Sashe 51
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
Ko dai aljanune suka shige ki? Nifa ina kokwanto bana so saina shagala ki canza min ainihin kala dinki" dariya tayi cike da nishadi tace"ka daina kokwanto akaina, ni ce dai hajiya saratun daka sani, matarka uwar ya'yanka" Murmushi pravin yai cike da jin shaukinta "Ka yi breakfast ko insa a kawo mana mu yi a daki nima banci komai ba" "In ban da abunki ay kinsan bana iya cin abinci idan ba atare dake ba, don ma ke dince wani lokaci baki jira na" "I'm sorry Yanzu bari na kira akawo mana a daki, me kake son ci"? Yana faman washe baki yace "Duk abin da zaki ci, zabinki ay shine nawa" Shu'umin murmushin gefen fuska hajiya saratu tasaki tare dakai hannu ta dauki waya ta kira layin kitchen ta isar da sakon akawo masu abinci, bayan abla ta kawo masu atare suka zauna suna ci, kamar sabbin ma'aurata abaki ta fara bashi har sai da suka cinye kafin ta soma jan hankalin shi. Gaba aya nema take ta zautar dashi da salonta, kasa jurewa yayi da sauri ya ara tighting nata a jikinsa. _________________________________ Bayan shigar chief bedroom dinsa a zafafe Ya fa a Bathroom dinsa don ya watsa ruwa ko ya samu zuciyarsa ta lafa daga radadin da ta ke yi masa. ganin ya shiga toilet yasa big guy sauke ajiyar zuciya, yayi tunanin zaiyi yadda ya saba ne idan ransa ya 6aci da wuya in bai yi ma kan shi illa ba, wani lokacin mirror yake kaima naushi ya tarwatsa shi har sai hannun shi ya faffashe saboda tsabar zuciyar dake gare shi. Kafin fitowarshi da sauri big guy ya fita na tsawon mintuna ya dawo hannun shi ru e da wooden tray mai dauke da breakfast din chief. Yayi mamakin ganin shi kwance kan gado, jikin shi sanye da bathrobe ya aura hannunsa aya kan lallausar sumar kanshi, ya lumshe wadannan kyawawan idanuwan nashi, bakomai yake tunawa ba acikin zuciyarsa face tarihin rayuwar prisoners, labarin yai matu ar ta6a zuciyar shi. "Allah Ya huci zuciyarka Yalla6ai, ga breakfast dinka, nasan kana jin yunwa" cikin girmamawa yayi maganar Tamkar bazai tanka mashi ba, sai da ya dauki lokaci kafin Ya furta"ka koma da abincin bana jin zan iya ci" Cikin sanyin murya big guy yace"ka yi hakuri Sir, kasan ni mai biyayya ne agare ka, bana yi maka jayayya amma yau bazan iya bin umarnin ka ba, saboda na damu dakai, abun da ke damunka nima shike damuna..." ya fada yana cigaba da kallonsa. "Sir, in cin abinci bashi bane mafita, kana bu atar kwanciyar hankali da nutsuwa, wanda hakan bazai samu ba sai ka jajirce wurin ganin ka kauda damuwarka, sannan yanzu ne ya kamata mu dage damtse mu yi aiki tu uru don ganin mun gano su wanene azzaluman mutanan da suke aikata 6arna a kasarmu" an kalamai Big guy ya cigaba da zayyano masa yana kara karfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, A hankali Ya fara jin saukin radadin da zuciyarsa ke yi mashi. "Sir, har yanzu kana akan bakanka na bazaka ci abincin ba"? Ya fa a yana duban cute face din Ogan nasa Slowly ya an motsa tausasan pink lips dinsa in a low voice ya furta"zan kokarta" gya a kai yai "Zan tafi yalla6ai, Ka huta lafiya" ya fada tare da sara mashi kafin Ya juya har ya kusa ficewa daga dakin muryar chief ta ratsa kunnansa"nagoda da kulawarka agare ni" Murmushi big guy yai"kada ka damu yalla6ai" Har zai fuce ya kuma dakatar da shi"please ka duba dakin Yaron nan, kaga Awani hali Yake a ciki, Idan ya farka a tabbatar Yayi breakfast dinsa, idan ya gama ka tambaye shi me yake bukata in ya fada maka ay gaggawar yi mashi, zuwa anjima sheikh Imam zai zo duba shi" "Okey, Sir" Ya fada tare da bude door room din Ya fito waje, dakatawa yayi da tafiya yana tunanin tawace hanya zai faranta ran chief? Don ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa aranshi, tunawa da Unaisah yasa shi saurin zaro wayarsa ya danna ma boss kira, tana fara ringing yai picking Call din Da zolaya yace"masu a, halan Har yanzu kana nan ma ale da ita" Sautin muryar boss da alamun dariya yace"To an sa ido, ka fara tsokanar taka ko"? Dariya Big guy yayi" inatayaka murna abokina" "Nagode sosai mutumina, Ina chief ne ina fata yana lafiya" "Ba lafiya, Har yanzu akwai damuwa aranshi, Kuma kasan halinshi mutunne mai zuciya, yanzu haka ina a kofar dakinsa, na kai masa abinci yace min bazai iya ci ba" Muryar bos da jimami yace"amma banji dadi ba, pls ka yi kokarin kwantar masa da hankali kafin inzo" da sauri big guy yace"anya zan iya? Ko dai zaka turo unaisah ko da godiyane tayi mashi, watakil hakan Ya kwantar masa da hankalinsa" "Nima nayi tunanin hakan, yanzu zan turo ta in sha Allah" murmushi big guy yai kafin yai mashi sallama a hanzarce Ya nufi bedroom diny Danish. GARKUWA A kishingi e Yake kan gadon shi, Ya hakimce kamar wani basarake, wasu hadaddun sleeping dress ne a jikin sa launin red colour sunyi bala'en yi mashi kyau, hannunsa aya rungume da pillow, lallausar sumar kanshi ta lullu6e gefen fuskarshi, yayin da kyawawan fararen idanunsa ke akan hadadden ceilling din dakin, tun da Ya farka daga bacci bai ta6uka komai ba, gaba aya ya shagala da tunanin Hateem, wani irin kewarsa yake ji, mutumin ya kwanta masa aransa saboda yadda ya tarairayesa ya bashi kulawa kamar wani nashi, bai ta6a tsammanin zaiji tsantsar kaunarsa ba, sai gashi zuciyarsa takasa samun sukuni saboda tunaninsa, da zarar ya lumshe idanunsa fuskar Hateem yake gani dauke da murmushi......" Yana son ya sake sanya shi a idanunsa, kwata kwata bai fahimci cewa prime minister kasar ya bari ba. Har Yanzu kamshin turaren daddy hateem bai bar jikin shi ba, saboda rungumarsa da yadinga yi jiya kamar zai maida shi jikin shi, fragrance din Yana da karfi sosai shiyasa ya kama jikin sa. Kalaman hateem ne suka fara dawo mashi _zan tafi da kewarka, dan Allah kada ka manta dani, inaso ka auke ni tamkar mahaifinka, aduk lokacin da wani abu ke damunka ka sanar da chief zai fada min, zamu dinga yin waya akai akai, daga yanzu inaso ka dinga kirana da sunan daddynka_ A hankali ya dago da yatsan hannunsa yana kallon zoben da ya sanya mashi ayatsa mai kyan gaske, wannan ne karo na farko daya fara sanya zobe, Daura yatsan yai kan kananun la66ansa Ya sumbace shi a hankali yanayin fuskarshi kamar zaiyi murmushi. Knocking din kofar dakin da akaine Ya sa shi daura idonsa kan kofar, bakomai Ya fado masa arani ba face Angel dinsa, yasan ita ka aice zata Iya zuwa duba shi awanan lokacin, Idan ba ita ba sai kuma yan uwansa, saukowa yai daga kan gadon bayan ya jefar da pillow hannunsa, da sauri Ya nufi kofar don Ya tarbe ta, saboda yayi kewarta jiya, idanunsa sunyi maraicin ganin ta,, shi kanshi baiyi tsammanin zai Iya mintuna batare da ita a gafen sa ba, sai gashi jiya daddy hateem Ya sace zuciyarsa. Ko da ofar ta bude yai arba da big guy tuni yanayin fuskarshi Ya canza, shi da ya taso da zumudinsa don Ya nuna ma Angel dinsa kyautar zoben da mutumin nan ya bashi, sannan Ya bata labarin abunda Ya faru atsakanin su ashe ba ita bace. "Barka da safiya danish" big guy ya fada da fara'a akan fuskarsa, ko kallo danish bai mashi ba, Hankalin shi na akan bayan shi, burin shi Yaga Angel don har yanzu bai fidda rai da ganin ta ba Da mamaki big guy ya waiga baya don yaga me yake kallo sai dai baiga komai ba. "Ina fata ka tashi lafiya" ya fada aranshi yana mai mamakin Girman Jikin Yaron ga tsawo tubarkalla uwa uba ga kyau kamar shi ya zana kan shi. "Magana na ke yi maka ka yi shiru ba ka ce komai ba, ko har yanzu ba ka jin da in jikin naka ne"? cikin sanyin murya ya furta"My Angel? Tana Ina"? Dafa kafadarsa big guy yai"kwantar da hankalinka tana nan cikin koshin lafiya, nasan zata zo dubaka..." kafin Ya kare maganar danish Yace"Ina son ganinta, " ya fada yana kokarin bi ta gefen shi Ya wuce, A hanzarce big guy yai saurin Shan gabanshi, gudun Kada Ya ruguza masa plan dinsa na zuwan angel part din chief. Wani kallo da danish Ya watsa mashi sai da ya an ji fargabansa, Karfin Hali Yai wurin furta"Ka yi hakuri bawai ina son dakatar dakai bane, daga gani yanzu ka farka daga bacci ko wanka ba ka yi ba, a haka zakaje wurinta? Itama bazata ji dadin ganin ba, kaje kayi wanka, kafin ka fito zan sa unaisah ta kawo maka breakfast dinka har daki" cikin sigar lallashi yakeyi mashi magana, badan Ya yarda da kalaman sa ba, ya amince mashi, juyawa yayi tamkar wanda ya rasa kuzarinsa, harta bugun zuciyarshi ya canza ji yake kamar wani abu na faruwa ko yana shirin faruwa Bayan ya shiga toilet Ya maida kofa ya rufa, ajiyar zuciya big guy ya sauke aranshi ya ayyana wai Allah daga ganin yaron nan zaiyi kafiya, dole saina mike tsaye idan ba haka ba zai iya zame min matsala. Ya fada tare da juyawa ya fuce daga dakin, Ya nufi sashen kitchen din su don Ya hada masa breakfast dinsa. UNAISAH ANGEL Bata jima da fitowa daga bathroom ba, sai rawar kai takeyi saboda daddynta Ya fada mata zancen zuwa dakin chief don tayi mashi godiya bisa ga irin kyautatawar da yayi mashi, ruwan ido Ya hana ta canki kayan da za ta sanya, tayi tsaye gaban faskeken closet dinsu, sai faman bin jerin kayan take yi da kallo, fuskarta dauke da murmushi tarasa gane meyasa take jin wani irin nishadi da annushuwa kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna. alla ta shafe mintuna kafin ta fito sanye cikin wasu riga da wando launin pearl pink masu kyan gaske, tsayawa zayyana kyawunta acikin kayan 6ata baki ne, abun sai wanda ya gani. Takalma ta auko masu tsini launin kayan, ta zura su a kafarta, bayan ta dauko mayafi ta tsaya gaban mirror ta ta soma