Sashe 84
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
zata rayu ba, inaji ina gani nabarta a kwamin wanka tana kuka tana kallona..." kuka ne Ya ci karfinta da sauri Aneelerh ta fara lallashinta "Ni damuwana wanene yake kokarin ganin ya rabani da dangina? Me na masa Aneelerh? Nasan bana jin magana tun a uruciyata inada jan fa a da masifa, mutane da dama na sanya su ciwon kai har da masuyi min mummunan fata amma wallahi ban ta6a zaton za'a samu wanda zaiyi min asiri, to waini me nayi masu haka??" idanunta jawur ta fa Dafa kafadarta Aneelerh tayi"in sha Allah duk wani mai nemanki da sharri kanshi zai koma, ubangiji Allah Ya tona asirin su" "Ameen Aneelerh nagode sosai da kulawarki agareni, ni wlh banyi zaton zaku kar6e ni hannu biyu idan na dawo ba, ko gida da zan dawo nayi fargaban ha uwa da su Daddy amma saina ga kowa Yana murnar gani na ba aramin da i naji ba, yanzu damuwana aya shine mijina da ata ina matu ar jin shakkarsu saboda nasan da wuya su kar6eni hannu biyu kamar yadda kukai min..." "Meyasa zaki ce haka? ay su sai sun fi kowa murnar ganinki" Girgiza kai tay"ba zaki gane ba Aneelerh, bayan tafiyata lokacin ina agidan zaki, kwatsam wata rana saiga sa on saki daga Taj hakan Ya tabbatarmin da yaji haushin abun da na masa" da mamaki Aneelerh tace"kina nufin bake kika nemi saki daga wurinsa ba?" aga mata kai tay alamar eh, shiru Aneelerh tayi jikinta Ya ara mutuwa lakwas saboda taj da kanshi Ya ta6a fa a mata Benazir ta tura masa text message tana neman ya saketa, to kenan wanene Ya shirya wannan tuggun?" Ta jafe ma kanta tambayar da bata da amsarta, o hannayenta Benazir tayi a cikin nata ta dam e su sosai cikin sanyin murya tace "Dan Allah Aneelerh ki taimaka min Inason yin magana da tajuddeen, naji kince baki da layin da Yake amfani da shi, tun da suna a tare da mijinki dan Allah ki kira Uzair in sai mu yi magana da shi..." Rass Aneelerh taji gabanta Ya fa i, tuni ta nemi nutsuwarta ta rasa, batasan taya zata shawo kan Benazir ba sam ta manta da jiya ta fa a mata hada mijinta suna a South Korea, "Kinyi shiru baki ce min komai" ta fa a idanunta acikin na Aneelerh, farat aya ta fahimci wani abu daga yanayin da ta nuna, Wani irin kwarjini Benazir tayi mata muryarta da inda inda ta shiga fa in "am..umm..bani da layin shima uzair...au wayarshi ta lalace zan ce....." bata are maganar ba ta katse ta da cewa "Kada kiyi min karya Aneelerh ba halinki bane, dan Allah ki fa amin gaskiya ni dama najima ina kokwanton maganar mami, daga baya sai da raina ya bani akwai wani abu da take boyemin don itama lokacin dana tambayeta lambar Taj tunda nasan bata rasata ba kamar da suka bayyana man cewa suke kula da yarinyata lokacin dana dawo amman sai ta nuna man basu da lambarshi ta inda yake, tun nan na fara shakkun maganar ta tunda ko don saboda yarinyar tawa ai ya kamata ace suna da lambar tashi da suke magana, kawai ki fa amin in da akwae wani abu nayi maki alkawarin bazan tada hankalina ba, boyemin bashi da amfani tunda duk min daren da ewa zanji ne kuma bazan ji da in sanar man da kuka yi ba...." Jinjina kai Aneelerh tayi tuni taji walla ta cika idanunta don har yanzu zuciyarta da ciwon abun, Numfashi taja kafin ta fara bata labarin abun da Ya faru na 6acewar su Tajudeen, Tsabar tashin hankali Yasa Benazir saukowa daga zaunan da take a gefen gadon ta dawo kan floor dirshan ta aura hannayenta biyu asaman kanta muryarta cike da tashin hankali take fa in "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN! INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN......" Misalta tashin hankalin da zuciyarta ta fuskanta ba abune mai sau i ba, Idanunta sun ka a jawur facial muscle dinta har kerma take gaba aya jikinta ya au wani irin mahaukacin zafi kamar mai fama da zazza6i sai kerma take, Dafa kafa arta Aneelerh tayi muryarta a raunace ta furta "Innallaha ma'assabirin Iya abun da zan iya furta maki kenan, abun da Ya faru Ya riga daya faru Benazir, illa iyaka mu cigaba dayi masu addu'a ubangiji Allah Ya bayyanar mana da su tunda har Yanzu babu labarin suna araye ko sun mutu, Cikin shesshekar kuka Benazir take fa in "nashiga uku Aneelerh! Meke faruwa da rayuwata ne? Da farko An rabani da dangina hakan bai isa ba sai da akayi silar da ata da mijina suka 6ace! Wai wanene ke bibiyar rayuwarmu ne? Uban me muka masa...." jin Yadda take aga Murya Yasa Aneelerh saurin toshe mata baki da tafin hannunta gudun kada su Mami su jiyota.... arshe ma sai ta rungumeta saboda ta samu relief in abunda ke damunta Allah ka ai Yasan tafarfasar da zuciyarta keyi mata kamar numfashinta zai auke bakomai take tunawa ba face fuskar Taj dana yarta Unaisah yanzu shikenan ta rasa su? Gunjin kuka taci gaba da yi, kwantar mata da hankali Aneelerh ta shiga yi, suna haka Mami ta shigo ganin halin da suke ciki yasa ta nufosu da sauri tana tambayar lafiya mike faruwa ne ta gan su haka da alamun tashin hankali, zama tayi a bakin gadon ta dafa kafa ar Benazir tana fa in "mike faruwa ne na gan ki cikin wannan halin??" Aneelerh ce dake walla ta fa i mata dalilin shigarta halin, yanayin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mami tace ma Aneelerh tunda bata sani ba ai da bata sanar mata ba, shiru Aneelerh tayi cikin kuka Benazir tace "Mami nice na matsa mata ta sanar man, 6oye mani baida amfani don koda yaushe ina sa ran ha uwa dasu ashe ba rabo, an raba ni da mijina da kuma ata, Mami suwaye wa annan azzaluman da suka tarwatsa kan iyalin mu, mi mukai masu ne don Allah" gaba aya ta gama karya masu da zukatansu itama Mami har idanunta sun ciko da wallan, rarrashinta ta shiga yi tana karfafa mata gwuiwa kan inda rabo sai suga sun bayyana tunda har yanzu ba'a da tabbacin ko sun mutu har ta bata misali da ita yadda ta 6ace 6at ba'asan ina take ba tsawon lokaci gashi yanzu Allah ya bayyanar masu da ita don haka ba abunda zasu yi sai suci gaba da yin Addu'a, a tare suka cigaba da rarrashinta har saida suka ga ta an samu nutsuwa Mami tace ta taso suje taci abinci dama shi ta shigo tayi mata magana, idanunta sunyi jawur ta girgiza mata kai kafin cikin disashshiyar murya tace bazata iya cin wani abu ba a yanzu, dole Mami ta yaleta Benazir in ta bu aci shiga toilet da sauri Aneelerh ta mi e tana nuna mata toilet in ta mi e jiki ba wari ta shiga, bayan shigarta Mami ta mi e cike da tausayinsu ta fita, wanko fuskarta tayi bayan ta fito akan gadon aneelerh ta kwanta kamar ba laka a jikin ta, tsananin tausayinta duk Ya kama Aneelerh tana ta kallonta, bayan wani lokaci ta mi e taje ta kawo mata abinci da juice don tasha tace mata bazata iya cin komai ba, lalla6ata tay dakyar ta samu tasha juice in, shiru sukai can Benazir din tace "Ina yaronki? Naga bangan shi ba? Ina abie?" "Bayanan sun tafi unguwa tare da Mahboob anin Zahra, su abie suma basa nan amma nasan zuwa anjima ka an zasu dawo gidan" "Allah Ya dawo da su lafiya" amsa mata tayi da Ameen daga haka bata ara magana ba har bacci Ya an dauke ta a akin. ____________________Chief Around 5 na marece Ya fito daga Gym room insa, daga shi sai short ba i a jikinsa, Ya ha a uban gumi zufa ta ko'ina take tsatstsafo masa, Hannunsa aya ru e da short towel da yake goge gumin jikinsa, Bathroom Ya shiga, within 15 mins Ya fito daga wanka ya nufi walk-in closet dinsa cikin kankanin lokaci Ya kimtsa cikin suit navy blue sunyi bala'en Yi mashi kyau da alama zai fita wani wuri ne, hadaddiyar agogon hannunsa sai salki take, kafafunsa na sanye da hadaddun leather shoe ta ko'ina kamshin turarensa Ya kara akin, Wayarsa ce ta fara ruri ya auko tare da duba sunan mai kiran sa, hidding number ce nan take Ya gane mutumin nan ne daya saba yi mashi kiran sirri, Picking call din Yayi tare da kara wayar a kunne, "Naji da i da ka fara yadda da maganata, Yanzu Ya rage naka Owais kai kokari wurin gano su wanene miyagun dake a family inka tunkafin lokaci Ya ure maka" "Sai yaushe ne zaka bayyana min kanka? Ina son sanin Wanene kai?And how did you know everything that's happening with my fam? Sautin dariyar mutumince ta cika masa kunnansa "sanin wanene ni bai da amfani, idan kuma ka damu da son sanin wanene to ka fara kawo arshen miyagun dake a cikin zuri'arku" runtse ido Chief Owais yai har cikin ranshi bai son jin Ya ambaci miyagu a family dinsa zuciyarsa karaya ta ke yi kalmar bata masa dadi, Rai a6ace yace "babu miyagu a family dina, ka kiyaye kalamanka," dariya mutumin yayi "shiyasa nake jin tausayin ka Owais saboda ka yarda da kowa na family inka, me zai faru a ranar da ka gane gaskiyar da nake kokarin ganar da kai" a fusace Ya daka masa tsawa baima tsaya ya arasa jin zancen mutumin ba Ya wurgar da wayar kan Gadonsa, Yana faman fitar da huci Ya furta "bazai ta6a yiwuwa ba, na yarda da family dina, babu bata gari a cikin su...." Yana a cikin wannan Halin Wayarsa ta sake Yin ringing, Ko kallonta baiyi ba a zaton shi mutuminne Ya ara Kiransa shiyasa bai kulata ba, Jiki amace Ya zauna kan couch gaba aya Ya rasa sukuninsa zuciyarsa sam bata masa dadi, Wayarsa sai faman ringing take da zarar kiran Ya katse wani Yake shigowa, Runtse idanunsa yayi bakomai Yake hangowa ba face fuskar Daddynsa data Uncles dinsa kai harma da Kakansa mutanan kirki masu Daraja a idon duniya, abune mawuyaci ya gasgata maganar mutumin in har ba gani yayi a zahirance ba, to wai wa akeso Ya