← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 70 OF 247

Sashe 70

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature _________________________________E22 Ta jima tana kallon hotunan kafin Ta mi auke da su a hannunta, da sauri ta juya ta nufi mirror drawer ta bu e gida na uku ta saka su a ciki. Tana arin mikewa sallamar Taj Ta katse mata hanzarin ta daga wajen dakin ta jiyo muryarsa. "Daddy gani nan zuwa na gama shiryawa, waya ta nake nema banganta ba" "Ina kika ajiyeta ne"? Watsa hannu tai kamar tana agabansa na manta daddy "Jiya naso na ganta a hannun an uwan ku sajeed, bari na tambaye shi" amsa mashi tayi da toh aranta tana mai mamakin yadda sajeed yake da nacin son waya, sam baya gajiya da ita." Badajimawa ba, taj Ya turo kofar dakin Ya shigo hannunshi ruke da wayar. Face dinsa da murmushi Ya mika mata"Na lura baki son wayar nan taki, saboda ba ki damu da ita ba, me zai hana ki bar ma sajeed din tun da yafi ki sonta" Muryarta da yar shagwaba tace"wallahi inason abuna, sai dai asiya masa wata tunda Yana so, dr laura fa ta bani ita taya ma zan bada ita" ta yi maganar tare da kar6ar wayar daga hannun sa "Kin ta6a kiranta ne kunyi magana"? "Mantawa nakeyi wlh, amma in sha Allah zan kirata in na samu nutsuwa" "Baki kyautaba yakamata kiyi kokari ki kirata" amsa mashi tayi da toh "Daddy dani kadai zamu tafi"? "Eh, next time suma zan kai su gidan" o hannunta yai acikin nashi, suka fito daga dakin, babu wanda Ya lura da su fira taja hankulan su, tana kallon su Deeja dake ta faman sakin murmushi wani irin sanyi taji aranta, yanzu damuwarta akan sauran prisoners ne wadanda ke AGIDAN KURKUKUN ADDARA! Har sun kusa fita daga falon, Kamar ance ta wurga eye balls dinta kan second floor, kwatsam Ta hango Danish dake kallon ta, cikin shiga ta pajama launin blue sky, tayi tunanin ba ita Yake kallo ba, sai tai saurin kau da idon ta, gudun kada ya ga za su fita, tasan halin mutumin nata. Suna fita daga falon ta sauke ajiyar zuciya, kasancewar baida nisa part din nashi, A afa suke tafiya suna fira hanyar da suka biyo ko'ina hasken electric bulbs ne tamkar ba dare ba ga wata iska mai ni'ima dake ka "Daugher, kina jin sautin da nake Jiyowa kuwa"? da mamaki Tace A'a daddy menene"? "Akwai mutun abayan mu, baki ji sautin tafiya ba" a an ru e ta furta mutum kuma? Wanene? bata jira ya bata amsa ba tayi saurin juyawa don ganin waye. Har saida gaban ta ya fa i idanunta adan zare take kallon shi, Hannayensa har e akan kirjinsa, fuskarsa babu fara'a, kayan baccin da ta gan shi da su sune a jikinsa fararen afafuwansa ko takalma babu. Juyowa taj yai tare da kallon shi, ashe tunda suka fito Yake biye da su, shi taj yasan da zaman shi itace bata lura ba. Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"daddy, mu tafi da shi kawai" ar dariya taj yai tare da cewa"ya zama dole ay, wa ya isa ya hana shi zuwa"? "mu tafi My man, nayi zaton kayi bacci, shiyasa ban neme ka ba, dama zamu je part din daddyna ne don in gaisa da Auntyna" kamar jira yake ta bashi damar yabi su, da sauri ya nufe su, a maimakon ya tsaya gefen ta sai ya shiga tsakaninta da taj, yasa hannu ya raba hannayensu dake ruke cikin na juna lamarin ya daurewa taj kai aranshi ya ayyana wannan wani irin namijin kishine? Uban nata ma bai yale ba inaga idan wani ne daban ba? Tun yanzu ya fara jin fargaban yadda zata kaya tsakanin chief da danish tabbas akwai ura. A haka suka jera har suka araso ofar shiga Part din, Komai nasa shigen kalar na sashen da suke ne banbancin ka an ne amma fa Ya ha u, Ita kanta Angel tayi mamakin katafaren Ginin gidan Chief gari guda An awatashi kamar A dubai. Dafe kofar taj yai da hannunsa a hankali ta zuge masu, katafaren falo ne an kawatasa da furniture, ga wani sanyin A.c na mai sanyaya zukata Sai ara kallon ko'ina take tana an jinjina kanta, har cikin ranta ta ara jin aunar chief saboda kyautatawarsa ga daddyn ta. "Bismillah, Ku zauna bari naje nayi mata magana" ya fada tare da wuce ya nufi upstairs. A hankali suka zauna kan sofa, kallon sa tai suka hada ido cikin na juna. "Baki kewata ba? kin manta da dani jiya ko ki neme ni" yana magana tamkar baisan motsa lips dinsa "Ni da kai waye mai laifi? Jiya ko kallo ban ishe ka ba, ka kama hanya ka bi uncle din chief inata kallon ka ko waiwaye na bakai ba" ta fa a tana kwa6e masa fuska Lumshe idanunsa yai batare daya furta mata komai ba "Har ciwon ciki nayi jiya kamar zan mutu, ni kadai a restroom na kasa bude kofa har na fadi kasa na suma duk kana ina"? "Ina atare dashi," atakaice Ya bata amsa o hannunsa tai tana kalllon dogon yatsan hannunsa dake asanye da silver ring, yayi matukar yi mata kyau "Shi ne Ya baka wannan"? aga mata kai yai alamar eh, Da fara'a akan fuskarta tace"Bani labarin abun da ya faru tsakanin ku jiya"? Sai da ya fara kai soft lips dinsa saitin kunnanta kafin ya fara bata labari saboda bai iya aga muryar shi. Sai faman sakin murmushi takeyi hakika taji dadin kyautatawar da prime minister yayi masa, kuma ta fahimce shima yaji dadi tun da gashi nan da bakinsa yake bata labari mutumin da be cika surutu irin haka ba. "My man, Ni dai fatana Allah yasa mutumin nan ya zama alkhairi agare ka, wlh tunda nagansa naji ya kwanta min araina saboda kamannin dake a tsakaninku..." kafin ta are maganar Sautin takalman daddynta ne Yaja hankalin su ga dubansa, saukowa yai down a hanzarce Ya nufe su Yana fadin"daugher, bacci takeyi auntyn naki, ko zaki je ki same ta adaki, Inaso ki bata mamaki" murmushi tayi tare da mikewa da sauri Danish Ya mi e zai bita, kallon shi tayi cikin sanyin murya tace"ka zauna ka jira ni, Yanzu zan fito ba da ewa zanyi ba" Taj dake kallon su murmushi yai tare da arasawa gefen Danish yace"Idan saboda ni ne, To mu zauna gani ka gaka ita sai ta shiga watakli hankalinka zaifi kwanciya,' Kamar kuwa yasan sbd shi Ya mi e zai bita, komawa yayi ya zauna hankalinsa akan Angel dinsa Harta haura kan stairs. A hankali Ta zura kafarta cikin dakin, tana shiga ta soma bin ko'ina da kallo masha Allah, a hankali ta sauke idanunta kan Danejo dake a nanna e cikin bargo sai sharar baccin ta take yi. watsa wa tayi da gudu ta daddage ta haye kan gadon gaba aya ta ameta tana dariya, wata irin firgita danejo tayi cikin magagin bacci take fadin"daddyn Angel, wayyo Allahna kana ina wai wanene ke takura min! Nashiga ukuna" Yaye mata bargon Angel tayi, tana faman haki ta bu e idanunta wa anda suka kada jawur saboda bacci, A hankali ta sauke su kan fuskar Unaisah ta ura mata ido tana kallon ta, da tsantsar ru ani take binta da kallo, Itama unaisah kallonta takeyi cike da kewarta, ba zata ta6a mantawa da fuskar denejo ba, ta ara haske fara jawur da ita kamar ba'indiya saboda kyau, ga gashin kan nan nata mai tsayi baki wulik har gadon bayanta.. Muryarta a an tsorace ta furta"wacece ke"? Mutun ko aljan"! Dariya unaisah tayi cike da nishadi tace mata"Baki gane ni na"? Waro idanu waje danejo tayi da arfi ta furta"ANGEL" tuntsirewa unaisah tai da dariya tare da fa a mata ta sake rungumeta, daura hannayenta biyu tayi akan bayanta tana fadin"Ni ce, Angel dinki, ashe da rabon zamu sake haduwa danejo na" mamaki Ya hana danejo magana, da sauri ta tallabo fuskar unaisah da tafukan hannayenta, ta kura mata ido tana kallon ta batare da ta kyafta idanunta ba, ko amafarki taga fuskar Angel sai ta shaida ta, duk da ta ara girma a yanzu ta zama yar matashiyar budurwa, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta, da sauri ta kwantar da unaisah kan kirjinta, itama kukanne Ya kubce mata, sautin shesshekar kukansu duk Ya cika dakin, a hankali take shafa sumar kanta tana faman sauke ajiyar zuciya, Allah ne kadai Yasan irin kaunar da take Yi mata, taso unaisah, tayi kukan rashinta kamar zata zauce, muryarta kasa kasa ta furta"Alhamdulillah Ya Allah, nagode maka wallahi bazan Iya misalta farin ciki da nake aciki ba, Ya Allah nagode maka daka bayyana min Angel ina, Ya Allah nagode maka...." cikin shesshe ar kuka ta fa a, tama rasa inda zata tsoma ranta saboda murnar ganin Angel. agowa unaisah tayi tasanya tafin hannu ta goge mata hawayen cikin sanyin murya tace"Aunty Danejo, naji dadi da Allah Ya sake ha a ni dake a matsayin matar daddyna, I can't thank you enough saboda halaccin da kikai min arayuwa Allah ne kadai zai Iya biyan ki, kin so ni kin kuma kaunace ni tsakani da Allah, duk da bakisan koni wacece ba a lokacin amma kin taimaki rayuwa, kiyi hakuri ki yafe min laifin da nayi maki....' tana fa a tana matsar kwalla. "Angel laifin me kikai min? Ni ay baki min laifin komai ba...." Girgiza kai tai hawaye nabin kuncin ta tace"nayi maki laifi, bayan mun sha u da juna, na gudu daga rugarku kina ji kina gani har biyo ni ki ka yi kina kiran sunana don in tsaya amma naki sauraronki, ashe da rabon in sha wahala" idanunta acikin na danejo takeyin maganar "duk da bana danasanin addarar rayuwar da ta riske ni saima farin ciki da nakeyi saboda a kowani rashi da nayi toh akwai nasara acikin sa" tun da tafara magana danejo ta nutsu tana sauraronta, har cikin ranta tana mai mamakin girman yarinyar da kaifin basirarta, komai nata na dabanne shiyasa take da saurin siye zuciyar mutune. "Aunty danejo, Kinga ikon Allah ko? Bayan na tafi sai gashi Allah Ya hada ki da daddy na har kun yi aure, amma baki takura kanki ba
Chapter 70 · 0% Book details