Sashe 151
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
gaji da zaman shi ba, sai don bayason yaja ma kan shi bala'e. Fitarshi keda wuya Unaisah ta bu e idanunta da suka ka a jawur da su, ga wani zafi da temperature din jikinta ya dauka kamar mai fama da zazzabi. ta rasa gane meke mata dadi, fitar Danish daga akin yasa taji batasan cin komai, mineral water kadai ta sha ta mi e jikinta na tsuma ta nufi hanyar fita daga dakin muryar aunty Ummi ta katse ta"Wai lafiya? Shi ya fita baici komai ba, kema kin mi e zaki fita? Meke damunku ne"? Ta tambaya kamar batasan meke wakana ba. Yamutsa fuska Unaisah tay tare da kallon Ummi datay maganar "Wayata zan dauko adaki, yanzu zan dawo" ta fadi hakanne don kada su zargi wani abu. kumshe dariya ummi ta yi abakinta, tana lura da yadda jikinta ke tsuma. "Okay, muna jiranki" fucewa tayi daga dining din tana tafiya da nawa kamar wadda kwai ya fashe mawa, tana shiga dakin su ta fa a toilet taja ofa ta datse, zama tay akan toilet seat tayi shiru tana tariyo abunda ya faru a dining room. Ta rasa gane dalilin dayasa take tsintar kanta awani yanayi duk idan tagan shi ko taji muryarshi! Batasan menene ba, ta kasa ganewa. bata gama zancen zucin ba, zatayi tsarkin fitsarin da tayi taga wannan farin ruwan mai yau i wani irin kyankyami da kyamane suka kamata, da sauri tayi tsarkin ta fito ta tsaya abakin kofar toilet tana faman sauke ajiyar zuciya, bayanin aunty Umminsu ta fara tariyowa a lokacin da take fa a mata dalilin dake kawo shi, abun da ya daure mata kai kallon juna kawai sukayi ba wani abu ba amma sai gashi ta gan shi, dole ta nemi arin bayani agurin Aunty ummin su. Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. ga yunwa tana ji sai dai bata jin zata iya komawa dining room din, fa awa tayi kan bedmattress ta janyo pillow ta rungume shi a kirjinta, wani sanyine ke ratsa zuciyarta, ga wani dadi da take ji a jikin ta. ta shafe tsawon mintuna shabiyar a kwance ba tare data motsa ba. "Sister, Aunty Ummi tace kizo wai" muryar hawwa ce ta katse mata zancen zucin ta, ba tare da ta bude idanunta ba tace"okay, gani nan zuwa" bayan fitar hawwa daga dakin ta sauko daga kan gadon ta, ta gyara mayafinta, tana okarin fitowa daga dakin kamar daga sama taji Sallamar Salsabeel da sauri ta juya ta dubi kofar falon, a tsaye yake ya auki wankan shadda kamar ba shi ba, hannun shi ru e da trolley, kwata kwata bai lura da ita ba. "Yaya salsabeel," muryar ta ce ta fargar da shi, murmushi yayi tare da nufarta yana jan trolley "Unaisah ykk" da fara'a tace"lafiyalou, ya salsabeel kwana biyu baka leko mu ba, munyi fushi" ta fada tana ha e fuska yar dariya yayi"i'm really sorry, wlh kuna araina, yanzu hakama da kika ganni saboda ku nazo" a mashi hannu tayi"kawo na ru e maka trolly din" mi a mata yai tasa hannu ta ru e handle din"Menene aciki? Ko kayanka ne"? Girgiza kai yai" mu karasa ciki, zan nuna maki abunda ke a cikin shi" amsa mashi tayi da toh suka nufi cikin falon akan sofa Ya zauna, Ta aje trolley din agaban shi Yace mata ta kira sauran yan uwanta ya fa a yana hangen su a dining room suna cin abinci sam basu lura da shi ba, da sauri ta juya ta nufi dining room din ta shiga ta kira su, tun da suka ji ta ambaci ya salsabeel ya zo kowa ya ajiye spoon din hannun shi, Cike da zumudin son ganin shi suka fito daga dakin su dukan su hada Ummi. Kafin su karaso ya mike fuskanshi dauke da fara'a ya gaishe da ummi ta amsa mashi da fara'arta, kallon su Haris yayi daya bayan aya aranshi yana tariyo lokacin da suke a prison, rayuwa ta canza sun wadatu da kwanciyar hankali Hannu ya mi a ma mazan sukayi musaba, Ya dubi Yan matan dake ta faman hade rai Dariya yayi"fushi kuke dani"? Khadeeja tace"eh mana, tun yaushe rabon da kazo gurin mu, ka manta damu.." Mubeen Yace"kullum sai munsa ran zuwanka amma saika ki zuwa" gaba daya suka rufe shi da korafe korafen su dakyar Ya samu ya shawo kan su, har suka hakura da fushin da sukeyi da shi bayan sun gama gaisawa da junansu yace su zauna zasuyi magana mai muhimman ci. Bayan Kowan nan su Ya samu guri Ya zauna kan Sofas suka nutsu suna jiran jin me zaice masu. "Ya salsabeel, Wannan akwatin fa? Ko tsaraba ne ka kawo mana" parveen ce tay maganar tare da nuna akwatin da hannu "Eh tsaraba ce amma bata abun ci ba, Kayan sawa ne" kallon juna su kayi da mamaki akan fuskokin su. "Ina Danish"? Ya tambaya yana kallon su "Yana a daki" suka ha a baki gurin bashi amsa" Yace"okay, wani ya kira min shi" Haris ne Ya mike da sauri Ya je kiran shi. falon yayi tsit baka jin hayaniyar komai, duk sun agara da son ganin menene acikin trolly din me kuma ya Salsabeel zai fada masu mai mahimman ci'? Jim ka an saiga Haris Ya dawo tare da Danish, Har ya canza kayan jikin shi yanzu silk pyjama ne a jikin shi na bacci. Tun shigowarsu Falon, Unaisah take satar kallon shi, bayan sun rungume juna da salsabeel a amutunce suka gaisa da junan su kafin daga bisani kowan nan su Ya zauna suka nutsu suna kallon salsabeel Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. "Mu farayiwa Annabi salati" suka amsa mashi da toh, bayan sun gama yayi shiru yana binsu da kallo aya bayan aya kamar mai nazarin wani abu, Azeeza da Jemimah sai faman kumshe dariya su ke yi kamar wasu zautattu. aya bayan aya ya fara kiran sunayen su, duk wanda ya kira sunan shi sai ya amsa mashi da Na'am, ummi dai tayi shiru tana jiran jin me zaice ma su Numfasawa yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa "Gobe Idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya, za'a tafi daku Isod headquarter...." Kallon juna su ka yi arude suka maimaita sunan Headquarter, Sajeed Yace"me za mu yi acan in"? Da alama sun ru e, murmushi Salsabeel yayi kafin yace"zaku gana da manyan jami'an Isod" Hankali tashe Unaisah tace"mu in"? Jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, Lokaci yayi da zasu gana da ku, don suji daga bakin ku, Suna bukatar bayani game da rayuwarku a gidan kurkukun addara, zasuyi maku tambayoyi da suka shafi rayuwar da kukai agidan kurkukun addara da kuma shi kanshi gidan kurkukun" Ya fada yana duban fuskokin su sunyi shiru suna sauraronshi kowa da abunda ya e sakawa aranshi. "Nazo ne don in arfafa maku gwiwa, nasan akwai masu jin tsoro har yanzu acikin ku, to inaso ku aje tsoron nan gefe aya da duk wani shakku da zakuji, yanzu lokaci ne da zaku bada gudummuwa ku taimaka masu gurin kawo karshen kurkukun kaddara, bayanan da zaku basu da su zasuyi amfani wurin yin binciken wa anda suka azabtar da rayuwar ku, kada ku 6oye masu komai, duk mun antar abu da kuka sani ku fa a masu zai iya zama mai amfani agare su" tun da salsabeel ya fara magana Danish Ya rufe idanunshi gam kamar baya atare da su, sarai salsabeel Ya lura da yanayin shi. "Ku fa a masu irin kuncin rayuwar da kukayi, Ku fa amasu azabtarwar da sukayi maku da kuma wulakanta rayuwarku da su ka yi, ku ka ai kuka san meya faru arayuwarku, tunkafin ku mallaki hankalinku kuke a kulle ba shige ba fuce, idan har kuka 6oye wani abu baku fada ma su ba, kanku zaku cuta, kwara ku tona masu asiri don uban su kowa yasan me suke aikatawa" ya fa a tare da bugun sofa din da yake zaune akai da hannun shi. "ku daina ganin ayanzu kun tsira kun samu rayuwar anci wallahi har yanzu rayuwar ku tana acikin ha ari saboda ba zasu yale ku ba, suna nan suna bibiyar rayuwarku don su salwantar daku saboda kune prisoners na farko da suka fara karya dokar kurkukun kaddara, tayaya ku ke tunanin zasu yale ku? Ay ko dan kada ku tona masu asiri dole su nemi hanyar da zasu shafe babin ku" Maganar salsabeel ta aga hankulansu, Tuni ido ya raina fata, wasu daga cikinsu har sun fara sharar kwalla, ya fa a masu hakanne don Ya tsoratar da su ya kuma tunzura su don su fusata su samu kwarin giwar tona masu asiri idan jami'an sirrin suka tambaye su. "Ko ba don saboda ku ba, Ku tuna an uwanku da kuka bari agidan kurkukun addara! Wa anda basu ji ba basu gani ba kamar ku dai, suna can ana azabtar da rayuwarsu, Sun maida su kamar dabbobi sai azabtar da su sukeyi, meye ribarku idan ku kun samu jin dadin rayuwa su kuma suna awahala? Baku da burin ku dauki fansar abunda akayi maku? Sannan ku cecei rayuwar yan uwanku? Za ku ja baki ne kuyi shiru acigaba da salwantar da rayuwar kananun yara da basu ji ba basu gani ba"? Ranshi a6ace yayi maganar yana kallon su, Jiki asanyaye sajeed Ya sauko daga kan sofa, Ya dawo asa ya zauna hannayen shi biyu tallabe da kan shi, Idanunshi sun ciko tab da kwalla. Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. Shesshekar kukan su ne Ya cika falon, kalaman salsabeel sun fama raunin dake acikin zuciyar su..." Salsabeel bai dakata ba saida ya tabbatar sun fusata sun harzuka kafin ya tsagaita da yin maganar Yana jiran jin me zasu ce. Cikin shesshekar kuka sajeed yace"wallahi ko ba ka fada mana ba, ba zamu raga masu ba, ni ashirya nake da duk wata tambaya da za'ayi min, nayi alkawarin zan fadi iya abunda nasani saboda