Sashe 12
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
jarabtar, Idan kaji na wani kai naka ba komai ba, shiyasa a koda yaushe akeson bawa ya zamanto mai hakuri dakai zuciya nesa, ha a ina tausayin wadannan bayin Allah, duk da ban kaiga jin tarihin rayuwarsu ba... ' murmushi taj ya anyi tare da cewa"kada ki damu, nan badajimawa ba zaki ji tarihin rayuwarsu, In sha Allah" a kai tayi "A ina za'ayi dinner din sannan arfe nawa ne zasu je can din"? "A cikin Estate din nan, Bayan sallar la'asar" Shiru tayi alamar tana nazarin wani abu, yayin da yake binta da kallo. "Menene dress code din da za'a sanya a wurin dinner din"? ta tambaya tana kallon fuskarsa. "abaya matan za su sanya, A cikin suturunsu mun sanya masu abaya na larabawa kala kala, A ciki za'a daukar masu masu kyau na mutunci, sannan bama son suyi shigar da zata baiyana sumar kansu, a rufe masu ko'ina na jikin su. a kai tayi"okey, in sha Allah amma baza'ay masu make up ba"? "Duk kyan da Allah yayi masu"? Ya fa a da murmushi kan fuskanshi, Itama ummin murmushin takeyi"masu kyaun ma su na yin make up, ko da yake naji ka ce arufe masu ko'ina na jikin su, ba bu atar yin make up, aga mata gira yai alamar eh. "Tare da ni zaku tafi ne"? "Idan kina ra'ayin zuwa" Girgiza kai tayi alamar a'a "Meyasa"? "Nafi so kubarni a gida, nasan Su Unaisah zasu bani labari, har ma su daukar min video na dinner din in gani nima" "Ban yarda ba, yakamata kema ki shirya mu tafi tare dake, zaki ji dadin shiga cikin family in Obinna," jim ta anyi tana wani tunani aranta. "Kinyi shiru baki ce komai ba" Numfasawa tayi tare da cewa"ka yi hakuri amma zuwana ba lallai ya zama alkhairi agare ni da ku kan ku ba, bana so na 6ata maku shagalin ku, nasan ka fahimce ni" jim ya anyi yana jujjuya mug din hannunsa, tabbas ya fahimci me take nufi,shi kanshi yasan ba lallai chief Ya amince su tafi da ita ba, yadai an bugi cikinta ne don yaji idan tana son zuwa sai kuma akaci sa'a bata ra'ayi. "Alfarmar da nake nema a wurin ku, dan Allah ku barni in fita gobe, Inaso zan ziyarci gidan awata dake aure anan abuja" "Bani da wannan hurumin, Amma in sha Allah zanyi kokarin nema maki alfarma wurin chief, but inaso kisan da sani duk inda zaki je jami'in mu ne zai ka i ki," har cikin ranta taji dadin maganarsa. "Idan akwai abun da kike bu ata ki fa a min" cikin kulawa yayi mata maganar yana dubanta. "Dan Allah ka fadamin shin dagaske ne chief Yasan komai dangane da rayuwana"? Ta fada cike da fargaba. Jim ya anyi yana dubanta kafin Yace" "I'll give you an assignment. If you can find the answer, then I'll tell you what you want to hear," A agare ta ke kallon shi, A hankali Ya sanya yatsun hannayen shi tare da zame mask din fuskarshi. Wani irin kallo ummi ta soma binshi da shi, Yau ne karo na farko da ta fara Yin tozali da fuskar Boss man, bata ta6a tsammanin Yana da kyawun fuska har haka ba. "Dama haka kake da kyau"? da alamun mamaki ta furta maganar, Murmushin gefen fuska Ya sakar mata har dimple dinsa ya lotsa, nan take ta soma kokarin tariyo inda tasan fuskarshi sai dai kash takasa tunawa amma tabbas tana ji aranta ta ta6a sanin shi ko kuma wani ne me kama da shi. "Ina da aure, Ki daina kallona, matana tana da kishi, zata iya yin komai akaina" da zolaya taj yayi maganar. Ummi tace"tasan tana da kishi meyasa ta auri namiji mai kyan sura? Ay kamata yayi ta auri mummuna, ni fa bazan 6oye maka ba, ka jima kana bani mamaki kai da abokin aikin ka big guy da chief din ku, tun da nataso rayuwata da wuya a samu namijin zan gifta awuri batare daya bi ni da kallo ba harma ya neme ni, amma ku sam babu wannan tunanin aranku, zuciyarki a tsarkake take, hakan ba karamin daure min kai yake yi ba, shi chief mace ko kallo ma bata ishe shi ba, wata irin dakakkar zuciya ce da shi. ayataccen Murmushi Taj Ya sakar mata batare daya furta mata ala ba "Wallahi nasan ka, sai dai bazan Iya tuna a ina nasan ka ba, ni hatta muryarka na jima ina son tuna ina na son ta," still face dinsa da murmushi Yake dubanta. "Amma meyasa kake yi min kama da Unaisah? Ko dai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba"? "Ba laifin idanuwanki bane, Unaisah ata ce, Jini na ce, Ni mahaifinta ne, asalin sunana Tajuddeeen," "I can't believe it, Unaisa fara ce zan iya sanyata a jinsin larabawa, kai kuma daga ganin ka hausa fulani ne" "A salin sunana Zaheer Tajudeen, Zaheer sunan Mahaifina ne, Tajudden kuma sunana ne, Ki tambayi Unaisah menene full name dinta zata fada maki da bakinta, Ita kanta ayanzu haka batasan cewa Ni mahaifinta bane addara ce ta rabamu, sai gashi cikin ikon Allah mun sake ha uwa," murmushi ummi tayi"Allah sarki, Na tayaka Murna, amma mahaifiyarta wani jinsi ce"? "Hausa Arab ce" Dariya Ummi tayi cikin raha ta furta"hausa arab! Bayan hausa fulani har Hausa rab ke da akwai, ban ta6a ji ba sai akanka" "Ina nufin Half cast ce, Mahaifinta hausa fulani ne, mahaifiyarta kuma Balarabi ce" gya a kai tayi"masha Allah, shiyasa yarinyar taka takasance fara sol, Ga gashi tubarkalla amma tsakanin kai da mahaifiyarta halin wa ta auko"? murmushi yasaki yana dubanta yace"meyasa kika tambaye ni"? "Unaisah tana da fa a, daga ka kalli idanunta zaka shaidan hakan, ga wayau da kaifin basiri Allah Ya bata fiye da sauran an uwanta" ha a Yaji da in Yabon da ummi tayi mata, "Haka mutane suke cewa, shiyasa nima nake alfahari da ita, Inason Unaisah, fiye da yadda nakeson kaina, A halin Yanzu bani da tamkarta a duniyarnan, Itace ta rage min wadda nake gani naji sanyi araina, silar unaisah nasamu alheri da dama wadanda idan na fada maki su zakiyi mamaki, aya daga ciki Unaisah itace silar ha uwana da Chief" da mamaki Ummi ta an zaro mashi sexy idanunta ha i da bu e baki, Jinjina mata kai yayi" Murmushin gefen fuska tasaki"Ina ara tayaka murna, Yarinyarka Jarinka ce, Allah Ya albarkaci Rayuwarta" amsa mata yayi ameen, daga ita har shi sun ji da in zaman firar da su kayi, Ha a taj ya ebe mata kewar ka aicin dake damunta, ta ara ganin mutuncinsa da imarsa a idanunta, Sai dai tarasa gane meyasa take jin kamar ta ta6a sanin shi? Musamman daya fa a mata sunan shi sai yawo yake mata akai. Ni'imtacciyar Iskar dake ka awa ta ara masu aimin firar ta su, kafin wani lokaci taj yace da ita"kada na cika ki da surutu, ko zaki koma ciki ne"? Fuskarta da fara'a tace"no ko kusa, ni baka takuramin ba, saima ebe min kewar da ka yi, naji dadi fiye da tunanin...... " bata arasa maganarba sakamakon sautin dirar motar daya ratsa kunnuwanta, kusan atare suka juyo suna duban motar. Bayan sojan dake driving din motar yayi parking, Ya fito Ya zagaya ya bu e mashi murfin back seat dinta, afarshi ka ai ya zuro waje Gaban ummi ya fa i rasss, jikinta ya soma kakarwa, A hankali ya arasa fitowa daga cikin motar, kamar kullum cikin shiga ta malamai magadan annabawa, bai aura idanunsa akan kowa ba sai akan Ummin america, a sukwane ta mi e tana gyara mayafin da tayi rolling, taj kuwa fuskarshi dauke da murmushi ya nufi sheikh imam yana fadin"Ya sheikh Barka da zuwa tun azu muke ta sa ran ganin ka" Martanin murmushin Shiekh Imam ya mayar masa a yayin da yake kokarin kau da idanunsa daga na ummi ya mayar da su akan fuskar taj, musabaha su ka yi shikeh imam yace"Ay min afwa, ban samu damar zuwa duba mara lafiya na ba, wallahi yana araina da shi na wuni, wani uziri ne ya ru e ni" Jiki na rawa Ummi ta juya ta nufi ofar shiga falo, Duk don kada su gaisa da sheikh imam, har ta kusa kaiwa ga ofar muryar taj ya ratsa kunnanta "Ummi, ki zo mana ku gaisa da sheikh imam" tamkar an dasa mata aya ta tsaya cak, tana mai mayar da numfashi, Har cikin ranta bata ji da in dakatar da itan da yayi ba, sai dai bata jin zata iya watsa mashi asa a ido, musamman yau daya faranta mata rai. Tunkafin ta juya ta soma jin takun tafiyarsu bayanta, jiki asanyaye ta waiwayo tana dubansu, lokacin da suka araso da sauri ta sunnar da kanta asa, muryarta na rawa ta furta"sannu da zuwa" Cikin sanyin murya ya amsa mata da yawwa Taj dake dubansu a fakaice yace"sheikh bari na gabatar maka da ummi,"jinjina mashi kai yai alamar toh "Ummi Tamkar uwa take a wurin yaran da muke raino, ita ce take kula da su" Fuskar sheikh babu annuri ya furta"anya kuwa sunyi dacen uwa"? Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aru e ya kalli fuskar shaikh imam *Daga alkalamin Boss Bature Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 10 Complete Novels Elite Admin May 25, 2024 _ *~ BOSSLADIESWRITERS ~Takun arshe An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ Har sai da gaban ummi ya fadi rass jin abun da yace, hatta shi kanshi taj aru e ya kalli fuskar shaikh imam. "Ya sheikh ko zan iya sanin dalilin da ya sa ka ce haka? Acewar Taj Sheikh imam yace "Tun da nake zuwa gidan nan ban ta6a ganin ta taka zuwa akin yaron nan ba, domin duba lafiyarshi, bansani ba ko tana shiga bayan bana nan amma raina na bani tamkar bata zuwa, a matsayinta na maru iyarsu yakamata ace tafi kowa bashi kyakkyawar kulawa ko da kuwa addu'a ne take zuwa tana yi mashi akai akai" tun da sheikh imam ya fara kora jawabi hankalin ta ya kwanta jikinta yai sanyi la was. "sheikh maganarka gaskiya ne, ummi baki kyautawa, kinga har sheikh