Sashe 228
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant in kurkukun addara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya ago ya dubi Benazir suka ha a ido cikin na juna. "A lokacin baya, kafin addara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?" Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba ha a ni da shi..." Bata are maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai. Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi arya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yun urin kashe ni" "Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya ha a ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..." Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da walwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta. "Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba aramin taimako zaiyi mana ba" Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su ha i da karantar yanayinsu ta fuskarsu. Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin ra a, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls" Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice. Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da in murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku" Shiru suka dan yi na wani lokaci. "Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim an hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi. Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene ala ar ku da ita?"? Har suna ha a baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama. "Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya ago ya kalle ta, a kunne ta yi masa ra a, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya fa a masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana" an ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i, Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai," Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief. Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi. Lokacin data arasa basu labarin idanunta cike tab da walla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi aurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna an jinjina heads din su, shi dama Taj ya da e yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce. "Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo aya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta" Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..." Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna. "Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka al awarin Ummi won't leave this house until everything is settled" Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya. "Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya fa a yana duban su, "Unaisah, ta i kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta i accepting din ta saboda ta ullace ta aranta. "Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah" Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle. "Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku fa a ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya fa a yana nuna floor da index finger insa. "Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure ka an zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai" Gaba aya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi al awari zasu kiyaye. "Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta fa a tana duba wrist watch din hannunta. Taj ya ce, "Zamu ru e wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya" Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara. Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi. yar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?" Taj ya ce, "Mi zai hana." ya auko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya. Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu. "Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su. Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir. Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya bu e idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya ha e rai, "Baki tafi ba?" "Taya zan tafi kana fushi dani" aure mata fuska ya yi. "Pls abunda ya faru azu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya. "Na ji, ya wuce." "Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ru e kwalar rigana kamar zata doke ni!" Ya fada babu wasa akan fuskarsa. Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta fa a tana yi mashi farfari da idanunta. Hakan da tayi ba aramin sace zuciyar shi ta yi ba. "Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta. agowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah. "Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da afa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...." Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da