← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 65 OF 247

Sashe 65

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

amarairaice ta kalli faces din yan uwanta kafin ta sanya yatsun hannunta dake kerma ta dauki aramar wu a, har taj ya yunkura zai ru o hannunta don ya taimaka mata ganin hannun ta na kerma, tunawa da danish yasa shi fasawa don har yanzu bayanshi bai daina yi mashi zogi ba. A hankali ta yanko cake din tare da agowa tana kallon su idanunsu duk suna akanta, tama rasa wa zata fara bama cake din duk da akwai wanda zuciyarta ta aminta da cancantarsa, satar kallonsa tai nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, "Angel ki ba danish, shi Ya cancanta ki bamawa," muryoyinsu sajeed ne suka cika kunnuwanta. kau da ido tayi daga kan danish ta kalli daddynta, Lumshe mata idanunsa yai alamar ya amince mata. Murmushi ta an saki har dimples dinta suka lotsa, matsawa tayi kusa da danish, ta mi a masa cake din ya bu aramin bakinsa ta sanya masa, gaba daya suka soma tafa masu, Bayan ta ara cirar wani cake din ta mi a ma daddyn ta Yaci. daga bisa ni ta mi a ma Haris Wu ar, Ya kar6a Ya datsi cake din ya sanya wa deeja abaki, wani irin farin cikine Ya lullu6e su Bayan ta gama taune na bakinta, ya bata wukar don ta bashi, abunka game tabin hankali, maimakon ta kar6i wu ar sai ta sanya hannu ta 6allo ato ta duma masa abaki har cikin hancinsa ya shiga, gaba aya suka sanya dariya, cike da nishadi. Kar6ar wukar batool tai, ta ballo cake din ta ba mubeen Abaki Yaci, Kafin Ta sake gutsuro wani ta mi a ma Rubina itama taci, aya bayan aya duk sai da suka ciyar da junan su cake din. Tunawa da aunty umminsu dake ta kallon su, yasa batool ta sake kar6ar wukar daga hannun Sarah, ta yanko cake din taje gaban ummi ta mi a mata, murmushi tasaki tare da ru o hannun batool ta tura shi abaki tana taunarsa agowar da zatayi kwatsam suka ha a ido da sheikh iman dake ta satar kallon ta, duk sai taji jikinta yayi mugun yin sanyi, tuni taji wasu hawayen sun cika idanunta, muryarta na rawa tace da batool"ba ki ba sheikh imam cake din ba" tana fadin hakan tai saurin juyawa ta nufi hanyar komawa bedroom dinta, sam yakasa janye idanunsa daga kallon ta hatta su taj sai da suka lura da kallon ummi da yakeyi sai dai basu kawo komai aran su ba. Jiki asanyaye Batool ta ara yanka wani cake din taje gaban sheikh Imam Ta mi a mashi, sai da Ya fara aura tafin hannunsa akanta ya an shafa shi ya furta"Allah yayi maki albarka" kafin Ya bu e baki ta saka mashi cake din' Murmushi kowan nan su Yasaki gwanin ban sha'awa. Da zolaya big guy yace"yau an nuna min wariyar launin fata, Ni babu mai bani cake din"? da sauri sajeed yace zan baka, girgiza kai yayi"I'm sorry Ni mace nakeso ta bani ba jin sina ba" dariya suka sanya gaba dayan su. Harara boss yadan jefa masa cikin muryar ra a Yace"kai bana son iya shege fa, halan tazurancin naka ne Ya motsa" ar dariya yai har hakoransa suka bayyana. "Ni zan baka cake din" jemimah ce tayi maganar, da karfin hali fuskarta sharkaf da hawaye, gaba aya suka sanya dariya, matsawa big guy yai tare da kai hannu ya dauki Jemimah, kafin Ya bata wukar Ta yanka ta bashi abaki, shima ya karbi wukar ya 6allo cake din Ya sanya mata abaki. Sautin tafin su Ya cika falon, wunin ranar shagali sukayi babu kakkautawa yadda kasan gidan biki. _______________________________ Safa da marwa takeyi a tsakar dakin ta, fuskarta dauke da tsantsar farin ciki, gaba daya ta shagala da tunanin Yar ta Angel sam ta manta da zancen tafiyar su, zumu i Ya hana ta zauna jira take Aneelerh ta tura mata da hotunansu duk tabi ta kosa da son ganin fuskarta Jin arar shigowar sakonni ta whatsapp din da ta bu e ne, yasa tai saurin duba screen din wayar dake ruke a hannunta, wayyo Allah dadi, tsabar zumudin ta bu e sakon Aneelerh yatsun hannunta har kerma sukeyi, lokacin da ta aura idanunta akan hoton Unaisah afafuwanta kasa aukarta sukai, awani slow ta koma gefen gado ta zauna hannunta aya dafe da bakinta take kallon hotunan Unaisah, yayin da zuciyarta ke harbawa da karfi da karfi tun da take a duniyar nan bata ta6a jin son wani an adam fiye da yadda takeson arta, duk da basu taba haduwa ba amma taji wani irin mahaukacin son yarinyar na ara shigar zuciyarta. Hotunan da Aneeleeh ta turo mata na unaisah tun tana jaririyarta nanna e cikin farin towel, hada hotunan Birthday dinta lokacin ta cika shekara goma aduniya, sunyi kyau hotunan kamar lu'u lu'u Wani irin sanyine Ya ratsa zuciyar benazir, a kalla ta shafe mintuna tana kallon hotunanta, kafin ta bu e na baby junaid din Aneeleeh, Murmushi tasaki tana kallon kyakkyawan yaron kamar sabon fure ya kwanta mata aranta, Bakomaine Ya fa o mata aranta ba face Fatimar yaya shureim ita kadaice babu acikin su A hankali ta furta"Allah sarki Aisha ke kadai ce babu jinin ki araye, mun yi babban rashi, Allah yaji an fatima Allah Yasa mai ceto ce....." idanunta cike tab da kwalla tayi maganar. "Benazir zaman me kike yi"? Rass taji gabanta ya fadi jin muryar hajiya layla, a hanzarce ta dago tana duban kofar shigowa dakin, Hannunta ruke da trolley din kayanta, fuskarta babu fara'a sai faman huci take yi, Shigowa dr shureim yayi da sauri yana kokarin shawo kanta"mommy dan Allah ki yi hakuri ki fasa tafiyar nan, kinga daddy bai amince maki ba, Yakamata kibi umarninsa ko dan gujewa fushin ubangiji...." harara ta watsa mashi tana fadin"shureim zan 6ata maka rai wallahi, Idan kai bazaka bi ni ba to ka yale ni in kama gabana, har yaushe ne zan cigaba da zama ana raina min wayau agidan nan? nafa san me nake yi, ni ba shashasha bace..." mai da dubanta tayi ga benazir wadda tuni ta mi e tsaye damuwa ce tsantsa akan fuskarta. "Wuce mu tafi, Idan kema ba zaki bi ni ba, to ki zauna tare da su" ta fada rai a6ace. Cikin sanyin murya Benazir tace"mommy ki yi hakuri dan Allah, kinsan bazan i bi umarninki ba amma bazan iya tafiya ba...." baki asake Layla ke kallon ta. "Nima ba son zama gidan nakeyi ba, Aneeelerh ce ta kira ni awaya, kiran da muke ta jira, sai yau Allah Ya nufa, dan Allah mami kibarni in hadu da ita inyaso daga baya sai mu tafi" Girgiza kai hajiya layla tayi"kawai kizo mu tafi, in mun fita zamu fara biyawa gidan su Aneelerhn kafin mu tafi" da arfin hali tai maganar, ita kanta tana jin fargaban zuwa gidansu aneelerh saboda bata so Benazir ta gane karyar da tayi mata nacewa su taj sun bar kasar amma a halin yanzu idanunta sun makance burinta su bar gidan duk abun da zai faru ya faru. Gyada kai Dr shureim yayi"ki bita ku tafi, Allah Ya kiyaye hanya, Ni zan jira daddy" Tsoki layla taja, tare da juyawa ta nufi kofar fita daga dakin, da sauri benazir ta dauko mayafi, dr shureim ne ya janyo mata trolley din kayanta, lokacin da suka fito falon gidan, yayi dai dai da fitowar su Hajiya sarah da gudu zeenatu ta nufi benazir tana kuka ta ru e mayafinta. "Aunty benazir kada ki tafi kibarni, dan Allah kada ki tafi, Mami Dan Allah ku yi hakuri ku zauna, Idan wani abu mukai muku badaidai ba zamu gyara, Ni dai banso ku tafi" "zeenatu zonan"! Muryar Alhaji musace ta katse mata koke koken nata, jiki ba kwari ta saki mayafin benazir ta koma wurin shi ta tsaya, ru e hannunta yai acikin nashi, Hajiya sarah kamar an rufe mata baki takasa ta6uka komai sai kallon su da take yi, dakatawa sukai da yin tafiya jin muryar Alhaji ubaid "Wallahi idan kika sa kafa kika bar gidan nan batare da yawuna ba, to ki sani abakin auran ki"!! hankulansu Dr shureim atashe suke kallon shi har suna hada baki wurin furta daddy meyasa? Dariyar takaici layla tasaki tana tafa hannu tace"sai me donka sake ni? Ni dama ay najima da gajiya dakai tun lokacin da na gane kai bakomai bane face rakumi da akala, Ina amfanin zama da namiji solo6iyo irin ka"? Rai a6ace ta fa a tana kallon cikin idon shi, Kalamanta sun ona masa rai, da yar Ya iya hadiye yawu mai aci ba tare da ya iya furta komai ba. Dauke idonta tayi daga kanshi ta kalli Alhaji musa, dake atsaye ya har e hannuwansa kan kirjinsa fuskarsa babu fara'a Harara ta watsa mashi kafin tace "Hankalinka Ya kwanta Ka shiga tsakanina da mijina, In sha Allah zaka ga sakayyar hakan" wani kallon asan ido Ya watsa mata mai wuyar fassaruwa. "Shureim Benazir, kada ku bi ta idan har na isa daku, Kubarta ta tafi ita kadai tun da bata jin maganata" acewar Alhaji ubaid. Murmushin takaici layla tasaki, ba tare da ta ara furta kalma ba ta juya a fusace tabar falon "Ka bar su su tafi" Alhaji musa ne ya fada agadarance. Da sauri benazir taja trolley dinta tabi mommynta, shima shureim yabi bayanta A bakin motar shureim ta tsaya zuciyarta a kuntace, batai tsammanin zasu biyo bayanta ba Dr shureim na arasowa Ya bu e mata back seat din motar ta shiga ciki, sannan ya sanya masu trolley din kayan su a boot, daga bisani itama benazir ta shiga ciki. Bayan ya shiga ya zauna a driver's seat, yai ma motar key, zuciyarsa cike fal da damuwar abunda Ya faru, yaji takaicin yadda Alhaji musa ya nuna halin ko'in kula akan tafiyar mamin su, abun da Yafi bata masa rai furucin mahaifinsu yansu shikenan yana ji yana gani auran iyayensu zai rabu"? "Shureim! Ya akai naga ka dakata da yin driving din"? Cikin rauni na murya yace"mommy Kiyi hakuri mu koma, idan kika tafi ya kike so muyi da rayuwarmu? Ke kanki bazaki so abun da zai tarwatsa farin cikin mu ba...." Shiru tayi tana nazarin maganarshi, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi lakwas "Mommy, kina atare
Chapter 65 · 0% Book details