← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 72 OF 247

Sashe 72

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

saboda son ha uwa da ita, ya aga tafiyarsa canada. Yayi zurfi a zancen zucin nasa muryar turai ta ratsa kunnansa "First born barka da hutawa" ta fa a tare da daura masa mug din coffee kan table, murmushi ya sakar mata, yana aya daga cikin abun da yake burge shi da mommyn nasu in har zata ganshi zaune yana aiki akan laptop sai ta kawo mashi coffee . "Mom har yanzu baki yi bacci ba"? ya fa a yana kallon ta. "Tayaya zan iya runtsawa Jazz bai dawo ba, daddynku bai dawo ba shima, su nake jira su dawo sai in kwanta" tayi maganar tare da aura gwiwowin hannunta bisa ga hand sofa din da zaki yake zaune idanunta akan fuskarsa "Ko akwai wani abu dake damun ka ne"? Ta fada cikin kulawa "Babu komai" ya bata amsa atakaice tare da kai hannu ya dauki mug din Ya soma kurbar coffee "My son, tayaya zaka 6oye min damuwarka, bayan ni mahaifiyarka ce, ta ido kadai ina gane damuwarka, tun lokacin da ka shigo asar nan na lura da damuwa aranka" Sauke mug din yai kan table kafin ya dubi hajiya turai"nagode da kulawarki agare ni, amma ki kwantar da hankalin ki ba abun da ke damuna" a kai tay"haka nakeson ji" ta fa a ne ba dan ta yadda da maganarsa ba tasan baya son taji ne "Bari na shiga ciki, ka kula min da kanka" amsa mata yai da toh Bayan tafiyarta ajiyar zuciya ya sauke, bawai baya son fada mata bane yafi son ya fara jin halin da take a ciki in har ta isa gida lafiya, kuma iyayen ta sun kar6eta ba abun da zai hana shi sanar da nashi iyayen labarin ta. arfe goma da rabi, jazz da sir mubarak suka dawo gidan lokacin da suka shigo falon tuni Zaki Ya koma room dinsa ba su taras da shi ba, Hajiya turai na kwance kan gado tajiyo sautin sallamar sa, jikinta har rawa yakeyin wurin saukowa daga kan gadon da sauri ta nufe shi yana atsaye cikin shiga ta kakinsa "Sannu da dawowa, tun dazu nake ta jiranka nayi kewarka yau kayi dare " cikin nuna kulawa tayi maganar tare da ruko hannunsa suka shiga dakin "I'm sorry bansanar da ke zan kai dare ba, wani aiki ne mai muhimman ci Ya ru e ni" ya fa a Yana kallon cikin idonta, "Ba nace ki daina jirana ba? daga kinga nayi dare to ki kwanta kiyi bacci" e masa kafa a tayi"kai ma kasan bazan iya jurewa ba...." murmushi ya an saki"kinsan me na tuna"? Girgiza mashi kai tay alamar a'a" annan twins din na wurin Owais, ko da yake yace min ba twins bane, aya ta girmi aya" da mamaki hajiya turai tace"ikon Allah, amma nayi mamakin jin hakan komai nasu fa iri aya kamanninsu sun 6ace" "Zai iya yiwuwa yan gida ayane" jinjina kai tay alamar eh "Yaran sun kwanta min araina, kinsan ni da son a mata, duk family dinmu ni kadai ne nake da ya'ya maza ina alfahari da hakan amma inason ya'ya mata, ga hateem nan shi mazan yake so Allah bai bashi ba" shiru mom turai tayi kamar ta dan shiga damuwa, sam bai lura da halin da ta shiga ba, ya nufi toilet Ya shige jin arar rufe kofar shi Yasa jiki asanyaye ta koma gefen gadonsu ta zauna idanunta sun ciko tab da kwalla.. Ceilling ta urawa ido tana tunano wani abu da ya ta6a faruwa acan lokacin baya shakeru da suka gabata, ta ta6a haihuwa ya'yan suna mutuwa wanda silar hakan Yaja har sir mubarak Ya hanata haihuwar gaba aya gudun kada itama tarasa ranta kamar yadda ya'yan da take haihuwa suke rasa ransu da zarar sun dira a duniya, Allah kadai yasan halin da ta shiga awannan lokacin saboda ta kwallafa rai akan son taga ta haihu da sir mubarak sai dai Allah bai bata ba shiyasa har su hajiya saratu suke yimata gorin sai dai taci ta kasayar Yunkurawa tayi jiki ba kwari ta mike ta futo daga akin nasu ta nufi bedroom din jazz sai da ta matse kwallar da ta taru a idanunta kafin tayi mashi sallama shiru ba'a amsa mata ba, har ta fara tunanin ko yayi bacci ne, shigarta ke da wuya kwatsam taci karo da wayarsa dake yashe kan floor ga dukkan alamu wurgo da ita yayi, hatta lap coat dinsa anan ya jefar da ita, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, a razane ta kalli gadonsa a zaune ta same shi tsakiyar mattress, Ya kifa kansa bisa gwiwowin sa, lokaci aya ta rasa sukuninta da sauri ta nufi kayan nashi ta kwashe su ta je ta ajiye masa kafin ta dauko wayar ta nufin gadon nashi ta hau sama ta zauna tana fuskantar shi "Jazz meke faruwa dakai ne"? ta fada fuskanta dauke da matsananciyar damuwa Shiru babu alamun zai tanka mata "Nasan kana ji na jazz, ka ago ka kalle ni sannan ka fadamin meke damunka" A hankali Ya ago da fuskarsa wadda ta ji e sharkaf da hawaye idanunsa sun ka a jawur, wani irin bugu taji zuciyarta tai muryarta na rawa ta furta"jazz kuka kake? Meke damunka ne? Ko bakada lafiya ne? Aru e ta fada tana shafa fuskarsa "Jazz dan Allah ka fadamin ko hankalina Ya kwanta" da yar Ya iya motsa la66ansa Ya furta sunan faryat, lokacin aya annurin fuskar hajiya turai Ya auke uff, saboda ta fahimci silar shigarshi halin da yake aciki, batasan ya zatai da jazz ba, tayi fama da shi akan ya rabu da faryat amma ya iya saboda tasan bazata ta6a auran shi ba, hasalima ma yarinyar bata kwanta mata aranta ba, saboda fitsararta da rashin kunyarta.. "Jazz yaushe ne zaka daina yaudarar kanka akan yarinyar nan? sau nawa ina maka gargadi akan ka fita sabgarta? Na fada maka ba sonka takeyi ba yakamata ka hakura ka nemi wata ay ba ita kadai bace mace a duniya....." kafin ta are maganar ya tarin numfashin ta da cewa"bazan iyaba mommy, Allah ne ya jarabce ni da sonta, wallahi nayi kokarin cireta araina amma na kasa ki tayani da addu'a Allah ya yaye min sonta in ba haka ba zatai silar da zan rasa raina..." har saida gaban turai Ya fadi jin abun da yace, ta fahimci mahaukacin son da yakema faryat ba lallai Ya fahimce ta ba "Me tayi maka ne"? labari Ya fara bata na abun da Ya faru tsakaninsu lokacin da ya je wurinta bai 6oye mata komai ba, har nemansa da tayi don ya bata hadin kai, "Mom kullum na kirata sai ta ci mutuncina, tace wai ni ba namiji bane tunda bazan iya biya mata bukatarta ba, sannan bazata ta6a auran mara asali dan tsohuwar mai aikin gidan su ba...." ya fa a idanunsa cike tab da kwalla Ita kanta hajiya turai hawayen ne ke sintiri kan kuncinta, ta tsani taji ana yi mashi gorin asali kamar kanshi farau, ta rasa gane meke damun wasu mutanan sun manta cewa bawa bashi ke daurawa kansa ba? Allah ne Yake kaddara masa rayuwarsa? "Jazz ta yi kuskure A kalamanta, wallahi sai tayi danasani, saboda ka fi karfinta nesa ba kusa ba, kuma kaine cikakken mai asali tunda kana jin tsoron Allah kuma ka tsare mutuncinka, ni in banda kaddarar so ina kai ina Faryat"? ta fa a ranta amatu ar 6ace "Tafi ni komai tun da tana da asali" "Kaima kana da asali jazz" da sauri Ya kalle ta "Mom bangane me kike nufi ba, ke da kanki kika fada min baki da kowa a danginki mahaifina Ya rasu" girgiza kai tayi"na fada maka hakanne saboda ka fidda rai da kowa nawa, bana son maganar jazz ka cigaba da hakuri in sha Allah komai ya kusa zuwa karshe" tun da tafara magana jazz Yake kallonta har yau ya rasa gane dalilin dayasa bata son tayi maganar abun da Ya shafi danginsa, shi dama yasan dole tana da family dinta akwai dai wani abin da take 6oye masa, duk da yana neman arin bayani daga gareta sai dai ya hakura yabarwa zuciyarsa zai cigaba da hakuri kamar yadda ta ce har zuwa lokacin da zata sanar da shi komai.... Shiru sukayi na wani lokaci babu mai magana a cikin su, "Ina ibad"? ya tambaya yana kallon ta "Tun bayan sallar Isha' Yai bacci, ya yi jiran dawowarka har fadamin yai ya kira layinka bakai picking ba" murmushi yayi"Allah sarki an uwana, dama nasan dole ya neme ni, na sanya wayar a silent ne saboda aiki da nakeyi" "Bari na kawo maka dinner dinka nasan kana jin yunwa, but pls ka shiga toilet ka wanke fuskarka bana son ganin hawayen nan" ta fada tana nuna face dinsa da yatsa amsa mata yai da toh da sauri ya sauko daga kan gadon Ya nufi toilet. Tana ta bin bayansa da kallo har ya shige kafin Ta mike ta fito daga dakin Kitchen ta shiga ta shirya masu abinci ta fara kaima jazz a room dinsa kafin ta dauki na sir mubarak ta nufi dakin su Lokacin da ta shiga a tsaye ta same shi hannun shi ru e da wayarshi Yana daddanata har ya sanya kayan baccinsa "Ina kika je ne" ya fada ba tare daya kalle ta ba "Na shiga kitchen shirya maku abinci ne," ta fada tare da ajiye masa tray din bisa table, murmushin gefen fuska ya dan saki batare data ankara ba, abun da bata sani ba tun time da ta shiga dakin jazz Ya fito Yabi bayanta gaba daya ya ji maganganun da su ka tattauna har recording voices dinsu yayi a wayarsa, yayi mamaki abun da yaji suna tattaunawa, maganganun sun tsaya masa aransa, wani lokaci turai tana da zurfin ciki, in har ba la6e yayi mata ba ita da jazz bayajin damuwarsu sai in tura takai bango tukunna take sanar da shi. _______________________________ Aneelerh har tayi shirin kwanciya bacci, sautin ringing din wayarta ya dakatar da ita, A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ganin sunan surukar arzi i yasa tayi saurin picking call din idanunta na akan baby junaid dake kwance kan mattress Yana sharar baccin sa Cikin girmama suka gaisa da junansu "Aneelerh kwana biyu? Ya ki ke Ya
Chapter 72 · 0% Book details