← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 174 OF 247

Sashe 174

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

mata alkawarin zai rufa mata asiri, ka ji masoyi na gari samun irinsu zaiyi wuya aduniyar nan. Zaki mutum ne mai ha uri ga tawakkali. Bayan ya goge fuskar shi, Ya rufe murfin motar, ya zaro shades ya sanya ma idanunsa. Bayan tafiyar Benazir da yan mintuna Sai ga Sir Mubarak da Alhaji Musa sun fito daga garden din gidan, fuskokinsu auke da fara'a da alama sun ji da in firar da suka yi. "Naji da in karramawar da aka yi mana, yanzu sai yaushe mahaifin nata zaizo Abujan ko mu zamu je can Jos dinne? cos ina son ganawa da shi game da zancen auransu" Alhaji Musa ya ce, "kada ka damu, basai kunje can in ba, tun da har ni na amince da aurensu, shima zai amince ne." murmushi Sir Mubarak yayi, "Mutumina ka faranta raina, Allah ya ara dankon zumunci a tsakaninmu," Ya amsa mashi da ameen. "Ba zaka shiga ciki ka gaisa da madam ina ba" "Ban shirya ha uwa da surukata ba, sai zuwa na gaba in sha Allah." Ya fa a yana bin compound din da kallo yana ci gaba da yin murmushi. Fitowa Zaki ya yi daga motar, fuskar shi da fara'a ya ce, "Daddy, mun riga da mun gama magana da ita, harma ta koma ciki." Farin ciki ne ya lullu6e Sir Mubarak, "Uncle, ina godiya da damar da ka bani, Allah ya ara girma da aukaka" ya fa a yana kallon Alhaji musa, Murmushin gefen fuska ya sakar ma shi, "Kada ka damu, na dauke ka kamar ana, komai zan iya yi saboda farin cikin ka." Bayan sunyi sallama da juna, Alhaji Musa Ya koma gidan, su kuma suka shiga motar su. Kwata kwata Sir Mubarak bai lura da yanayin fusakarshi ba saboda shades din da ya sanya ya rufe idanun shi ya hana yaga eye balls dinsa wa anda suka kada jawur tamkar garwashin wuta. "Bani labari mana my son, ya kuka yi da ita?" Shiru yayi jim kafin ya cije ya ce, "ta amince Daddy, " "Alhamdulillah, yanzu da yaushe zamu zo nema maka auren ta?" Tamkar baison furta maganar ya ce, "Ba yanzu ba daddy, mun yi da ita sai bayan na sake samun hutun aiki zan zo Nigeria sai a aura mana auren" farin cikine ya cika Sir Mubarak. "Ina tayaka murna my son, ni dama nasan da wuya a samu macen da zata yi rejecting dinka, saboda kai din na musamman ne." Murmushin takaici ya alo kan fuskar shi ba tare da ya iya furta kalma ba, a ranshi ya riga da ya yanke shawarar barin asar gobe, kwara ya nisanta kanshi da ita in ba haka ba zai iya zaucewa. *MEETING ROOM* Around arfe 11 na safe hamsha an motoci suka fara kur owa ta entrance gate din Isod headquarter, jigunannun gaske da matsakaicin gudu suke tururuwar shigowa a jere har kusan guda shida, kowace mota tana da tinted. A parking space motocin su ka yi parking, a hanzarce Jami'an dake sintiri su ka yi saurin arasawa bakin car doors in suka bubbu e masu kofar.... Chief Owais ne ya fito tare da Big guy, motar bayan tasu Senior agents in su ne. Bayan su sai Commender james Ya fito shima tare da sauran sojojin da suka zo, kowannansu yana asanye da kakinsa.. Motar arshe General in sojoji ne. A gaggauce Jami'an dake kewaye da su sukayi hanzarin buga kafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su kamar zasu zu unna masu tsabar ladabi. Basu tsaya 6ata lokaci ba, Cikin takun dattako suka nufi Secure operation center duk inda suka gifta sai amshin turarensu ya gauraye da iskar gurin dadda an gaske, kuma duk hanyar da suka bi jiki na 6ari jami'an dake a gurin ke sara masu, sai dai kawai su aga masu hannu alamar sun kar6i gaisuwar tasu. Bayan sun hau lift ta sauke su a third floor, A bakin awani Katafaren Meeting room ( akin taro na sirri) wanda gaba ayan shi a kewaye yake da zallar glass launin blue sky, wanda ke a waje bazai iya ganin na ciki ba, bayan haka bangon gilashin akin soundproof ne irin wanda ke hana sauti fitowa waje, duk wani abu da za'a tattauna iya cikin akin sautin ke tsayawa na waje bazai ta6a iya ji ba.. Gaba aya sun nutsu suna jiran kofar ta bu e ma su, biometric authentication ce sai ta tantance mutun kafin ta bashi iznin shiga.. Tafin hannu Chief ya aura kan saitin na'urar ta yi screening din shi ta haska kwayar idanun shi kafin ofar ta fara sliding slowly har ta arasa zuge kanta.. Walking majestically suka fara shiga aya bayan aya cikin katafaren Meeting room din, U.s armies din dake a tare da su sai faman jinjina kai suke saboda awatuwar dakin taron yayi matu ar burge su, cos ba su tsammaci zai kai ha uwar meeting room in su na America ba, wata irin ni'imtacciyar iskar A.c ce mai fita da umi ta fara ratsa hudojin gashin jikin su irin mai sanyaya zuciyar mutun ta kwantar masa da hankali yaji shi a wata duniyar daban. Wani katafaren zunguraren table ne a tsakiyar akin shape insa kamar rectangle ya ke iya jikinshi abun burgewa ne sai sal i da daukar ido yake, ga wasu high-end Chairs kewaye da shi ga wasu ha un Microphones da Laptops a gaban kowace kujera, bangon dake fuskantar table in wani tafkeken large screen ne. Komai na yin meeting an tanade shi a akin. A tsanake kowannan su ya ja kujera ya zauna, suka fuskanci junan su, bayan sun daidaita nutsuwarsu akin yayi tsit na an wani lokaci, kowa da abunda yake sa awa acikin zuciyar shi... Abu na farko da suka tsara yi ma junansu barka da zuwa da kuma gabatarwa.. Dakin taron ya yi tsit a daidai lokacin da Chief Owais ya mi e daga kan kujerarsa tare da tawagarsa, domin fara gabatar da kan shi cikin dattako ya fara magana yana duban kowannansu.... "Good morning everyone, i'm director Owais Sharafudeen Obinna, the Chief of Isod, With me are my team members," ya fa a tare da yin nuni da su, "Deputy Director General Omar Musa Wadata, Chief of Operations Ahmad Hassan, Chief of Intelligence Commander Haroon, and Senior Agents Dr. Zarah Saeed, Agents Ethan Kim and Jabeer Osman." yanayin yadda yake gabatar da su ba aramin burge su yayi ba komai nashi cikin aji yake yin shi, duk wanda ya ambaci sunanshi zakaga ya saki ayataccen murmushi kan fuskar shi.. "Muna yiwa kowa barka da zuwa" ya fada tare da komawa kan kujerarsa ya zauna suma duk suka zauna. The next person General Noah ne wani bayerabe ba i mai jiki ya mi e yana gyara necktie insa, "Hello everyone, nice to meet you all, I am General Noah the General Officer Commanding the Nigerian Army, It's an honor to be here today." ya fa a fuskar shi da murmushi kafin ya koma ya zauna. Cike da kwarin gwuiwa Commender James Ya mi e tare da tawagarsa su shidda, "Hello everyone, I am Colonel James, the U.S. Commander of the Joint Task Force. I am joined by my team.." ya fa a tare da nuna U.s armies din dake gefen shi, Ya fara zayyana sunayen su, "Major Smith, Captain Lewis, Canal herry and Lieutenant Thompson tare da Jackson lee, munayi ma kowa barka da zuwa, mun ji da in gayyatar mu da ku ka yi" gaba daya sunji dadin gabatarwar da yayi bayan sun zauna akin yayi shiru na an wani lokaci. Kafin Chief ya numfasa calmly ya cigaba da kora jawabi, "Thank you, everyone, Let us proceed with the agenda, we are gathered here today to discuss a grave and urgent matter, already mun riga da mun san abun da ya tara mu, dangane da yaran da sojojin America suka tsinta a dajin Evil forest suka dam a case dinsu a hannun hukumar mu ta Isode..." gaba aya sun nutsu suna sauraron shi hadi da kallon fuskar shi, an dakatawa yayi kafin ya daura da cewa, "...bayan bincike da hukumarmu tayi mun samu bayanai daga gurin yaran, wato wasu miyagun matsafa ne suka iri wani gini a karkashin asa wanda suke kira da Gidan Kurkukun kaddara! Inda suke kulle mutanan da basu ji ba basu gani ba ta arfi da yaji suke killace su, anan suke aikata duk wani fasadin su.." gaba aya hankalin Jami'an ya karkata akan shi cos ba komai suka sani dangane da yaran. "But that's not all, bayan untata rayuwar yaran, suna azabtar da su azaba mai ra i, ta hanyar yin amfani da karfin sihirin su gurin sarrafa su, su yi amfani da su ta arfi da yaji..." "But that's still not the worst of it. They use these innocent children as sacrifices for their dark magic rituals, draining their blood and exploiting their suffering for their own gain. And, tragically, they have been known to target young girls during their period, subjecting them to... unspeakable atrocities..." kasa arasa maganar yayi saboda takaici da ba in ciki da ya mamaye zuciyar shi, tuni gumi ya fara tsartsafo mashi akan fuskar shi, a ido su ka yi da commender kasancewar suna fuskantar juna, tun daga kan yanayin yadda ya ura mashi ido ya fahimci maganar da yayi tayi matu ar girgiza shi, a agare yake da son jin karin bayani, hatta sojojin sun yi matu ar girgiza da jin maganar kurkukun addara. Mamakinsu wai har za'a samu yan adam da zasu iya shirya mugunta da zalunci a ashin asa na tsawon lokaci batare da asirin su ya tonu ba? "Owais, kai muke sauraro, Muna bukatar arin bayani daga gurin ka." General Noah ne ya yi maganar... Cikin sanyin murya ya amsa mashi da Okay, kafin ya kunna laptop din gabanshi ya fara operating inta nan take large screen in dake a jikin bangon dake fuskantar su ya kawo haske kamar tv nan take ya yi displying video in su Unaisah a Questioning room wato akin tambayoyi, lokacin da suke bada bayani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun addara komai da suka tattauna camera ta na e shi. Yayin da suka nutsu suna sauraron tattaunawar su, wata irin zufar bacin rai da tashin
Chapter 174 · 0% Book details