Sashe 44
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
Basu tsaya bata lokaci ba suka afka cikin ruwan don su ceto rayuwar dan su, ko da suka shiga, Habu Ya kankame kakansu Yana sambatu iri iri, ya dinga nuna masu saitin inda yaga halittar da hannun shi, da sauri aya daga cikin kakannin nasa mai karfin Hali ya kutsa kai cikin don ya kashe halittar, aikuwa yana shiga yayi tozali da mutumin dake a kwance kasan ruwan, lamarin ya daure mashi kai, ganin an mutun acikin ruwa, aranshi ya dinga tunanin mutunne ko aljan? Watakil aljanin ruwa ne" Wasi wasi yaci gaba dayi, har zai tafi sai kuma zuciyarsa ta dinga azalzalarshi akan ya dauko mutumin watakil tsautsayine ya afka da shi... Baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya kinkimo tajuddeen abunka ga tsohon kashi na majiya karfi wadanda suke da shirinsu baiji nauyin taj ba akan kafadarshi ya sargafo shi, Ya fito masu da kawunansu daga cikin ruwa, ya aga murya yana fadin"Ta mutunce ba aljani ba," Gaba aya suka zaro idanu waje suna lekensu kowa da abunda yake sakawa aranshi, Bayan sun fito dashi daga ruwanne suka kewaye shi suna kallon shi, anan suka ga alamar bai mutu ba, da ranshi, wani abu daya basu tausayi game da shi, mummunan raunin da suka gani akan tafin kafarsa ta dama, fatar wurin ya rarake yayi rami, ba tare da sun 6ata lokaci ba suka tafi da tajudden can rigarsu, a inda suka cigaba da bashi kyakkyawar kulawa suka aure masa raunin kafarsa bayan sunyi mashi an dabarun su na mutanan daji, tsawon kwanaki baya acikin hayyacinshi, ko bacci yake yi ya dinga farkawa kenan yanayi masu sambatu akan yarsa da ya baro cikin ruwa, sun rasa gane me yake nufi saboda basa jin harshen hausa, wani lokacin kamar zautacce yai ta kuka yana ambaton sunan Angel, a kalla taj ya shafe tsawon watanni ba tare da ya iya taka kafarsa ba, wannan dalilin ne yasa bai samu damar zuwa neman Angel ba, bayan haka ya yi loosing memory dinshi, sunanta ne kadai ya tsaya mashi aran shiyasa yake yawan ambatonshi.... Lokacin da ya fara samun sauki yaci gaba da rayuwa da su yana ta kokarin ya tuna miya faru dashi amma ya kasa saboda lalurar data sameshi a haka ya rayu a rigar su na tsawon shekara biyu cikin ikon Allah a daren wata rana yana tsaka da baccinsa yayi wani mummunan mafarki dangane da Angel dinsa wanda ya yi silar dawowar memory din shi, tun a cikin daren ya fara kokarin barin rigar don yaje nemanta gaba daya ya tada masu hankali duk wani mai bacci sai da ya farka yai ta ambaton sunan arsa da ya jefa cikin ruwa yana ta kokarin kwatanta masu sai dai sun kasa gane me yake nufi, lallashin shi suka cigaba dayi suna kwantar masa da hankali, a dole ya hakura bai fita a daren ranar ba, A Washe garin ranar da sassafe kakansu habu ya bashi kyautar sandar da zai yi amfani da ita wurin yin tafiya, saboda har time in kafarsa bata dawo dai dai ba, lokacin da su habu zasu tafi kiwon shanu sai yabi bayan su don ya nemo Angel dinsa, sai dai kash ita kuma a lokaci har wannan tsautsayin ya fada da ita, tana acan gidan kurkukun kaddara, kuma bata jima da barin rigarsu Danejo ba, shi kuma yafara zuwa nemanta, tunda yaga kogon ruwan ya afe babu ruwa acikinsa saboda damuna ta wuce, mutun na iya ganin komai dake a kasan ramin, yayi kuka na fitar hayyaci kamar ransa zai fita, har yunkurin fadawa yayi don ya kashe kanshi, da sauri su habu suka rirrike shi tare da jan shi suna lallashin shi, saidai sam baya fahimtar me suke cewa. Sai da takai ga abakin ramin ruwan yake kwana tun safe har dare ya ritsa da shi baya motsawa anan fulanin suke zuwa kawo mashi abincin da zai ci, tunda ya i komawa rigarsu, yafi son zama bakin ruwa, hakika sunji tausayinshi duk da basu san meke damun shi ba, saboda son da kakansu habu keyi mashi, bukka ya ha a mashi a wurin saboda yaji dadin cigaba da kwana abakin ruwan, hada bargon lullu6a suka mallaka mashi, da duk wani abu da zai bu ata...... Bayan wani lokaci, awata rana yana zaune abakin ruwan yayi zurfi a cikin tunaninsa, sai ga bafullatanar dajin da ta taimaki Angel, ta koro shanayenta zuwa kiwo, ita kanta bazata tuna rana ta karshe da ta zo bakin ruwan ba tun bayan da angel ta gudu tabar rigarsu bayan ta gama haukan jimamin rashinta gaba aya danginta suka hanata fitowa kiwo, sai dai yan uwanta suka cigaba da yi, sai ranar ta samu suka barta, bata nufi ko'ina ba sai bakin ruwan da yabar tarihi a zuciyarta, tana cikin tafiya ta hango sabuwar bukkar da akayi abakin ruwan ga kuma mutun zaune ya zura kafafunsa cikin ramin, Kamar a mafarki haka take kallon shi, gaba aya hankalinshi baya akanta.... Sautin kukan shanayenta ne suka dawo dashi daga zurfin tunanin daya shiga, firgigit yai tare dakai idanunsa gareta, duk a tunaninsa su habu ne suka zo yin kiwo, ko da idanunsa suka yi masa tozali da fuskar kyakkyawar matashiyar budurwa kamar aljana, da sauri taj ya mike yana kallon ta da tsantsar mamaki akan fuskarshi, babu wanda yayi ma wani magana acikinsu sai kallon kallo da suke jefawa junansu, ita dai danejo kallon sani take yima fuskarshi duk da tayi imanin wannan ne karo na farko data fara ganinshi, yayin da shi kuma tajuddeen baisan dalilin kallon da yakeyi mata ba, ya dai yi mamakin tsantsar kyawun dake gareta. Jin shirun yayi yawane yasa ta soma yi masa magana da yaren fulatanci"wanane kai? Daga ganin bakuwar fuskarka ba fulanin dajin mu bane" fuskar ta da murmushi tayi maganar tana nuna shi da sandar hannunta..... Bin ta da ido yayi don bai fahimci me tace masa ba. Tamkar bazai tanka mata ba yace"bana jin yaren da kikai min magana shi," waro mashi dara daran idanuwanta tayi, wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskarta, cike da mamaki yake kallon ta ganin tana ta murmushi, bakomai ne yasa ta farin ciki ba face jin yayi mata magana da yaren Angel dinta, yarinyar da ta kwallafa rai akan son ta. Bai yi tsammanin zatai mashi magana da hausa ba sai ji yai tace"Ya sunanka? Wanene kai? Me kake yi a rigar mu" dakyar ha usar ke fita irin ta an koyo. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bata amsa da cewa sunana tajudeen, bako ne a rigarku, ban jima da tsintar kaina a cikin ku ba," wani irin bugu taji kirjinta yayi mata, jin sunan daya ambata kamar ta ta6a jin sunan abakin angel, sai dai takasa tunawa Cigaba tayi da janshi da fira saboda Ya kwanta mata aranta, wunin ranar danejo tana atare da taj, ba laifi ta ebe mashi kewar dake damun shi, yawo suka dinga yi acikin dajin suna tafiya suna fira ka an ka an saboda rashin sabo, da kuma arancin hausar dake gareta, bakomai ne take fahimta ba. Tun daga ranar daya ha u da danejo, wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, kullum ne sai tazo kawo mashi abinci sau uku arana, wani lokacin gasassar masara zata kawo masu su zauna suna ci suna fira, har dai wata rana ta gayyace shi zuwa rigarsu, duk da ya nuna mata baisan zuwa, ro ansa ta dingayi hada sanya mashi kuka, a dole ya amince mata suka je rigarsu, tashin farko danginta suna ganin taj suka tada 6alli akan basa son ganin shi tare da ita, hankalin danejo ba karamin tashi yayi ba, jin zasu rabata da mutumin da take sa ran zai maye mata gurbin Angel, akan idonshi suka rufe ta da fada kamar zasu bugeta cikin harshen fulatanci inna wuro ke ta faman zazzaga masifa tana fadin ta manta gargadin da sukayi mata akan kada ta kuskura ta ara kawo masu wani a cikin rigarsu! So take ta kashe kanta saboda taimakon bare ne? Ko ta manta da irin wahalar da tasha bayan tafiyar yarinyar da ta walla rai akanta ne? Babban yayan su bawuro yace"tun wuri ta rabu dashi, idan ba so take su kashe shi ba" fashewa tayi da kuka hada bubbuga kafa tana fadin ita wallahi bazata rabu da shi ba, saboda zuciyarta ta kamu da kaunarshi," jin wannan maganar daga bakinta ba karamin fusata su yayi ba, Inna wuro tace"sai dai ta za6a ko su ko shi," abunka ga mai karancin hankali ga kuruciya dake damunta, da bu ar bakinta sai cewa tayi zata bishi, aikuwa a fusace bawuro ya kifa mata mari, da sauri taj ya dakatar da su ganin abun nasu na neman wuce gona da iri. Cikin kwantar da murya yace masu su yi hakuri, su daina bugunta indai saboda shi ne yanzu zai tafi yabar masu rigarsu" sam basu fahimci me yake cewa ba, sai ma wani irin kallon tsana da suke jifar shi da shi, har ya juya zai tafi danejo ta ru o hannunsa, a fusace gidado ya ru o hannunta, suka riketa don kada tabi shi. Sautin kukanta ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, shi kanshi baya son rabuwa da ita, ba don yaso ba sai don ba yadda zaiyi ne... Har yayi nisa da tafiya, ya an dakata zuciyarshi na raya mashi ya juya ya kalle ta, watakil bazai sake ha uwa da ita ba, har zuwa lokacin da zai bar dajin, Juyawar da zaiyi keda wuya, kwatsam idanunsa suka sauka akan rigar Angel dake shanye kan aya daga cikin bukkokin su, daga gani wanke ta akayi aka shanya don ta bushe, da farko bai tantance abunda idanunsa ke nuna masa ba, sai da ya an kara ura idanunsa tukunna Ya shaida itace rigar baccin da ke a jikin Angel aranar da ya gudo da ita, sune kayan jikin ta, was wasi yafara yi a cikin zuciyarsa tayaya akai rigar unaisah tazo dajin a hannun fulani? Ko dai suma suna da irin rigunan gayu ne"? Farat aya zuciyarshi ta bashi amsa da cewa me zai kawo irin wannan suturar a hannun mutanan da ke rayuwa a daji? Sai dai idan tsintar ta su kayi...' muryarshi na rawa ya furta"idan har dagaske