← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 43 OF 247

Sashe 43

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

na an wani lokaci kafin taja numfashi taci gaba cewa" aya daga cikin abun da unaisah tayi wanda har a bada bazai ta6a gogewa acikin zuciyata ba, shine musuluntar da yar uwar mu unaiza da tayi, unaisah bata bari unaizah ta mutu a matsayin arniya ba, sai da ta taimaka mata ta kar6i shahada duk don saboda ta tsira a lahira..." muryarta na rawa tayi maganar, kusan atare suka rushe da kuka tunawa da yar uwarsu unaizah, maganar batool ta fama masu raunin dake acikin zuciyoyin su. zu6ewa su ka yi gaba dayansu saman gwiwowinsu agaban tajuddeen, suna kuka yana kuka babu mai lallashin wani a cikin su, ummi da batasan kan zancen nasu ba tuni itama ta fara matsar walla cikin rauni na murya tace dan Allah ku fahimtar dani ku yi min bayani tun kafin zuciyata ta buga, saboda hankalina ya tashi na kwa aitu da son jin tarihin rayuwarku......." Lumshe ido chief owais yayi, zuciyarshi ta karaya, wankan suit ne ajikin shi, bai jima da dawowa daga Airport ba wurin rakiyar prime minister. A hankali Ya dubi Big guy dake a tsaye gefen sa, hawaye ya gani sun cika mashi idanunshi, Shi kanshi dauriya ce kawai, amma kalaman su sun ta6a ta6a zuciyarsa. Cikin sanyin murya ya furta"ka kira salsabeel a waya ka fa a masa inji ni ya shirya sauran yaran, su zo nan gida su sameni, inaso suga yan uwansu" cikin girmamawa big guy yace"okey, sir." ya fa a tare da zaro wayarshi ya danna ma salsabeel kira wayar na fara ringing, yayi picking, "barka da safiya yalla6ai" "Yawwa barka, Ina fata dai ban katse maka baccinka ba" muryarshi da yar dariya yace"ay bana yin baccin safe saboda khadeeja kasan halinta kamar mai fama da cutar yunwa, tun da safe take tashina, don in shiga kitchen in dafa mata indomie" "Allah sarki, ka cigaba da ha uri da ita, Yanzu dai gani tare da chief, yace yana son ganin ka da sauran yaran yanzun nan ku same mu agidansa" Muryar salsaleen da dan rudani yace"yallabai badai wani abune ya faru ba? Naji kace nazo da yara da sassafen nan" "Ba wani abu kazo kawai, " amsa mashi yayi da toh, kafin su ka yi sallama Ya maida wayar cikin aljihu... Angel dake atsugunne bakin kofar toilet din, jikinta ya gama yin sanyi tamkar wadda aka zarewa laka, duk abunda su batool ke fadi akan kunnanta tuni tayi shiru ta dakata da yin kukan, ita kanta bata ta6a tsammanin sun ru e kyautatawar da take yi masu ba acikin zuciyoyin su, shiyasa ake son bawa ya kasance yana aikata abun alkhairi arayuwarsa saboda duniya tayi alfahari dashi, al'umma su yi koyi dashi ko bayan ba ranshi, unaisah dai ta bada gudummuwa ta bangarori da dama harta ta bangaren addinin musulunci ta musuluntar kuma ta fadakar Allah ne ka ai zai iya biyan ta. Cikin shessher kuka suka soma yi mata magana, muryoyinsu duk sun disashe "Yar uwarmu rabin ranmu, amadadin abban mu, muna baki hakuri dan Allah ki taimaki daddynmu, Kiyi hakuri ki fito yana son ganinki, daddy ya gane kuskurenshi kuma ashirye yake daya baki hakurin laifin da yayi maki.... " magiya suka dinya yi mata duk don su samu ta bu e masu kofa "Unaisah kin manta irin kyautatawar da daddynmu yayi maki tun kina karamarki, lokacin da mommynki ta gudu tabar ki a cikin kwamin wanka, ya daukeki yaci gaba da baki kulawa duk da kasancewar bakyajin magana ahaka yaci gaba da rainonki saboda irin son da ya ke yi maki shi bai tafi yabar ki ba, unaisah da bakin ki ki bamu labarin nan ko kin manta ne......" gaba aya kowan nan su ya osa ta fito saboda ta rungumi daddynta. Ba zato ba tsammani, suka ga taj Ya dafe saitin zuciyarshi yana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Muryarshi da wani irin sauti na tashin hankali, gaba aya suka zabura da sauri suka rufe shi suna ambaton daddy meke damunka? Baka da lafiya ne...." Jin wannan maganar yasa unaisah yin saurin mi ewa, yatsun hannunta na kerma ta soma kiciniyar bu e kofar, a fujajen ta fado dakin, ganinta yasa suka bata hanya, ta fa a jikin tajuddeen ta ame shi tana kuka take fadin daddy dan Allah kayi hakuri nasan nice na bata maka rai, ka tashi ka ji daddyna abun alfahari na, la66anta na kerma takeyin maganar, hawayen fuskarta tuni sun wanke fuskarshi, sumbatar goshin shi tayi, tare da manna masa wani kiss din kan kuncinsa ...." sai da taj ya bari ta gama firgita, tukunna ya bu e idanunsa fuskarshi dauke da murmushi, fashe mashi tayi da kuka da sauri ya janyota jikinsa suka rungume juna tamkar zasu koma mutun aya tsabar yadda suka matse junan su lallashinta yaci gaba dayi yana fadin"am sorry my angel, ki yafe ni, nasan bankyauta maki ba, wlh kina araina, kamar yadda kike fadin kin yi kewata nima haka nayi kewarki, angel rashinki ba karamin gi6i yayi min ba rayuwata sai da nakusa zaucewa saboda haukan rashin ki a kusa da ni, Angel bana iya bacci batare da nayi mafarkin ki ba, duk dare na Allah sai na tashi nayi salla saboda inyi maki addu'a Allah ya kare min ke duk da bani da tabbacin kina araye ko kin mutu......" dakatawa yai da yin maganar, idanunsa acikin na Angel dinsa, sai da ya fara tattara nutsuwarsa kafin cikin sanyin murya ya fara basu labarin abun da Ya faru dashi bayan ya jefa Angel cikin ruwa. _______________________________ Abun da ya faru lokacin da wadannan migayun dattawan su ka yasta lighter bayan sun zazzaga mashi fetur a jikin shi, idan ba zaku manta ba, ba su kaiga jefa mashi lighter din ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna suka cinna wutar, sannan ba su tsaya sunga wutar ta kone sa ba, suka shiga cikin motocinsu tare da fusgarsu suka bar dajin a guje, bayan tafiyarsu hucin wutar Ya daki fatar jikinsa wani irin radadin azaba ne ya ziyarci sassan jikinsa, nan take ya farfa o daga suman da yayi ko da yaga wutar dake ci, cikin matsanancin tashin hankali ya yi wani irin kwakkwaran juyi da dukkan karfinsa gaba aya ya rubza cikin Kogon ruwan daya jefa Angel, tsulundun Ya rubza cikinsa ya nutse can kasan ruwan kuma nan take ya sake sumewa. Suna acikin ruwa aya da Unaisah sai dai akwai tazara tsakaninshi da unaisah, wanda silar hakan yasa har danejo ta ceto rayuwar unaisah ba tare da tasan cewa akwai mutun acikin ruwan ba saboda ruwa daya ja shi... A kalla taj ya kwashe tsawon kwana uku acikin ruwan ba tare da ya samu taimako ba. Ana haka cikin ikon Allah, Wasu fulanin daji dake kiwo daga can wata ruga dake a cikin dajin, su biyu matasa suka koro shanayensu zuwa wurin da ruwan nan yake, Anan suka ya a zango, to aya daga cikin su mai suna habu mayen ruwa ne duk in suka zo bakin ruwan sai ya shiga yin wanka, babu irin gargadin da an uwansa garbati baiyi mashi ba akan yadaina shiga ruwa saboda hatsarin dake gare shi amma yai kunnan uwar shegu da shi saboda taurin kansa da kafiyarshi, Abun ne yabi jikin shi tun suna kanana Yake shiga ruwa yin wanka har izuwa girmansa, shi kuma garbati mugun tsoron ruwane da shi, ko kusa da ruwa baison zuwa jikin shi kerma yakeyi saboda Labaran da yake ji daga wurin mutane dangane da mugayen halittun ruwa dake cinye mutun shiyasa yake jin shakkar kusan ta kanshi da ruwa, aranar da suka je bakin ruwan, habu na kokarin cire kayan shi don yashiga yayi wanka, garbati yayi saurin dam ar rigarsa suka soma kokawa a tsakaninsu, cikin harshen fulatanci suke magana garbati yace wlh bazaka shiga ruwan nan ba, ka manta da gargadin da baffa yayi mana akan shiga ruwa? Ko so kake ka mutu ne kafin lokacin ka yayi? Habu da ya gama hasala Ranshi a6ace yace"Aradun Allah garbati baka isa ka hanani shiga yin wanka ba, ko da kuwa sama da kasa zasu hade saina shiga, idan ma wani abu ya same ni, ni naja ma kaina kai dai naka kallone kawai" duk yadda garbati yaso ya hanashi amma yaki ji, a karshe sai yasa hannu ya hanka e garbati gefe daya ya kife kan ciyayi da sauri habu ya bi ta hanyar da ya ke shiga ruwan ta cikin sauki yabi duwatsun dake kewayen da ruwan ya tsunbula cikinsa Ya cigaba da yin wanka yana raira waka cikin harshen fulatanci. Mikewa garbati yayi zuciyarshi a 6ace yaci gaba da kula da shanayensu yana jiyo muryar habu dake acikin ruwa yana raira mashi wakar habaici har yana kiran shi da ragon namiji, zaifi dacewa ya koma aura zani maimakon wando, har ma ya dinga taya su Inno surfen Gero, ranshi ya 6ace jin wannan maganar, amma saboda hakurin dake gare shi sai ya share shi yaci gaba da kula da shanayensu Habu yana cikin yin nutso ya shige can kasan ruwan yana shawagi ba zato ba tsammani idanunsa suka sauka akan mutumin dake kwance kasan ruwa rai hannun Allah, kasancewar kasan ruwane idanunsa sunyi mashi biji biji sai ya dinga ganin kamar wata halittar ruwace me girman gaske, bakomaine ya fado mashi aranshi ba face gargadin da garbati keyi mashi akan ya daina shiga ruwa akwai mugayen halittun dake cinye naman mutun, nan fa hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta soma yi mashi dakan uku uku, Jiki na bari ya soma yin sama ya fiddo kanshi yana ihu na fitar hayyacin tamkar zai fasa makoshin sa, ko da garbati yajiyo ihun Habu abunka ga firgitacce bai tsaya tambayarshi menene ba, ya watsa aguje kamar karan farauta Ya nufi rigarsu.... Ya bar habu acikin ruwa Yana ta Zagba ihu tsabar rudu Ya hana ya fito daga ruwan gaba daya ya gama rikicewa. Da gudun gaske Fulanin Rigarsu suka nufo wurin ruwan wasu ko takalma babu a kafafuwansu, wasu kuwa hannayensu ruke da makamai saboda su ceto dan uwansu, bayan sun karaso gaban ruwa wasu dattijai daga cikin kakanninsu irin wadanda suka da e suna gwagwarmaya ne, basu da tsoro ko miskala zarratin, sun saba da duk wani abu daya shafi daji suna da kwarewa akansa
Chapter 43 · 0% Book details