← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 232 OF 247

Sashe 232

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya auka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh. Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sau i a cikin lamuransa ya kuma ara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba. After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba. Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin an uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate. Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, aya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya arasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa okin ganinsa yake yi. Da yar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki ya i rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya bu e baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba. Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun araso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da arasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya i rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ru e shi ya yi a akinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba aramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, azu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya aga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin oshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training. Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya ha ura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa. ~________________________________ The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering *Daga Al alamin Boss Bature *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ~___________________________________~ fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa bu e baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"? A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata. Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta. Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci.. "Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya.. Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...." Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta" Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan. Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba. Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi. Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya auke afa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi. Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido. Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko aya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su. Lokacin da Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba. Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba. Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata. Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai. badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh. Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta fa a ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su. Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya yale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta. a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta
Chapter 232 · 0% Book details