← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 62 OF 247

Sashe 62

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

to tabbas za ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoners in da suka tsira daga kurkukun addara ba, su ne na farko kuma sune na arshe, da farko sunyi nasarar etare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahalu in da ya isa ya iya etare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya auke shi munyi nasarar yi mashi abunda zai dawo gare mu sai dai wani abun al ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi_ Kamar yadda suka ce tun tarihin kafuwar kurkukun addara ba'a ta6a samun prisoners da suka tsira ba sai akan su, kuma ba kowa bace sila face addarar kurkuku, da ace unaisah ba ta kasance a gidan kurkukun ba, wallahi Danish bazai ta6a yun urin taimaka ma wani don ya gudu daga cikin sa ba shiyasa bai ta6a taimakon su Deeja ba bayan yana da hanyar da zai iya fitar da su. Salsabeel Ya ci ba ar wahala wurin awainiya da su Hibba, babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, saboda yankin da su ka fa o a dajin babu ko kayan marmari da mutun zai sha, yasha jaraba yin amfani da sihirinsa don ya sawwa a masu wahalar amma abun ya faska, Saida ta kai ga ciyawa su ke ci ko su ci ganye don suyi maganin yunwar cikinsu, ga Deeja ba hankali tun da tafarfa o sambatu takeyi shi kuma Mubeen wasu irin marurai ne masu masifar zafi suka mamaye fatar jikin shi, kullum sai yayi hauka kamar zai rasa ransa saboda ra adin azaba, ga uwar rana dake walo masu ta ko'ina ba sauki, ga damuwar rashin yan uwansu sunyi kuka tamkar zasu kashe kawunansu, ba in cikin da suka unsa baya misaltuwa, hakika salsabeel yayi namijin kokari wurin ganin Ya basu kulawa duk da wani lokacin abun nema yake yafi arfinsa, gaba aya sun jigata sun sha wahala, babban tashin hankalinsu miyagun halittun daji dake kawo masu farmaki, kusan kullum ne sai Salsabeel Ya zubda jinin shi wurin fa a da su. Satin su aya acikin dajin suna shan ba ar azabar rayuwa, acikin rana ta takwas suna cikin tafiya agalabaice sunata yi ma Salsabeel kukan yunwa suke ji ma oshinsu zafi yake yi masu ruwa zasu sha bawan Allah Ya rasa ya zaiyi da su, da gudu Ya nufi Cikin dajin yana neman inda zai samo musu ruwa tun yana tafiya da kuzarinsa har afafuwan sa suka fara sagewa sai da yagama shan wahala bai samu ruwan ba yana kan hanyar komawa wurinsu kwatsam ya fa a wani yanki na dajin ba zato ba tsammani ya hango gungun Sojojin asar Ghana da suke yin atisayen horaswa a dajin, da gudu ya tunkare su kamar mahaukaci haka suka ganshi Ya fa o masu, har sun saita shi da bindigu ya zube kan gwiwowinshi ya fara rokon su akan su taimaka mashi da ruwan sha, gaba aya sojojin suka kewaye shi hannunsu ru e da bindigu saboda basu yarda da shi ba, sunyi tunanin wani mugunne shiyasa basu bashi taimakon daya bu ataba, tsawa suka fara daka mashi suna tambayar shi wanene shi? Meyake yi a cikin dajin, sam ya kasa ba su amsa, kwatsam ana haka sai ga su mubeen sun watso da gudu iya arfinsu suna neman shi wata dabbar daji ce ta biyo su aguje, a gaggauce sojojin suka harbeta da bindiga tun kafin su araso nan take suka tarwatsa kan dabbar ta fa asa tana birgima, ai koda sojojin suka ga prisoners sanye da jajayen kaya masu numbers a jikinsu sai suka fara zargin salsabeel ne Yayi garkuwa da su tun da shi ne babba acikin su kuma jikin shi akwai zanan tattoo, wanda alama ce ta tambarin wata ungiya, ba su tsaya bata lokaci ba suka aure Salsabeel da igiya tamau, su Mubeen sunata kuka suna rokonsu su yale masu an uwansu amman ko ta kansu sojojin ba su bi ba, gaba aya suka sanya su a bayan motarsu ta sojoji, ba su nufi ko'ina da su ba sai cikin asar Ghana. Bayan isar su, A headquarter suka ru e salsabeel wurinsu, su kuma su Hibba Asibiti suka mi a su ganin muggan raunin dake a jikin su, babu irin bugun da sojojin nan basuyi ma Salsabeel ba don ya fa a masu me yakai shi daji tare da ananun yara amma ya i fa a masu, sai ce masu yai bazai iya tuna komai daya faruwa da shi ba, ya fa i hakanne saboda bai yarda da sojojin ba yasan ma koya fa a masu gaskiya ba lallai su yarda ba, A alla ya shafe kwana uku a hannun sojojin kafin ya fa a masu cewa su an nigeria ne, iya abunda zai iya tunawa kenan a rayuwarsa, ba su sake shi ba har sai da su rubina dake a Asibiti suka samu lafiya sunata tambayar ina an uwansu Salsabeel tukunna sojojin suka gane cewa ba mugu ba ne, ba su tsaya 6ata lokaci ba don sun fahimci al'amarin su babba ne ba kamar rahoton da Asibiti suka bayar, hakan yasa suka tuntu6i hukumar sojin Nigeria don su sanar da su dangane da yaran inyaso sai su mi a case in wurin su. Lokacin da sa on Ya riski su Sir Mubarak, bayan ya duba duka bayanan yaran, nan take ya yanke shawarar kiran chief owais don ya sanar da shi zancen case in saboda yafi dace wa da hukumar Isod, su yakamata case din yaran ya kasance a hannun su saboda abune da ya shafi 6angaren bincike. Chief Owais yayi farin ciki lokacin da Sir Mubarak ya sanar da shi, dama a lokacin sunata faman bincike kan yadda zasu gano Unaisah, daga shi har taj sunyi tsammanin cikin yaran zasu ga Angel, sai dai ko da sukaje Ghana suka dubasu babu ita aciki, aranar da sukaje basu kwana ba, sai da suka ha a yaran gaba aya tare da Salsabeel suka tafi da su a privet jet din chief suka shigo Nigeria.... Bayan komai Ya lafa, Sun sama masu gidan da zasu zauna, basu fara bincikar su ba don sun lura da ba'a hayyacinsu suke ba, sai dai suna lura da duk wani motsin yaran sunyi matu ar yin al'ajabi da irin rayuwarsu, ba su san komai ba, kamar ranar aka haifo su duniya, daga sunci abinci sai bacci, ba zancen yin sallah, ranar da boss ya kunna masu kallo a tv sunga tashin hankali, kuka suka dinga yi ganin ba on abu da ba su ta6a gani ba, a arshe deeja ce tayi silar mutuwar tv Chief ne ya aukar ma su Jazz a matsayin likitan da zai dinga duba lafiyar su, kafin ya bashi aikin sai da ya garga e shi akan kada ya kuskura ya sanarma kowa ko da kuwa mommynsa ce, shiyasa dr jazz ya i sanar ma kowa nashi wanda silar hakan yaja har sir mubarak ya fara zargin shi akan wayar da yake yawan kama shi yanayi ta maganar gidan kaji, matsalar da aka samu shi Sir Mubarak baisan da zancen Aikin da Jazz ya ke yi ma chief owais ba, sannan baisan a gidan da chief owais ya killa ce su ba, amma Yana bibiyar case din yaran don jin wani hali ake ciki game da binciken su. Bayan wasu yan kwanaki, Su chief suka tuntu6i Salsabeel suka tsare shi da tambayoyi dangane da rayuwarsu, bai 6oye masu komai ba gaba aya ya sanar da su, wa'iyazubillah kusan zaucewa sukayi saboda tsananin tashin da hankulansu suka yi, ba su ta6a jin labarin daya gigita su ba irin wanda Salsabeel ya ba su, abu kamar ashirin wasan kwaikwayo amman wai a zahiri yake faruwa zuciyoyin su sun karaya ainun. to a cikin labarinsa ne suka ji ya ambaci sunan Angel, sunyi matu ar girgiza da jin cewa tana a cikin su, kuma sun raba hanya da su, hankalin su ba aramin tashi yayi ba, musamman taj kamar zai zauce jin cewa Angel dinsa tana a cikin su, ba dan zuciyar imani ba da tuni ya ha iyi zuciya ya mutu, ganin yadda yake kuka kamar aramin yaro yasa Salsabeel tambayar shi meya faru, Chief ne ya bashi amsa da cewa yarsa ce Angel in da ya ke magana akai, wani irin farin cikine ya lullu6e Salsabeel ganin Mahaifin unaisah, jiki na rawa ya ru o hannun shi tamau ya fara jinjina mashi yana fa in ya gode ma Allah saboda yarinyarsa tana da kaifin basira Allah yayi mata baiwar da zaiyi wuya asamu mai irin ta, bayan haka yace da shi ya kwantar da hankalin shi, in sha Allah babu abun da zai faru da su saboda suna atare da garkuwa yayi imanin in har ba lokacin mutuwarsu ne yayi ba to kuwa zasu ku6uta batare da sun cutu ba, abun da ya dace shine su tayasu da addu'a kuma a bibiyi dajin evil forest inda rabon agansu toh, shi kanshi Salsabeel in yayi mamakin da ewarsu a dajin, amma da yayi zurfin tunani sai ya tuna cewa Danish baisan inda zai kai su Unaisah ba, shi iya rayuwarshi daga gidan kurkukun addara sai cikin dajin evil forest, bai ma ta6a sanin akwai wasu mutane dake rayuwa a wajen dajin ba, kuma hada arin ba su da taswirar dajin da komai zaifi zuwa masu da sau i, saboda dajin evil forest kurman dajine yana da wuyar sha'ani. Jami'an isod sun yi matu ari wurin ganin sun gano su a dajin, kusan kullum ne sai jiragensu sun kewaye shi suna shawagi Allah ne dai bai nufa za su ha u da su ba. Babban abun da yaja ma su Angel da ewa a dajin, Lokacin da Danish ya ke yin amfani da sihirinsa wurin jigilar aukarsu idan dare yayi lokacin sun yi bacci yana yin tafiya mai nisa da su
Chapter 62 · 0% Book details