← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 126 OF 247

Sashe 126

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

rayuwar zeenatu! "May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya fa a tare da dukar da kan shi asa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba. Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice.. "Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing, "Zan aga kira" "Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne? Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba" Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan? "Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku" "Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu" Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya auki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli. Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi. "Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta. Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..." Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba. Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining ___________________________________ Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa... Gaba aya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru "Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula.. Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara. Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da mi a mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta are maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah.... Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, bu e baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, an mintuna alilan Benazir ta fara gyangya i idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." an zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu aya, dakyar take bu e idanun ta masu auke da matsanancin bacci ta urama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel" a matu ar ru e Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa. Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta aga masu hankali. Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel. A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ara haduwa ba, lokaci aya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta. "Azeezaty! Ke nake jira muje ko"? Dr jazz ne yayi maganar yana daga tsaye bakin kofar akin, mi ewa tayi daga kan kujerar, kamar wadda aka zarewa laka, ta sunkuyar dakanta saitin fuskar Benazir ta manna mata sumbata har sau biyu kafin ta juya taje ta auko backpack dinta, ta kalli hajiya layla mi a mata hannu tayi alamar tazo, da sauri unaisah ta arasa gareta, hajiya layla ta rungumota a kirjinta. "Toh Azeezaty, mungode Allah yasaka maki da alkhairi, Allah ya baki ilimi mai amfani duniya da lahira, Allah ya baki miji nagari, zamuyi kewar rashinki, an zaman da mukayi dake mun saba dake, benazir zatayi kukan rashin ki, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah yasakama iyayenki da alkhairi..." amsa wa tadinga yi da ameen kamar kar su rabu da juna. "Ki gaida min da mutanan gidan, in sha Allah zamu zo wata rana har gidan naku" Murmushi Unaisah tayi"Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ara ma mamana lafiya, nima daddyna yace zai kawo ni gidan ku" murmushi hajiya layla tayi taji dadin maganar, sallama sukayi da juna, A hankali take tafiya tana waiwayon Benazir dake kwance tana ta sharar baccin ta.... Dr jazz harya fara gajiya da jiranta, sai faman duba wrist watch dinsa yake yi baya son chief ya karaso don yasan bai son jira. Har fa ta kusa fitowa daga dakin sai kuma ta juya da sauri ta koma gaban gadon Benazir ta manna mata peck a goshin ta. Ganin abun nata bame karewa bane yasa dr jazz shigowa dakin Ya tasa keyarta gaba suka fito, baiwar Allah tana tafiya tana waiwayon dakin hajiya layla tana tsaye bakin kofar room din, hawaye sun cika idanunta har saida suka bace ma ganin ta kafin ta juya ta koma ciki zuciyarta cike fal da kewar Azeezaty. A dai dai lokacin da suka fito, hamshakiyar motar chief ta kunno kai ta entrance gate din asibitin yar uban su launin ash colour har sal i take da daukar ido, yanayin yadda motar take tafiya slowly yayi matu ar jan hankalin visitors dake zarya a arean wurin, suka bi da ido har saida ta tsaya a parking sace. "Muje, Ina tunanin shi ne ya karaso" jaz ya fada tare da jan hannunta, tunkafin su arasa take ta kallon hamshakiyar motar, tayi mata kyau, lokacin dayazo kawota ba irin wannan suka hau ba. Bayan sun arasa gaban motar, ta ciki aka bu e mata cardoor din wani dadda an fragrance ne Ya daki hancinta, mai ha e da sanyi A.c. "Ki shiga ciki" jazz ya fa a tare da nuna mata hanya, sunkuyar dakai tayi tare da shiga ta zauna, wurga ido tayi akan shi har saida taji gabanta ya fadi saboda wani kyau da taga yayi mata, ya kare gefen fuskarshi da phone dinsa, da alama waya yakeyi, fuskarsa tana asanye da mask. Hadadden yard din dake ajikin shi Senator cotton material
Chapter 126 · 0% Book details