Sashe 29
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
da hanci suna kallon ikon Allah, hatta su Hajiya malikat da su sir mubatak mamakinne ya kamasu yadda ya rufe ido yana jan hajjaty da tsiya yake son fitar da ita daga hall din. Alhazawan canada suna ta kallon ikon Allah abu kamar a drama, anbarsu a duhu sun kasa gane meke faruwa... Tsawar da Sir mubarak Ya daka mashi ne yasa shi saurin shiga taitayinsa, A fadace yace"wannan wani irin shashanci ne? Baka da hankali ne? Ina ruwanka da ita? Tun da ta nuna batason tafiya ka yale ta mana!" Kallon hajjaty pravin yayi idanunshi jawur yana huci ya furta"idan har baki bini mun koma gida ba ranki zaiyi mugun 6aci, wlh kada ki bari na riga ki fita daga hall din nan" yana fadar hakan Ya juya tamkar mayunwacin zaki Ya nufi kofar fita hall din cike da sa ran hajjaty zata bi bayan shi, sai dai har ya fuce babu alamun zata bishi, kamar an ru afafuwanta, hakanan taji ba ta son tabi shi, taji kunyar abun da yayi mata, agaban jama'a, tasan dole adasa masu ayar tambaya, ita kanta a ru e take batasan dalilin dayasa pravin ya rikice mata ba, Hajiya saratu yau taga abunda yafi karfinta, tamkar a mafarki take ganin komai, akan idonta pravin ya ru e hannun hajjaty bainar jama'a batare da ya ji tsoronta ba, lallai zai fuskanci horo mai tsanani daga gare ta, har ta ita kanta hajjatyn yaja mata bala'e domin kuwa bazata yale ta ba, ransu twins su yayi mugun 6aci musamman zayn shi da yafi zuciya...... Bayan hatsaniyar ta lafa, senate lateef ya dubi su unaisah "tun da mahaifinmu ya yanke hukunci akan ku zauna, ba mu da ja, ya zamar mana wajibi mu tarbe ku, amma kafin nan ku sauke facemask dake akan fuskokin ku" ya fada yana nuna faces din su. Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su. "Kamar ka shiga zuciyata, nima abun da nakeso nace kenan, gaskiya ba zamu bari ku shiga da wannan face mask din ba, yakamata mu ga fuskokin ku," tun da aka fara rikicin nan sai yanzu his excellency abdul razak ya sanya baki, His excellency deen yace"to nima dai abu e min inga fuskokin nan, ko hankalina ya kwanta" ya fada da an murmushin kan fuskarsa. A hankali Batool ta aura yatsun hannunta da ke kerma ta ru o face mask din ta yaye shi daga kan fuskarta, Har saida gabansu ya fadi da ganin kyawun fuskarta, wato wani guntun murmushi da tayi ta sunnar da kanta kasa ba karamin tafiya yayi da imanin su ba, wasu tuni sun fara danasanin sanya su kuka da su ka yi. Bayan batool ta cire nata, Sajeed Ya zame face mask din fuskarshi, tsabar ki ima da ganin fuskarshi yasa hajiya laura an zaro idanunta ga dukkan alamu akwai wani abu da ya ru e ta da shi, kyawun sajeed ba aramin tafiya yai da imanin su ba. "Saura ku, Ku cure naku mu gani" Zaki ne ya fada yana nuna sauran Sajeed ne ya taimaka wurin Cire ma Azeeza nata, Duk tabi ta ame shi, fuskarta tayi sharkaf da hawaye har wani zazza6i ya lullu6e ta, ganin fuskar Azeeza ya yi matu ar razana Sir mubarak har sai da ya kalli fuskar Mom turai, ba shi ba, hatta Dr jazz da su Ibad kusan a lokaci aya suka jefa wa junansu kallon kallon mai nuni da tsantsar mamaki da al'ajabi. Jamimah dake a ma ale jikin angel, babu alamun zata motsa, ru o hannunta Angel tayi tare da cire mata mask dinta, fuskar ta 6aci da hawaye hada majina hakan yasa basu samu damar ganinta da kyau ba. Kusan atare Javed da Haris suka tu6e nasu face mask din, Kallon kallon aka komayi atsakanin Iyalan obinna kowa da abun da ya aure ma shi kan shi. "Parveen ku cure naku" cikin sanyin murya Unaisah tayi masu magana Batare da 6ata lokaci ba, Parveen ta cire nata mask din, wani irin bugu zuciyar hajiya saratu tayi, ha a ta razana da ganin kamannin ta dana yarinyar, har sun 6aci kamar tayi kakin ta, banbancin su launin fata, ba ita ba harta sauran matasan family din da iyayan mamakine tsantsa akan fuskokin su... Lokacin da Naufal ya cire mask din fuskar shi, wata irin firgita hajjaty tayi, har sai da ta dafe saitin zuciyarta da ke yi mata wani irin mahaukacin bugu, tagaza yarda da abun da idanuwanta suke gane mata, gani take tamkar mafarki ne ba gaske ba, domin kuwa ita dai tasan wanda ya mutu baya dawowa, harta su Hajiya Muhibbat sai da suka saci kallon fuskar hajjaty da ta naufal saboda wani abu daya ja hankalin su.... Gaba aya sun rikice Sun ru e, sun gaza gasgata abunda idanunsu ke nuna masu Tamkar an kulle masu baku nan su, Sun kasa magana, Lamarin ne yafi karfin tunanin mai tunani, mamakin su tayaya akai yaran suke bala'en kama da an family din su? _Ba zata juri bugun da zuciyarta ke yi mata ba, da azalzalarta akan son ganin fuskar yaron da hateem ya kwallafa rai akanshi, tabbas tana son ganin shi, kowa na gurin burin shi Danish ya cire mask din fuskar shi, sunyi matu agara da son ganin sa, walking gently gimbiya mujeedat ta tako ta tsaya gab da inda danish yake atsaya kamar mai wani nazari abu akanshi, idanunshi na kallon kasa sam bayason hada ido da kowa_ Sanya hannu tayi ta cire mask din dake akan fuskar shi............ Kiris ya raga zuciyar gimbiya mujeeda ta daina bugawa saboda razanar da tayi, gaba aya hankulan su ya dawo kan shi, Wani irin mugun bugu zukatan su suka soma yi, yadda kasan ana dakan sakwara, Gaba aya suka zazzare idanunsu gami da bu e bakunansu saboda tsabar ki ima kamar sun ga wani mugun abu, wato Sun gigita sun razana da ganin wanan abin al'ajabi da yai matu aga hankulan su, Afirgice Chief Of Staff Na canada Ya dubi fuskar Security Advisor da wani irin ru ani akan fuskokin su, at same time su ka yi saurin kallon Prime minister Hateem, Baba obie kuwa kusan suman tsaye yayi da ganin wannan Kama ta ban al'jabi, Senate lafeef da su His excellency sai faman jinjina kan su suke yi sam sun gaza magana kamar kurame, sai yanzu suka gane dalilin dayasa hateem ya firgice ma su da kaunar yaron ashe shi yasan abun da ya gani, Kai kowama dake a wurin ya rasa lissafin kwalwarsa saboda ganin fuskar Danish, Wai shin Ina Nazli? Ay tun da tayi tozali da danish tsabar firgici da ru ani yasa har batasan sa'adda ta saki wayar hannunta ba, gaba aya ta kife kan flloor, Jikinta ya kama kerma kerma tana faman zazzare eyes din ta akan fuskar shi yadda kasan twin brother din ta. saboda ru u tunani su ka yi ko dai Nazli ce ta koma inda danish yake atsaye hakanne yasa sukayi Saurin kai idonsu inda take atsaye don suga idan tana nan, Ganinta yasa suka ara rikicewa. Security adivisor ya kasa samun nutsuwa saboda al'ajabin da ya kama shi, Muryar shi na rawa rawa yana tangyadi cikin harshen turan ci yace" dama prime minister yana da wani ane da ba mu san da shi ba, ko kuwa aninsa ne? Ko dai giyar dana sha ce takai mun karo? Pls ku yi min bayani yadda zan fahimta. Senate lateef ne ya bashi amsa da cewa"ba su ha a ala ar komai ba, kama ce kawai" babu alamun za su gasgata maganar shi. "Abun da aure kai, amma ya ya akai su ke bala'in kama har haka? Kamar an yi photo copy din fuskar Hateem, ko ma ince Nazli" his exellency Deen ne yayi maganar, Yazrin sam takasa samun nutsuwa Sai kallon shi take yi ko yaftawa babu, wato danish ya girgiza su da kyawun shi, Hankulan su Faryat ya tashi haikam tsabar yadda su ke kallon shi kamar za su ha iye shi, yadda kasan irin kura taga naman nan. a sun rudu da prisoners, babu wanda bai yi mamakin sanyin kyan su ba, da al'ajabin kamanceceniyar su da an uwan su yadda kasan ya'yan cikin wasu daga cikin su tsabar yadda kamannin su ya bayyana da juna... Ganin kallon nasu ba mai arewa ba ne gashi sunbar yara atsaitsaye, da sauri Ziyad ya ce "Lokaci yana tafiya, yakamata acigaba da shagali" kafin Ya are maganar sautin wa a mai ratsa zuciya ya kara e cikin hall din, aya bayan aya Suka juya suna nufar wurin zaman su kowa da abun da yake sa awa a cikin zuciyar shi. Hateem kamar jira yake yi a samu maslaha, jiki na rawa ya nufi danish ya ru o hannun shi acikin nashi, burin shi su ha a ido don su kalli juna dakyau amma ya i bashi damar hakan, murmushi ne dauke akan fuskar sharafudeen sai faman kallon su ya ke yi, yaji dadin ganin hateem a irin wannan yanayin. Da zolaya yace irin wannan kallo haka? Ka da fa ka lashe mana yaro" ar dariya hateem yayi, Chief owais da ke kallon su ba karamin kwanciyar hankali ya samu ba ganin ya faranta ran uncle din sa "Uncle ka tafi da shi, zaman shi anan bazai yiwu ba, saboda baya son hayaniya, kuma baya son ana kallon sa, From now until nightfall, I entrust him to your care" wani irin farin ciki ne ya ara lullu6e prime minister, kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, cikin sanyin murya yake fadin"nagode owais, wlh ka gama min komai, bazan ta6a manta alkhairin ka a gare ni ba, Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" addu'o'i ya dinga zuba mashi, bai manta da sheikh imam ba wanda ke atsaye tun dazu murmushine akan fuskar shi. "shukran jazeelan Ya sheikh, Allah ne kadai zai iya biyan ka, saboda babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani da su wurin yi maka godiya" ya fa a yana ru o hannun sheikh imam gaba aya wani irin annurin farin ciki ne akan fuskokin su. Unaisah da ke ta sauraron su aranta Allah Allah take Danish ya amince da bu atar chief yabi prime minister don tasan halin shi da kafiya ba kowa ke iya tankwara shi