Sashe 108
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
hannu suka gaisa.. Fitowa hajiya Layla tayi daga dakin jikinta a sanye da hijabi bakinta washe ta fara gaishe da su, suka yi mata ya mai jiki ta amsa masu. tunda Taj Ya kalleta sau aya ya kau da idon shi gefe, ba zai ta6a mantawa da irin wula ancin da Hajiya Layla tayi mashi ba, hakanan ta aura mashi karan tsana saboda yana son yarta, har fa i take in banda ha ama irin na an talaka ina shi ina Benazir? waye ubansa a kasar? Da aikin Jarida zai ciyar da ita? "Wama ya sani ko asiri kayi mata shiyasa ta nace saita aureka .." murmushin takaici ya saki ta cikin face mask insa..., Dr Adam Ya ce, "ina yarinyar ne?" da yake basu lura da ita ba duk ta takure bayan Anila kamar tana jin tsoron wani abu, "Azeezaty, zo nan mana" Biy guy ne ya kira sunanta, fitowa tayi idanunta na kallon asa ta tsaya a tsakiyar su, gaba aya ta tsargu da kallon da su ke yi mata, Hajiya Layla ta kasa rufe bakin ta saboda mamakin ganin yarinyar, sai taga kamar sunyi kama da Benazir inta, sai lokacin Dr Jazz ya lura da ita sun an ru e da kyawunta, musamman Dr. Adam har dai ya gaza jurewa ya ce "Tabarakallahu ahsanul khalikin..." bai are maganar ba, Dr jazz ya yi saurin yi mashi ra a a kunne"kallon ya isa haka! Future wife in babban yayanmu ce, wlh ka shiga taitayinka" da sauri Dr Adam ya rufe bakin shi da tafin hannu. "Azeezaty, ina fata anyi maki bayanin abunda ya kawo ki nan?" aga mashi kai tayi alamar eh, "Okey, abunda muke so kaitsaye ki shiga akin wurin patient in, ki yi hugging in ta sannan ki kirata da sunan Mommynki" amsa mashi tayi da toh, kafin slowly ta juya ta nufi akin zuciyarta na dakan uku uku wani irin fa uwar gaba take ji, gaba aya sun nutsu suna kallon ta... Duk taku aya idan tayi sai gaban ta ya fa i rass, ta rasa gane dalilin shigarta yanayin da take a ciki. Tunda ta zura afarta a akin idanunta suka sauka akan mara lafiyan dake a kwance tana bacci, walking slowly ta arasa ta tsaya daga bakin gadon tana kallon ta, tun daga kan fararen kafafuwanta har zuwa kan fuskarta, sumar kanta ta lullu6e gefen fuskarta daga gani ba aramin hauka tayi ba kafin a samu ta runtsa. Wata irin kasala ce ta baibaye Unaisah gaba aya ta kasa ta6uka komai sai kallonta takeyi kamar zata ha iyeta..... "Ki rungumeta mana, ke muke jira" asa asa da murya Dr Adam ya furta maganar, Numfashi ta ja kafin ta daidaita nutsuwarta, a hankali ta zauna daga gefen gadon kafin ta fa a kan irjinta tare da lumshe idanunta lokaci aya ta fashe da matsanancin kuka me sautin gaske ita kanta batasan kukan Ya kubce mata ba, hankalinsu ba aramin tashi ya yi ba amma sai suka yi zaton tayi ne don abun ya tafi dai dai.. Sautin kukanta ne Ya daki kunnan Benazir, cikin magagin bacci ta fara sambatu tana fa in "Babyna, wayyo Allah mami! ina babyna naji sautin kukan ta, don Allah ku kawo mini ita..." yatsun hannunta na kerma ta aura su kan bayan Unaisah, da dukan hannayenta biyu ta fara shafa bayanta taji mutun akan cikin ta, hakan yasa ta fara kokarin bu e idanunta, da yar ta bu e su sun ka a jawur saboda bacci, Daga can waje Dr Adam ya ce "Nayi mamakin farkawarta, because bana tunanin allurar da nayi mata ta isa ta saketa..." Su Anila duk sun agara Benazir ta karasa farkawa, gaba aya jikinsu sai tsuma yake yi ga wani irin annurin farin ciki da ya wanke zukatansu, Mayafin kan Unaisah tuni ya jima da zamewa, hakan yaba Benazir damar cusa hannayenta acikin sumar kanta ta cigaba da sambatu tana fa in "Babyna ne? Mami daddy kuna ina? Wanene Ya kawo min babyna? meyasa take kuka?" Sosai Unaisah ta ameta, ta ara cusa kanta a kirjin Benazir babu alamun zata saketa, Allah sarki jini aya ba wasa ba, wannan unconditional love in dake atsakanin uwa da anta shine yayi tasiri a zukatansu, a karo na farko da ta fara jin umin mahaifiyarta ba tare da sanin itace ba, aru e Benazir ta zabura ta ago da fuskarta ta ura mata ido tana kallonta, baiwar Allah Angel fuskarta tayi jawur da ita ruwan hawaye ya wanketa tass, da yar take bu e idanu tana kallon cikin idon Benazir, kallon kallo suka fara jefawa junansu duk hawayen Unaisah sun wanke fuskar Benazir, la66anta na kerma irjinta na bugawa ta furta "Mamana! Ni ce babyn ki, meyasa kika tafi kika barni? kin manta dani a rayuwarki? Nayi kukan rashin ki atare dani mamana!" Shigowa akin Hajiya Layla tayi daga bakin gadon ta tsaya tana kallonsu, walla sun taru acikin idanunta, "Mommy ki fa amin? Da gaske babyna ne nake gani ba mafarki nake ba? Angel ina ne?" Kwata-kwata Angel bata fahimci sambatun Benazir ba saboda ita kanta ta an shiga ru anin halin da ta tsinci kanta game da matar, "Benazir, yarinyar ki ce Angel, ki rungume ta a jikin ki, " Hajiya layla ta fa a da murmushi akan fuskarta, fashewa da kuka Benazir tayi, da sauri ta kwantar da Unaisah kan kirjinta ta rungumeta sosai kamar zata mayar da ita cikin cikin ta. Cikin shesshekar kuka take lallashin ta"kiyi shiru ki daina kuka, bana son ji, nasan nice na 6ata maki rai, kiyi hakuri ki yafe min bazan ara tafiya in barki ba, nayi maki alkawarin zan baki kulawa babyna, kinji my Angel"? Sambatu taci gaba da yi ta i bari Unaisah ta ago da kanta ta ame abun ta kamar wani yace zai kwace mata ita..... Jikin Taj ba aramin sanyi yayi ba, da sauri ya du ar da kan shi hawaye sun cika idanunshi, sai yaji inama ace zai iya zuwa ya ha a su duka a kirjinshi ya rungumesu, Zahra sarkin tausayi tuni ta fara matse walla, ita kanta Aneleerh kukan ne ya kusa kubce mata, da hannu biyu ta toshe bakin ta don bata son ayi zargin ko yarta ce ta gaske, Lumshe ido Chief ya yi a yayin da yake kallon su, ya jima baiga abun farin cikin da ya sanyaya zuciyarshi ba irin na yau! abun ya ta6a zuciyar shi.... Hatta Docs in dake a tare da su saida suka ji tsananin tausayinsu, A hankali Dr shureim Ya zaro hanky daga aljihu Ya share kwallar da suka tarar masa, yana ji aransa da wuya yarinyar in ba jinin su bace!! Dr Adam ne ya sauke yar ajiyar zuciya ya ce "in sha Allah zata samu sau i, naga alamun nasara tun kan aje ko'ina, Yarinyar ba aramin wayau ne da ita ba, ta iya acting,..." kallon shi kawai Anila tayi su da suka san meke atsakanin su.. Dr jazz ma ya ce "Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah yasa yarinyar nan ta zama silar warakarta" gaba aya suka amsa mashi da ameen.... "Yalla6ai, muje office mu arasa magana" Dr. Jidenna ne Yayi maganar, atare da Chief suka nufi katafaren office dinsa.Tattaunawa suka yi dangane da Unaisah, Chief ya ce masa baya son kowa ya sake shiga akin mara lafiyan daga grandma inta sai Unaisah, bayan haka Yana so a canza mata aki su maida ta private room saboda Unaisah ta samu damar sakewa wurin yin jinyarta, ya aura da fa in "Bana bu atar wani likita ya shiga dakin ta in ba Dr Jazz ba, shi nake so ya cigaba da kula da mara lafiyan" Dr Jidenna ya ce "Consider it done sir, in sha Allah a cikin daren nan zamu aiwatar da komai" sun jima suna tattaunawa a office din kafin daga bisani suka fito a tare, har lokacin su Shureim suna a tsaye bakin kofar dakin suna kallon su Benazir, Bayan sun dawo wurinsu chief Yaja hannun Dr Jazz suka ke6e wuri aya dama shi mutuminsa ne, Yana jin dadin aiki da jazz yaron yana da hankali, "Jazz, nayi magana da Md, kaine zaka cigaba da kula da mara lafiyan! Pls bana so asamu matsala!" murmushi jazz yayi "In sha Allah babban yaya zanyi kokari sosai gurin basu kulawa," "Good, sannan inaso ka duba jikin yarinyar, ta fa amun bata jin dadi, pls inaso ka bata kulawa ta musamman, bana so ta nemi wani abu ta rasa! Kayi kokarin kwantar mata da hankalinta kamar akwai abunda ke damunta" Jinjina kai jazz ya yi "In sha Allah My Boss, kasan bana wasa da duk wani abu da ya shafe ka" harara Chief ya an watsa mashi, ya sunnar dakai asa yana murmushi... o hannunsa chief yayi suka koma wurinsu Taj, Duba agogo big guy ya yi "Yakamata mu tafi dare yayi, almost 12," Da sauri Anila ta ce "pls muna son muyi mata bankwana kafin mu tafi" Dr Adam ya furta "Okey, bari na kira maku ita" shiga dakin yayi, "Azeezaty yan uwanki suna son ganinki zasu tafi, ki fito kuyi sallama" shiru yaji bata amsa mashi ba, le a fuskokinsu yayi abun mamaki bacci ne ya aukesu rungume da juna bayan sun gama shan kukan, gaba daya Unaisah tana kwance kan jikin Benazir shiyasa gadon ya dauke su.... Fitowa Dr Adam ya yi fuskarsa auke da murmushi ya ce "sai dai kuyi hakuri bacci suke yi, ba zamu iya tada su ba" "Dr ga backpack in kayanta, ka shigar mata da ita ciki" sauke jakar Taj ya yi tare da mi a ma Dr Adam ya shiga da ita ciki ya aurata kan kujerar gaban gadon. Kamar kar su tafi haka suka dinga kallon su ta cikin door glass in, kafin daga bisani suka kama hanyar barin asibitin, har bakin parking space Hajiya Layla ta rakasu tana ta faman yi masu godiya kamar zata du asa, shima Dr. Shureim godiya sosai ya yi masu tare da fatan alkhairi, sallama sukayi wa junansu Zahra da Anila suka shiga motarsu, Taj da Big guy suka shiga tasu motar, kafin Chief ya shiga motarshi, saida Hajiya Layla ta ara yi masu Anila godiya saboda halaccin da su ka yi masu kafin motocin suka fuce a jere da matsakaicin gudu, ya