← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 146 OF 247

Sashe 146

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ta cika za ewa agane sun san juna da jimawa fuskar Aneelarh da fara'a tace"lafiyalou, Zahra tana gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.." "Lafiyalou Aunty Aneelerh" Dr shureim Yace"Babyn Benazir, Ni baki ganni bane, tun da kika ga mamanki kin manta da mu ko" an murmushi tay"ba haka bane ya shureim, kana araina, ina wuni, ya su mami? ina zeenatu"? "lafiyalou Azeezaty, su mami suna gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.." "Lafiya lou, naga jikin mamana yayi sau i, ubangiji Allah ya ara mata lafiya" "Ameen babyn mamanta" yar dariya sukai, kafin wani ya kara magana wayar hannun shi tay ringing daga cikin aljihunsa, a hanzarce Ya curota Ya duba sunan me kiransa, mikewa yai tare da kallon Benazir dake kallon shi"Mami ce"? "A'a bakuwar number ce, bari na aga naji" cikin sauri Ya nufi hanyar fita daga sitting room din, zuciyar shi cike fal da tunanin yarinyar daya tsaya ma shi aran shi, baiso kiran ya katse mashi kallonta da yake yi ba, bai kula ba tun da ya mi e Batool tabi bayan shi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, harya kusa fucewa ya an juya don ya saci kallonta karaf suka ha a ido da juna, sanyayyar murmushi ya sakar mata tare da aga mata hannu, kunyar shi ce ta kama ta da sauri ta juyar da kan ta gefe aya, mutumin ya kwanta mata aranta tun da Unaisah ta bata labarin kamannin su, yau da ta gan shi face to face sai taji ta kamu da aunar shi. Da ido Unaisah tay ma Batool nuni da data gaida su Aunty Aneelerh muryarta na dan rawa ta furta"Aunty Anila Ina wuni" da fara'a Anila ta ce"lafiyalou sister fatan mun same ku lafiya" "Muna lafiya" Bata kau da ido daga kallon fuskar Batool ba, tana so tasan wacece ita? Ko itama aya ce daga cikin yaran da zahra ta bata labarin badakalar da aka sha akan su ranar dinner din prime minister, ko kuwa dai yar uwar chief ce? Ta ayyana acikin zuciyarta, Ta dai bar abun aranta har zuwa time da za su yi magana da unaisah, tayi zurfin acikin tunanin ta taji hannun unaisah akan nata a hankali ta kau da ido daga kallon batool ta dubi unaisah, kar6ar junaid tay daga hannunta ta kwantar da shi kan laps inta, ta ura ma shi ido tana kallon shi kamar zata lashe shi.. "Yau dai na kawo maki babynki, da kike ta zumudin son ganin shi, Ina fata na wanke laifi na" ta fa a tana le en fuskarta, jinjina kai Unaisah tay"da har nayi fushi, da ace baki kawo min shi ba, zansa daddyna ne ya kawo ni har gida don inga anina, amma yanzu kin wanke kanki agurina" ta fa a da murmushi akan fuskarta Anila tace"Tun acikin mota yake ta sharar bacci, Kamar wanda Yasha waya" "ay ko dai yanzu zan tada shi, saboda ba karamin missing din shi nayi ba...." kafin ta are maganar Baby junaid Ya fara mutsu mutsu alamar zai farka lura da hakan ya aga hankalin Aneelerh, fargabanta kada junaid ya kwafsa masu, tasan muddin ya farka zai yi wuya in bai gane Angel ba kamar yadda kwanaki ya shaidata a hoto sau in ta ma dr shureim ya fita daga akin dama shine damuwarta bata da matsala Benazir tasan komai already sunyi plan. burinta Ya farka su ha a ido da juna matsawa tay da fuskarta saitin ta shi ta kurama shi idanunta, mi ewa batool tayi ta dawo gefen Unaisah ta zauna tana kallon junaid ba ta son ta nuna zumudinta akan shi saboda unaisah ta kwa6eta, shiyasa ta i sakin jiki kada tay wani abu ba dai dai ba. Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. Da wata irin kasala Ya karasa bu e idanunshi, sun ka a jawur da su, biji biji yake ganin fuskar mutun a saitin tashi, red lips dinsa na kerma ya furta"mommy," shiru yaji ba'a tanka mashi ba, a hankali ya aura yatsun hannayen shi akan fuskar Angel ya shafata har zuwa saitin la66anta ya an matsa su kamar ya samu abun wasa, sam bai gane wacece ba saboda idanunsa sun disashe "Mommy" ya sake ambaton sunan yana faman yamutsa fuskar shi. Jin shiru taki amsa mashi ne yasa shi murza idanunshi da yatsunsa suka washe ya sake duban fuskar Unaisah dake yi mashi murmushi, shiru yayi yana kallonta yanayin fuskarshi ya nuna kamar ya ru e da ganin ta, tsawon mintuna bai tanka mata ba, kowa yayi shiru suna jiran ganin me zai yi Tsinin hancinta Yaja da hannun shi, ta lumshe ido tana dariya, shima sai ya kama dariya kamar sun san juna, lamarin ya daure ma su anila kai, da alama junaid yayi azan mafarki yakeyi Cikin sanyin murya ta furta"My little bro" Lokaci aya yanayin fuskarshi Ya canza Ya kura mata ido Yana kallonta ba tare da yaftawa ba, Unexpectedly taji ya furta"ANGEL"? Waro idanu waje tay tare da bu e baki ta dubi Batool itama mamakinne Ya kamata saboda ta fa a mata basu ta6a ha uwa da juna ba wannan ne karo na farko Sam Ta asa furta kalma har sai da taji Ya ce"Angel uhm? Angel ina ne? Yayata" Sautin muryarshi baya fita dakyau ta fahimci kamar baya jin dadi, ruwan hawaye ne suka taru akan fuskarta, cike da jin dadi ta jinjina mashi kai la66anta na kerma ta furta"ni ce" Aneelerh sai faman sakin murmushi ta ke yi dama tasan zai yi wuya in bai gane ta ba. Still da ru u akan fuskar shi, kokwanto yake, kamar bai yarda ba, Lumshe idanun shi yai tare da bu e su. ago da kan shi tay tare da kwantar da shi saman kirjinta, ta tallabe shi tare da manna mashi sumbata har sau uku kan cheeks dinsa Gyaran muryar da Aneelerh tay mata ne yasa ta ago adabarbarce ta dube su sam ta manta da Benazir duk saita kama kanta tana faman rarraba idanu akan su, Basarwa Benazir tayi tamkar bata ji me Junaid yace ba sarai ta fahimci ru ewar da Angel tayi tasan don saboda ita ne kada ta gane wani abu. Tun da Aneelerh tay gyaran murya junaid ya kalle ta tayi azan zai sanya rigima akan ta auke shi kamar yadda ya sa6a yi ma kowa iwuya amma wani iko na Allah sai ta ga bai yi ba, aranta ta ayyana watakil ya ga ne Angel dince shiyasa ya yarda da ita, mi a hannu Batool tay da niyar ta dauke shi Ya ma e kafa a alamar ba zai je ba. Anila tace"sai kunyi hakuri da shi, baya da koshin lafiya" atare suka ha a baki gurin furta"Allah ya bashi lafiya" ta amsa masu da ameen "Kana bu atar wani abu"? Cikin kulawa unaisah tay maganar tana kalon fuskar shi Ya nutsu Yana ta kallonta "Batool zubo mashi juice a cup" unaisah ta fada tare da kallon ta da sauri batool ta auko juice din da dr shureim Ya aje a cup bai sha ba ta mi a wa Angel ta kar6a ta kanga mashi abaki A hankali ya fara sha. "Naji shiru yaya shureim bai dawo ba" ta fa a tare da kallon Anila "May be bai kammala Yin wayar ba" acewar Anila Sauke ajiyar zuciya ta anyi har yanzu da sauran damuwa akan fuskarta. Wrist watch din hannunta ta duba karfe aya da rabi "Bansan lokaci yaja har haka ba," Anila tace"nasan mami zata neme ni" "Batasan kin fito bane"? Ta sani amma ce mata nayi gidan ku zanje" Da zolaya Benazir tace"Mai karya dan wuta dai," dariya Anila tay.. "Naji shirun yayi yawa, bari naje na duba Ya shureim" ta fa a tare da mi ewa ta fuce daga dakin Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke tare da kallon su Unaisah, Hankalinta Ya kwanta da ganin yadda junaid Ya saki jiki da ita. "Aunty Anila ki bani wayarki mu dauki hoto, Na bar nawa a daki.' Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. "Okay" ta fa a tare da zaro wayar tace"bari nayi maku pics din da kaina, ku gyara" hotuna ta fara aukar su kala kala wani daga zaune wani daga tsaye wani kuma sukayi atare su uku junaid dai yana a ma ale da Unaisah Batool tay kwakwar ta auke shi Ya i yarda da ita, bayan sun gama aukar hotunan Anila ta ibi snacks a dan plate ta ba unaisah" ki bashi yaci, da safe baici abincin kirki ba" kar6ar plate din tay ta fara bashi abaki Yana ci. Lokacin da Benazir ta fito waje neman Dr shureim A tsaye ta hango shi jikin Motar shi yana yin waya, da sauri ta nufe shi adai dai time din ya kammala yin wayar"ya shureim lafiya naga ka dade baka dawo ba" fuskar shi babu walwala Ya ce"Zeenatu ce ta kira ni da layin tani, tana kuka bata jin dadin jikin ta tace inzo gida tana son gani na" "Baiwar Allah, dole taji ba da i ya shureim, Banji dadin yadda Uncle yake takura rayuwarta, ni nasan hada damuwar hakan" ta fada cikin sanyin murya tana kallon shi "Ka tafi ya shureim, Inyaso sai mu tsaida me abun hawa Ya kai mu gida" girgiza kai yai"a'a bazan iya tafiya nabarku ba, zan bata hakuri ta jira zuwa lokacin da zamu koma gida" ya fada yana kokarin danna mata kira da sauri Benazir ta ru e hannun shi amarairaice ta furta"a'a ya shureim kada ay haka, tunda kaga ta kira ka da akwai wani abu dake damunta, tana son ganinka, kuma kaima nasan hankalin ka bazai kwanta ba in har ba zuwa kai gurin ta ba..." shiru ya yi jimm yana nazarin maganarta, aranta Allah Allah take Ya tafi duk don saboda ta samu taj yace zai kaisu a motar shi agowa yai da ido Ya dube ta"zan tafi amma zan dawo zuwa anjima in auke ku" Amsa mashi tay da toh ka kula min da kanka" murmushi ya anyi mata harga Allah baiso
Chapter 146 · 0% Book details