← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 41 OF 247

Sashe 41

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 3 min read

dakyar dakyar take kallon fuskarshi ba tare da sanin shi ba, acikin zuciyarta ta dinga ambaton sunan shi daddyna daddyna dama kaine kake boye min fuskarka..." siraran hawayene suka wanke fuskarta, ganin yana kokarin juyowa yasa tai saurin lumshe idanunta, saukar hannun shi taji asaman kanta, A hankali Yake dan shafa mata shi, wata irin ni'ima taji ta saukar mata, jikin ta yayi sanyi ba kamar dazu da zazzabi Ya lullu6eta ba, bakomai take tunawa ba face lokacin da ya jefata cikin ruwa... Taj sam baisan cewa babu face mask a fuskarshi ba, gashi har unaisah taga fuskarshi, don ma babu kwarin jiki ai da ta tuhumesa nakin bayyanar mata da kanshi da baiyi ba, dama tuntuni ranta yana bata cewar daddynta ne duk da bata ta6a ganinsa ba, amma kulawar dayake bata fiye da ta sauran yan uwanta da yadda yake janta a jikin shi da kuma muryarshi su suka kara sanya ta hasashen ko shine. Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, tuni Kowa ya koma masaukinsa bayan da suka hallara a gidan prime minister inda suka karasa shagalin nasu acan, a 6angaren chief owais tun bayan da suka shiga Part din Nazli, ba tare da sanin shi ba, ta kashe mashi wayar shi don kada a kira shi, bayan haka ta hada baki da daya daga cikin hadiman gidan ta sanya mashi maganin bacci a coffee, duk don kada ya tafi yabarta, Sai wuraren karfe sha daya na dare tukunna chief Ya farka, a lokacin nazli har tafara bacci, bai bi ta kanta ba, da sauri ya fito daga part din ta ya sauko down, Kafin Ya kunna wayar shi, Layin prime minister Ya fara dannama kira don Yaji idan Yasa an mayar da danish gidansa. Bayan yai picking Hateem Ya fada masa suna atare da shi a bedroom dinsa, bai tsaya bata lokaci ba Ya nufi part din prime minister, dakyar ya raba shi da danish, kamar karsu rabu, na rana daya kawai sun shaku da juna har kyautar zobe ya ba shi mai tsadar gaske saboda ya dinga tunawa dashi, kuma yayi mashi alkawarin kullum xai dinga kiransa suna gaisawa, bayan chief Ya tafi da shi har kwalla saida Ya zubda daboda kewar rabuwa da danish....... Asubar Fari, Motoci suka dinga tururuwa wurin fita daga Estate din,da wata irin jiniya mai kuwar gaske tamkar zasu tashi sama, kaitsaye suka nufi shantalelen titin da zai sada su da Airport, gaba daya family din obinna ne dashi kanshi obinnan suka yi masu prime minister rakiya, Kamar karsu rabu da juna, musamman mahaifinsa da yan uwansa, duk irin juriyarsu saida suka share kwallar rabuwa da shi, Hajiya saratu tasha kuka kamar karamar Yarinya, shi kanshi hateem din saida Ya zubda kwallar rabuwa da yan uwanshi, Ji yake kamar idan ya tafi ba lallai Ya kara dawowa ba, hakika kowa yayi jimamin tafiyar prime minister da Iyalansa, ko bayan da suka baro Airport din suna akan hanyar komawa estate nasu lokacin da suka jiyo karar jirgin su Haka suka dinga leken jirgin ta windows din motocinsu, har Sai da ya bace ma ganinsu tukunna suka hakura kowa Ya sanyawa zuciyarsa salama, kusan duk aranar Su his excellency deeen suka bar abuja, harta su Justice kowa Ya koma inda Yake da zama wasu Nan cikin Nigeria wasu kasar suka bari, Zaki ne kadai bai tafi ba, yanzu estate din Ya rairaye ma zauna cikinsa ne kadai suka rage. *Daga Al alamin Boss Bature *Littafin kurkukun addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 16 Complete Novels Elite Admin June 06, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~ BOSSLADIESWRITERS
Chapter 41 · 0% Book details