Sashe 212
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
sai in shirya mu tafi" "Kin fada mata ne"? Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta. Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin, Ya fita don yaje ya shirya. Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka. *DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE *Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Health College Home Kurkukun Kaddara Kurkukun addara Takun arshe page 61 Complete by Boss Bature Novels Elite Admin September 29, 2024 Sponsored Link Takun arshe Zaune yake a mazaunin driver na motarsa, ita ka ai ya ke jira su tafi, har ya fara gajiya da jiran ta, wayarsa ya zaro daga front pocket din rigarsa ya danna mata Call. "Idan kika ara minti aya baki fito ba zan koma ciki ne." Yana fada yayi rejecting call in, jingina kanshi jikin headrest ya yi tare da lumshe idanun shi. Sam bai ji tahowarta ba, sai dai ya ji motsin bu e cardoor din, bu e idanunsa yai tare da kallon ta baki a bu e ganin yadda ta ca6a ado kamar wadda zata je gidan surukanta, Wani hadadden Code lace ta saka orange riga da skirt sun an kama jikinta, mayafin kayan a kafa a ta daura shi, ga wani hadadden daurin dan kwali da ta yi, ba ar sumar kanta ta sauko har mid back dinta, fuskarta ta sha make up....,sunkuyar da kai asa ta yi ganin kallon da Dr Shureim in ke yi mata. "Benazir, wa ki kai ma kwalliyar nan? sai ka ce wadda zata je bikon mijinta?" Tuntsirewa ta yi da dariya, ta yi mamakin jin ya canki abunda ta shirya, don wannan kwalliyar da ta yi saboda Taj ta yi ta, yau ta aura amarar janyo hankalin shi gare ta. "Zai iya yiwuwa." ta fa a tana sakin murmushi, ta6e baki ya yi tare da an girgiza kan shi ba tare da ya kawo komai a ransa ba, Kafin ya yi wa motar key a hankali ya yi reverse, a tsanake Ya ke yin driving in su... "Zeenatu ta ganki da zaki fito daga gidan?" Ya tambaya yayin da yake juya sitiyari. "Eh, amma bata nuna zata bini ba, naji tace zata bi Aunty Sarah Office, may be shiyasa bata damu da ta biyo mu ba." Tafiyar mintuna alilan Suka araso layin su Aneelerh, Bayan Baba mai Gadi Ya bu e masu gate Dr Shureim ya shigar da motar ciki, a parking space ya dakata. "Mu shiga ciki" Girgiza kai ya yi, "ki fara shiga za n shigo daga baya" amsa mashi tayi da toh, Fitowa ta yi ta nufi cikin gidan, bakinta auke da sallama ta shiga... "Muryar wa nake ji kamar Benazir?" Murmushi ta saki tare da sauke idanunta akan Mami da Ummi dake zaune a falo suna kallo a tv, gaba aya suka ago suna kallonta bayan sun amsa sallamar da ta yi... "Wlh ni ce Mami, na yi maku zuwan bazata ban kira na fa a ba" ta fada tare da karasawa ta dan du a gaban sofa in da suke a zaune ta gaishe da su. "Ina wuninku, fatan na same ku lafiya" A tare suka ha a baki "lafiya lou, ya mutanan gidan naku?" "Suna nan lafiya, Sun ce agaishe masu da ku." "Ina Zeenatu da Shureim namu"? A cewar Mami, "Yaya Shureim shi ya kawo ni, yana a waje, shi ya ce in fara shugowa zai biyo ni, mun baro Zeenatu a gida za su je office tare da Mommynta." Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi.. Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta aura aure da zaman aki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta," "Bata da lafiyane?" Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..." "Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta fa a tare da mi ewa ta nufi dakin Aneelerh.. A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a arshe ta yanke shawarar shiga ciki. Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta urawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji? Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta mi e zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta aya dafe da saitin zuciyarta. Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta. "Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba. Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta aro murmushi kan fuskarta.. "Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh. Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?" Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana are mata kallo.. A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..." Kaitsaye Benazir ta ce, " arya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne." Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta fa a min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...." Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ru o hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka urawa juna ido.. A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba aramin aga hankalin Benazir ya yi ba. "Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A agare Benazir ta jinjina mata kai. Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta. tunkan ta arasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata are sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su. Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi. Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka asa kasa. A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi. Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?" "Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo." Jinjina kai Benazir ta shiga yi. "Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu watarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...." bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina aga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah ka ai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada." Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa,