mi ewa yayi bayan ya zauna ya ago da ido ya kalle ta, babu alamun zata kalle shi "Mommy, kince kina son ganin na, zamu yi magana" sai da ta mula ta sha iska kafin tace"eh, magana ce mai mahimmanci, Ina fata zaka bani aron hankalin ka.." Amsa mata yayi da toh, tsawon mintuna biyar ta shanya shi, kafin ta fara kora mashi jawabi dangane da zuwan su Zahra, da alfarmar da suka nema a wurin ta...." tun da ta fara maganar, Yake dubanta da alamun rudani akan fuskarshi. "Ita zahran da ta kawo min maganar, tana aya daga cikin interior designers din da suka yi mana aiki aranar dinner din hateem a hall dinne taga yarinyar, sunan yarinyar ta wurinsu Angel amma asalin sunan ta Unaisah, har hotonta sun nuna min, sunyi kama sosai da yarinyar wurin ka," Cike da son jin arin bayani yace"ko ta fada maki sunan Baban Yarinyar da sunan mahaifiyar ta"? Shiru tayi tana kokarin tariyo sunan su ....can tace"na tuna, sunan mahaifin yarinyar zaheer tajudeen, mommynta kuma sunanta benazir" ." Bari na kira Daddyn nata, naji idan Ya san su" da mamaki hajiya saratu tace"oh dama mahaifin yarinyar yana atare da ku"? "Eh," ya bata amsa atakaice, har cikin ranta taji dadin jin hakan.... Phone dinsa Ya curo daga aljihu Ya danna ma Taj Kira, Tana fara ringing Ya saka wayar a handsfree don taji abunda zasu ce "Yalla6ai barka da marece, Na shigo gidan na taras baka nan.." "Ina agidan grandpa, zuwa anjima zan shigo" "Allah ya dawo kai lafiya" Am so nake na tambaye ka, Wa cece Aneelerh! Kamar na ta6a jin sunan abakin ka" "Yalla6ai ka kamanta ne halan, matar aminina ce uzair, kamar mahaifiya take awurin Angel ina..." murmushi hajiya saratu tasaki jin abun yazo mata cikin sauki "Zamuyi magana idan na shigo gidan" amsa mashi yayi da toh, bayan yayi rejecting call din Ya ago Ya kalli hajiya saratu dake kallon shi "Yarinyarsa ce..." "Alhamdulillah, Yanzu gobe da yaushe zasu zo ganin ta? ta tambaya tana kallon shi "Duk lokacin da yayi miki, su zo kawai" murmushin gefen fuska tasaki, Taji dadin yadda yake bata girma "Nagode my son, bari nasa akawo mana abun sha" da sauri yace"ina so zan shiga wurin baba" "Okey, mu tafi tare" mikewa sukayi atare suka jera suna tafiya, abun ba karamin dadi yayi mashi ba, tsawon lokaci basa jituwa da juna, sai gashi silar neman unaisah da yan uwanta sukazo yi Allah Ya ha a kan su, Har fira ta fara jan shi da ita, a haka har suka karasa dakin baba obie... Idan muka koma 6angarensu Hajiya Layla dake a asibiti, wuraren arfe 8 na dare, Hospital staff suka fara sallamar mutanan da ke zuwa dubiya, saboda a dokar asibitin karfe takwas na safe visitors suke zuwa da zarar takwas Na marece Yayi kowa zai tafi za'abar majinyaci karkashin kulawar nurses Hajiya layla tace ita fa ba inda zataje, dole ta kwana don ta kula da yar ta, dr shureim ma ya goyi bayanta, tunawa da barazanar kashe benazir da ake Yi, Idan suka tafi ba lallai nurses su san lokacin da za'a farmake ta ba, duk da akwai cctv camera a kowani daki na marasa lafiya, bayan hakan asibitin Yana da tsaro sosai, kawai dai bai yarda subar benazir ta kwana ba tare da wani nata akusa ba Hospital staff din basu Yi masu gardama ba, ganin sanannu ne a idon jama'a, kuma da ma ire irensu sunayi masu alfarma, kodan saboda matsayin dake gare su, musamman hajiya Saratu da takasance former firstlady ta kasar, tun da ta sanya baki a maganar suka amince hajiya layla ta kwana tare da ita. Gaba dayansu sun hallara a harabar ajiye motocin asibitin, Sun fito domin tafiya gidajen su, Mami da abie suna atsaye, Ga Aneelerh da Zahra