← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 50 OF 247

Sashe 50

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ HAJIYA SARATU _safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abun da Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanu arta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu warin gwiwar yi mata haka? ru e qugu tayi da hannu aya fuskarta babu annuri_ Maganganun da suka Tattauna jiya ita da su Har excellency ta soma tariyo bayan fitowarsu daga hall kafin su nufi gidan prime minister. "Meyesa pravin zai ja hannunta abainar jama'a? Menene alakarsu? Wai ku ba ku zargin wani abu atsakanin su"? Hajiya laurace ta fada babu wasa akan fuskarta "Najima ina zargin matar nan, na dai yi shiru ne ban fada maki ba, saboda bana so in shiga tsakanin ki da mijin ki, amma ni kwata kwata hankalina bai kwanta da ita ba, tun daga kan yanayin yadda take daukar wanka zaki fahince akwai wata a kasa ba banza ba, ni ay ban ta6a ganin yar aikin da ta samun anci kamar hajjaty ba"! Her excellency muhibbat ce tai maganar, Hajiya jamila tace"yanzu wani hukunci zaki yi masu"? ta fada tana kallon hajiya saratu. Da sauri Hajiya madina tace"please, ku daina tunzurata ku bar ta taji da abun da ke damunta, ni banga abun aga hankali a maganar nan ba!" Hajiya saratu da ke sauraronsu aya bayan aya sai da ta cika ta batse kafin tace "Wallahi bazan yalesu ba! Daga ita har shi sai sun fuskanci 6acin raina, sai tayi danasanin kasantuwarta yar aiki a gidan nan"! Ta fada a tsiwace tana huci "Ni shawarar da zan baki kawai ki kore ta daga gidan ta koma can kasarsu acigaba da bautar shanu, idan ba haka ba Allah ka ai yasan muna isar da take shirya maki, wara tun wuri ki yi maganinta kafin ta jaza maki matsala" Acewar hajiya Muhibbat Dafa kafa arta hajiya laurat tayi"idan da zaki bi shawarata kada ki tanka masu! Nasan yanzu hankulansu atashe yake saboda sun san dole ki tuhume su, abun da yakamata ki yi shine ki manta da zancen hukunta su, ki yi tamkar babu abun da ya faru, za su yi zaton kin kyale su ne, ki bari sai sun shagala tukunna ke kuma ki fara bincike akan su, ta haka ne kadai zakisan meke atsakanin su amma yanzu idan kikace zaki hukuntasu to ba za ki san menene alakarsu ba, kwara ki fara bin diddiginsu har zuwa lokacin da zakiyi nasarar kama su dumu dumu" Jinjina kai hajiya saratu tay alamar gamsuwa da shawarar Hajiya laurat.. Bayan ta dawo daga duniyar tunanin taja gauran Numfasawa ha i da an jinjina kanta, cikin takun sauri ta nufi wayarta dake ajiye kan pillow ta dauka ta kira landline na kitchen. Tana fara ringing akayi picking, kara wayar tai a kunnanta. "Inason ganin Marwa, ta same ni adaki bana son bata lokaci" ta fada tare da katse kiran ta ajiye wayar Cigaba da zagaye bedroom din tayi, yayin da take dunkule tafin hannunta na dama tana tura shi ana hagu kamar ar dambe. Knocking kofar da akayi mata ne yasa ta dakata. "Wanene"? "Aunty ni ce marwa" "Okey shigo ciki" Turo kofar tayi, Jikinta sanye da uniform na ma'aikatan gidan ta shigo, cikin girmamawa ta gaishe da hajiya saratu, bata amsa mata ba, sai tay tamkar ba ta ji me tace ba. Tuni marwa ta sha jinin jikin ta, tsoranta kada ace wani laifin ta aikata da yasa hajiya saratu ta kira ta don tasan halinta masifaffiya ce. Muryarta na rawa tace"Am.. Aunty gani, naji kina nemana" Wurga mata harara hajiya saratu tayi da sauri ta dukar da kanta kasa Tsawon lokaci bata tanka mata ba, gani ta ke kamar zubda ajine ta nemi taimakon yar aiki, sai dai ba yadda zata yi itace kadai hanya mafi sauki agareta. Zama tayi gefen gadonta, cike da isa ta dubi marwa"ke zonan"! da sauri marwa ta dawo ta zukunna agabanta. "Wani aiki nakeso kiyi min, bana so kowa ya sani daga ni sai ke! Na yaba da hankalin ki ne shiyasa na za6e ki saboda nasan zaki Iya......" Tun da tafara magana marwa ta soma zare idanunta cike da fargaba. "Kafin na fa a maki, zan gindaya maki sharadi, Idan har na kuskura naji maganar nan abakin wani, ko kika bani matsala wallahi thumma tallahi na lahira sai yafi ki jin dadi...." Wani irin yawu marwa ta ha iya jiki na bari tace"in sha Allah zan kiyaye." Ta6e baki tayi kafin ta aura da cewa" me kika sani dangane da head maid din gidan nan? ya mu'amalarta daku take? Sannan Wacece aminiyarta acikin ku? Shin tana fada maku sirrinta"? Shiru marwa tayi aranta ta ayyana to fa! Ko me hajjaty ta aikata ma aunty masifatu da take neman karin bayani dangane da ita? Watakil watan cin ubanta ne ya tsaya A fili kuma tace "Abun da nasani dangane da ita, macace mai saukin kai, tana da mutunci kuma tana kyautata mana, ba ta shiga sabgarmu, sannan bata cika zama yin fira da mu ba, macece mai kamun kai bata da surutu, sannan bata da aminiya acikin mu balle har wani yasan sirrinta, wannan shine Iya abunda sani" Tur6une fuska hajiya saratu tayi, ita ba haka taso taji daga bakin Marwa ba. "Okey, ki nutsu ki saurareni," jinjina mata kai tai "Daga yau inaso ki fara shisshige mata, saboda ina zarginta, inason kisan duk wani sirrinta, ki zama aminiyarta, bayan haka duk wani motsinta ya kasance a tafin hannunki, idan har kikaga wani abu ba dai dai ba, to kiyi hanzarin sanar dani," amsa mata tayi da toh "Idan har na samu abun da nakeso nayi maki alkawarin zan baki mukamin da take da shi agidan nan, bayan haka zanyi maki kyauta ta musamman, kin dai san wacece ni, basai nayi maki bayani ba" Wani irin farin cikine Ya lullu6e marwa musamman da taji Hajiya saratu ta ambaci zata bata mukamin hajjaty ga kuma kyautar da zata samu, aranta ta udiri aniyar saita yi ma hajjaty kutse koda kuwa bata kama ta da laifin komai ba, ita zata ala mata sharrin da za'a sauke ta daga kan mukaminta. Shu'umin murmushin gefen fuska tasaki. "Baki da matsala dani aunty, in sha Allah zaki samu abunda kikeso" "Zaki iya tafiya" mikewa marwa tayi zuciyarta cike fal da murna, dama ta jima tana jin haushin hajjaty saboda yadda tayi masu zarra agidan, komai itace akan gaba, gata head maid ga farin jini awurin mutanan gida, bayan ba wani aiki takeyi ba acikin gidan sune masu wahalar girka abinci, ita aikin ta tsara abunda za'a girka ne da kuma bada umarnin yadda abu zai kasance. Dole ta ana mata tarkon da bazata Iya fidda kanta ba, ko dan ta wace mukamin ta, wannan alwashine ta daukarwa kanta! Ta fada aranta, yayin da take nufar hanyar komawa kitchen Bayan fitar marwa, hajiya saratu ta sauke ajiyar zuciya, yanzu ne ta samu kwarin gwiwar shiga toilet yin wanka Lokacin da fito, A zaune ta same shi gefen gadonta, sam bataji alamun shigowarshi ba. Tun da ya ago suka hada ido da ita yai saurin sunnar da kanshi kasa, wani irin nauyinta yaji, baisan ta ina zai fara shawo kanta ba, Yasan dole ta tuhume shi akan abun da Ya faru jiya. Kau da ido tai daga kan shi, Ta juya ta nufi closet, jim ka an Ta fito har ta sanya riga bubu ta atamfa, gaban mirror ta tsaya tare dakai hannu ta dauki turare ta soma feshe jikin ta da shi, yadda ta share shi kamar batasan da zaman shi a dakin ba. Shi kuwa gogan Ya kasa dauke idanunsa daga gareta. Kamshin turarenta ne yakai mashi karo har ya gaza jurewa duk da shakkarta da ya ke ji arfin hali yai wurin furta"Har Yanzu fushi kike dani? Banza tayi da shi Mikewa yai tsaye ya nufeta, daga bayanta ya dan dakata Yana bin ta da kallo. Kafin cikin sanyin murya yace "Tun jiya nake ta so na baki hakuri, nasan ban kyauta maki ba, ni kaina ba'a hayyacina na aikata hakan ba, bansan meyasa na ruko hannunta ba, wallahi sharrin shai anne" Murmushin gefen fuska tasaki, ba tare da ta bari ya gani ba, dama dagangan ta dauki wankar da zai zautar da shi "Na cancanci kowani irin hukunci daga gareki, a shirye nake dana kar6e shi, ni dai bana son 6acin ranki" ya fa a tare da aura kansa saman kafadarta saboda karfin hali irin nashi Lumshe idanunsa yai tare da shakar kamshin turarenta. "Kinyi shiru baki ce min komai ba" sai da ta mula tasha iska tukunna Tace"laifin me kayi min"? "Kin riga da kin sani" "In dai dangane da abunda ya faru jiya ne to ka manta kawai, bana son tada maganar, ko alokacin abunda yasa raina ya 6aci saboda ina kishin ka ne banji dadi ba, amma yanzu komai ya wuce" Tsabar mamakin kalamanta yasa shi saurin agowa yana duban fuskarta ta cikin mirror. "Amma dai wasa kike min ko"? Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"na taba maka wasa irin wannan"? Girgiza kanshi yai"a'a, baki taba min ba, amma dai nayi mamaki, Allah yasa ba mafarki nake ba" juyowa tayi suka fuskanci juna, fuskar ta dauke da ayataccen murmushi ta aura hannayen ta a kan kafadunsa. Lamarin ya aure masa kai gaba daya ta canza mashi kamar ba hajiya saratun daya sani ba. Cikin sanyin murya tace"hubby, kada ka ara maimaita kuskuran da kayi, bana so, kasan inada kishi, akan ka zan iya komai daga ciki har da kisa" Zaro idanunsa yayi"in sha Allah hakan bazata faru ba, zanyi kokarin ganin na kiyaye duk wani abu da zai bata maki rai" Ba zato ba tsammani yaji tayi huggin insa tare da zagayo da hannayenta kan waist dinsa, tuni yafara jin shi awani yanayi. Sumbatar wuyansa tayi kafin ta dago da bakinta saitin kunnanshi cikin muryar ra a mai hade da kwarkwasa tace"fadamin me ka ke so nayi maka wanda zai faranta ranka" "Nagaza yarda da abinda kike fada min, anya kuwa kece?
Chapter 50 · 0% Book details