Sashe 91
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
tunanin tarko ne za'a ana masu!? in ba haka ba tayaya matsafiya wadda take rayuwa acikin gidan kurkukun kaddara zata neme sa da sunan bashi gudummuwar tarwatsa kurkukun addara Knocking kofar room dinsa akai da sauri Ya daidaita nutsuwarsa kamar wani abu bai ta6a faruwa ba... Yayi zaton unaisah ce sai da yaje gaban kofar ya bu e karaf idanunsa suka sauka akan chief owais Ya auki wanka cikin shiga ta kakinsa Yayi shirin zuwa Office, from head to toe Ya kalle sa kafin Ya ha e fuskarsa bakomai Ya tuna ba face unaisah da ya gani adakinsa jiya shiyasa ya arajin haushin mutumin Chief owais baibi takansa ba Ya nufi cikin dakin hannunsa ru e da shopping bag, Ya dire masa ita kan gadon shi A hankali Ya juyo suka fuskanci Juna "Ba ka Iya gaisuwa ba ne"? wani an iskan kallo danish Yayi masa Murmushin gefen fuska chief Yai "Laifin me na maka kamar baka kaunar gani na"? Shiru yayi bai tanka masa ba Da ace chief yasan unaisah ce Silar dayasa danish Yake ha e masa rai ay da tuni Yayi masa bayanin da zai kwantar masa da hankalinsa don shi A yanzu mace bata agabansa, burinsa ya gano miyagun gidan kurkukun addara da kuma kawo karshen su shi ne abunda Yasa agaba kallon shoppin bag din yai alamar yana neman arin bayani yaga bakon abu adakin sa "It's a gift from Uncle Hateem. Please don't break them they're not toys," he said jokingly. tare da bu e jakar ya soma fiddo da kayan cikin ta "suna da amfani, idan ka bani dama zan nuna maka yarda zakai amfani da su" cikin lallami yakeyi mashi magana Ganin Yayi tsaye Yaki matsowa Ya duba kayan, Yasa chief Tunkararsa Ya ru o hannunsa Ya janyo shi har bakin gadon "Zuwa anjima zan ware mana lokaci in fara koya maka Yadda zakai amfani da su ko baka so"? Yai maganar Yana dubansa sai wani shan mur Yake. Daurewa kawai cheif yakeyi amma fa ya fara hasala da halin danish kwata kwata baya sakar masa fuska kuma Ya i magana da shi, in banda ma Yana neman alfarma awurinsa ay da bai kai matsayin da chief zai kulasa ba Fucewa yai daga dakin Ya Bar danish a tsaye Ya kasa ta6uka komai, zuciyarsa har yanzu bata daina ambaton sunan jeremiah ba, kalaman tsohuwa Khala sun tsaya masa aransa sai yake ganin kamar amafarki ta bayyana.. zama yayi gefen gadon Ya zubawa kayan ido har cikin rashi Yaji dadin jin cewa Hateem ne Ya bashi kyautarsu, duk da baisan amfaninsu ba amma sunyi mashi kyau, bai ta6a ko aya ba, ya yanke shawarar sai unaisah tazo zasu bu e su atare ________________________________ *ANEELERH* "Mu tafi asibitin kawai, bazan Iya jurewa ba...." gani take kamar zata rasa benazir, shiyasa ta hakura da shiga estate din Su mahoob daman hanyar da zasu tafi suke nema, jiki na 6ari Ya bu e motar Ya zauna a driver's seat, Aneelerh ta shiga ciki, Zahra na kokarin shiga kwatsam ta hango dankareriyar motar dake tunkaro estate din dakatawa tayi saboda ranta na bata cewar Motar Hajiya saratu ce.... "zahra ke muke jira ki shigo mu tafi" acewar mahboob an jira, naga kamar motar Hajiya saratu ce ke tunkaro estate din..." jin wannan maganar yasa Aneelerh yin hanzarin fitowa daga motar shima mahboob Ya fito duk suka urawa motar ido cike da sa ran ganin wanene a cikin ta Lokacin da motar ta kusa arasowa dab da inda suke gudunta ya ragu slowly window glass dinta na back seat Ya zuge hakan Ya basu damar ganin na cikinta Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya zahra ta sauke mai ha e da annurin farin ciki Ita kanta Aneelarh ajiyar zuciyar ta sauke haka shima mahboob duk da basu ta6a ganinta ba Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta ido da ido A hakimce take zaune cikin motar, ta auki wankan lafaya, idanunsa na a manne da farin glass ba karamin kyau yayi mata ba Da alama su take kallo, Umarni ta ba security din dake driving dinta idan sun karasa kusa da motar su zahra yai parking, ya amsa mata da toh Daga bayan motarsu zahra yayi parking din motar, jiki na 6ari zahra ta nufe ta, a lokacin ta bude car door din ta zuro kafarta aya waje Sallama tayi mata cikin girmamawa tace"sannu da zuwa mommy, ya gajiyar aiki...." Fuskarta da fara'a ta furta"lafiyalou daughter, zuwan bazata akai mana? Amma ya akai naganku a waje..." Zahra kamar zatai mata sujjada tsabar yadda take magana cikin ladabi da biyayya "Masu tsaron gate din ne suka hana mu shiga sunce dole sai an basu izni, har layinki na kira baya shiga nasan kin shiga busy ne..." "Eyyah! Na sanya wayar a silent lokacin da zan shiga meeting...' tai maganar tare da kai dubanta ga su aneelerh"su wanene? Ina fata dai lafiya? Ta fada cike da son jin karin bayani "Auntyna ne da anina mahboob, wani abune mai mahimmanci Ya kawo mu .." da sauri Aneelerh da mahboob suka karaso bakin motar hajiya saratu cikin girmamawa suka gaishe da ita, fuskarta asake ta amsa masu wato sunci albarkacin zahra shiyasa ta sakar masu fuska "Pls kuyi hakuri sun shanya ku arana, Yanzu ku shiga motar, mu tafi. " wani irin dadi Ya lullu6e su, da sauri suka nufi motarsu, bayan sun shiga a jere motocin suka nufi cikin estate din babu wanda yayi gigin dakatar da su cikin securities din sai ma gaisuwar da suke mika ma hajiya saratu wadda ko kallo basu ishe ta ba. Bayan sunyi parking, kowan nan su Ya fito, Aneelerh sai faman satar kallon katafaren estate din takeyi kamar a dubai, Inaga mahboob wanda Yake ta jinjina kai aranshi Yace"Wai dama haka daular obie estate take? Gari guda, Tab ijan Daga gani anyi almubazzaranci wurin ginasa, Mutane kamar bazasu mutu subar duniya ba? Yo ni Allahna na tuna ko amafarki ban ta6a ganin katon gini irin wannan ba! Kai jama'a..sai faman santi yakeyi acikin ranshi Gaba hajiya saratu tayi da sauri suka bi bayanta, zahra hada kar6ar handbag dinta ta ru e mata ita, irin fadancin nan Ashe mahbbob baiga komai ba, suna shiga falon kiris Ya rage ya zabga salati saboda ganin makurar kayan alatun da aka baje ta ko'ina...har wani zazzabi yake ji ajikin shi Ga masu aiki dake kai komo cikin uniform "Bismillah ku zauna, Ku an bani mintina ka an, Yanzu zan fito..' amsa mata sukai da toh, ta nufi daki zahra tabi bayanta don ta kai mata handbag dinta.. Ya rage saura mahboob da Aneelerh, zama sukai akan tamfatsa tamfatsan royal sofa din falon... "Karshen duniya yazo aunty aneelerh" ya fa a yana kishingi a bayansa jikin sofa, duk da halin damuwar da Aneelerh take aciki sai da an murmusa jin abunda Mahboob Yace, ita kanta ta girgiza da ganin katafaren ginin "Alhamdulillah Ya Allah.."ta furta aranta"Ya Allah kamar Yadda ka bamu ikon shiga gidan nan lafiya, Ya Allah ka bamu ikon ganin Yarinyar nan cikin sa'a ba tare da mun sha wahala ba" har cikin ranta wani irin sanyi takeji, fatanta Allah Yasa su dace Kallon mahbbob tayi wanda ke ta bin ko'ina da kallo baki asake kamar lehen sakarai "Mahboob! Pls kaja aji mana, kada kai mana kauyanci, duk fa abinda suke da shi mu ma muna shi agida...." tashin Farko Ya ce"muna da lifter..? murmushi aneelerh tayi"a'a amma ai akwai stairs ko"? Girgiza kai yai"ba irin wannan ba duba fa kiga ni har hawa uku, ga yan aiki ta ko'ina..." murmushi tayi tana kallon shi" nifa aunty aneelerh bawai kyawun gidanne Ya ru e ni ba, no kawai almubazzarancin da akai wurin ginasa shiyafi komai 6ata min rai, Allah ba karamin mai imani bane zai zauna agidan nan kuma yaci gaba da yin sallah..." yar dariya Aneelerh tayi Kafin wani Ya ara magana sofia ta nufo wurinsu hannunta ru e da tray na cool drinks tare da snack ta ajiye masu kan table "Inayi maku barka da zuwa" amsa mata sukai da yawwa "Hajiya saratu ce, ta bada umarnin akawo maku drinks, idan akwai abun da kuke bukata ku sanar dani..." har suna ha a baki furta"a'a mungode, Bayan ta bar wurin Mahboob Yace"munci darajar Zahra wlh da ko kallo bamu ishi matar can ba, daga ganin ta zatai ji da kai..." Bayan wasu an mintuna, Hajiya saratu ta fito har ta canza kayan jikin ta, wata hadaddiyar abayace ta sanya, zahra na abiye da bayanta har suka karaso, zama tayi kan sofa tana fuskantarsu, itama zahra ta zauna. ara gaisawa sukayi kafin ta ce"Zahra ta fa a min abune mai mahimmanci Ya kawo ku! ina sauraronku..." cike da dattako tayi maganar. Gyara zama Aneelerh tayi cikin nutsastsiyar muryarta ta fara kora mata jawabin abun da Ya kawo su... bayan ta kammala hajiya saratu tayi jimm na an wani lokaci kafin ta dubeta"kun tabbata Yarinyar ce? Shiru sukayi ta kuma cewa" Bana so asamu matsala! Ba ku tunanin ko mai kama da ita ce..."? Duk da warjinin da hajiya saratu tay wa aneelerh hakan bai hanata Yin karfin halin furta"muna sa ran itace, saboda ni tamkar uwa nake agareta, Yau shekara shida zuwa bakwai da 6atanta kamar Yadda na fada maki, kuma sunan yarinyar Unasah kamar yadda itama yarinyar da shi owais din yake ru o sunanta unaisah, amma muna kiran ta da Angel sunan da daddynta Ya sanya mata..." da kwarin gwiwa Aneelerh tayi maganar don ji take zata iya komai akan yarinyar nan Numfasawa hajiya saratu tayi abunka ga mace mai izza, bata son abunda zai jawo raini tsakaninta da chief gani take kamar zubda girmane ta nemi alfarma awurinsa shiyasa take jinjinawa lamarin da suka zo mata shi, duk da tana son taimaka masu. "Ina hoton Yarinyar, Ina son ganin shi" cikin sauri zahra ta bu e mata hoton awaya ta mu a mata. Bayan ta kar6a ta kurawa hoton ido nan take ta gane fuskar yarinyar cikin yaran da owais yazo da su wurin dinner..... "Ina hoton ita Yarinyar ta wurin ku"? Ta fa a tana kallon Aneeelerh, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin saurin curo wayarta daga cikin handbag ta bu e hoton Angel ta yunkura taje gaban hajiya saratu ta