Sashe 204
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ta bu e kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ru e qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum. "Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata ha o min wani kuma ma zata dafa min noodles..." "Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta auki junaid ta shiga toilet da shi. da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dau e da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet. Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa. Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido.. "Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya? "Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou" "Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon. "Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta fa a tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne? Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya "In sha Allah next week zai koma" Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafa i a duniya Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci. sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da le a fuskar ta, gabanta ne ya fa i ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun ka a jawur. Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba. Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ru e zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta.. "Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake" dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..." murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gya a kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late" "Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin. Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa" "Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin.. Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su. tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya wama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar aramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matu ar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a. Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane. "Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sau i ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi" "Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma" Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya ha e fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai auke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..." a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle aya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su ago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"? Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa. Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"? Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata. A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu. Tsaye take a gaban dressing mirror tana an jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da ha uwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, an light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, dadda amshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar akin da wani irin kamshi mai dadin shaka. Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan. Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran arasowarka my lovely husbad" ta fa a tana yar dariya. High heels ta auko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan. *HAJIYA SARATU* Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta. Iphone dinta dake ajiye saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"? "Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta mi e fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya. Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..." bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"? "Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba" "Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"? "Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"? e rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"? sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport" "Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama. Saukowa tay daga gadon tana uni kan maganar gyara da baba obie yai mata. "Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta arashe kukunin tare da bude toilet door ta shige. Lokacin da ta araso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa. Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi. Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu. "Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa" Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama"