← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 163 OF 247

Sashe 163

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

gindaya mashi na kusantar inda take sai gashi yau saboda halin data shiga na gudun kada ta rasa shi yasa ta kunsata kanta da shi ta kuma rungume shi saboda tana bukatar jin dumin shi a jikinta, tausayinshi da kaunarshine suka rufe mata ido har tagaza gane abunda take badai dai bane ta manta. Sunyi shiru babu mai magana acikinsu, ko motsi basa sonyi saboda yanayin da suka tsinsu kan su mai wuyar fassaruwa ji suka inama zasu dawwama ahaka sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi ko ba mutuwa akwai kaddara da zata iya raba su Da wata irin kasala Yasa hannu yaja hijab din jikinta ta zame ta dawo kan kafadarta. ya cusa hannunshi cikin lallausar sumar kanta ya nanna eta gefe guda ya fiddo da kunnnata na dama. Saitin kunnan ya daura tausasa red lips dinsa cikin sanyin murya mai dadin sauraro ya furta"kamar baki yarda da kaunar da nake maki ba? Meyasa zaki aga hankalinki bayan kinsan cewa bazan iya rayuwa batare da ke ba, idan ma kina tunanin hakan toh ki daina...." ya fa a cike da bata tabbaci har cikin kunnnata take jin iskar numfashinsa.. "mutun yana rayuwane tare da addararsa sannan bai isa ya guje mata ba, nima haka take agurina, bazan taba tafiya nabarki ba in har bake kika bani iznin in tafi ba, ke kadaice zaki bani umarni in bi, gaba aya burin rayuwana akanki ne da yan uwana, bazan ta6a rabuwa babu ku ba, duk runtsi duk wuya zan kasance atare daku" bai are maganar ba ta tari mumfashin shi da cewa"ka yi hakuri da abun da ya Omar yayi maka, nasan shine ya bata maka rai, nima raina ya 6aci zanyi mashi magana yadaina bata maka rai" ta fada ba tare da ta dago kanta ba. Murmushi ya danyi har cikin zuciyarshi yaji dadin maganarta shiyasa yake kara kaunarta saboda kaunar da take masa, zata iya bata mashi rai amma wani bai isa ya daga masa yatsa ta kyale shi ba. "Ki kyale shi, ba laifinsa bane, ni ne na 6ata masa rai, komai ya faru ni naja ma kaina.." Hankalin shi Yayi mugun tashi da abunda idanunsa suka gane mashi, tsabar kidima da tashin hankali har wani jiri jiri yake gani acikin idanunshi, da sauri ya dafe kofar dakin gudun kada jiri ya kwashe shi ya kife asa, Yayi danasanin zuwa dakin Danish dayasan zaiga abunda zai jijjiga kwakwalwarsa da tashi hankali da baiyi gigin zuwa ganin Danish ba!. Ya gaza yarda da abunda idanun shi ke nuna mashi da kuma abunda kunnuwanshi suke jiyo mashi. Angel dinsa ce kwance ajikin namiji sun kankame juna kamar anta da jini? Wlh bai ta6a zaton zatay mashi haka ba, ta karya zuciyarshi ba kadan ba. bazai juri kallon su ba, adaddafe Ya juya yabar kofar dakin dama yazo ne donya ga Danish Chief ne Ya bashi labarin sun ganshi, bawan Allah da farin cikinshi ya zo don ya bashi hakurin abunda big guy yayi mashi ashe da rabon yaga abun da zai hana shi runtsawa adaren yau. shi mamakin shi tayaya Unaisah har tasan dadin ta rungumi namiji? A tunanin shi batai wayon da za ta yi hakan ba, bayan haka yana yi mata kallon mai hankali bai ta6a zaton zatay abunda tasan haramun ne ba. yana tafiya kamar zai kife kasa saboda jirin dake shirin kwasar shi, babban tashin hankalinshi ya zaiyi ya raba ala ar su? Saboda ya fahimci azababbiyar kaunace atsakaninsu ko romeo da juliet albarka, kai wannan har layla da majnoon sun shallake sai yanzu ya gane dalilin dayasa azu ta haukace tabi bayan Danish har mota takusa hankadeta ashe sone Ya makantar da ita. shi azaton shi shakuwace atsakaninsu ashe shine bai fahimta ba, bakomai yake tunawa ba face alkawarin daya daukarwa kanshi na mallaka ma chief Unaisah, tun kafin ma ta bayyana ya bashi ita, sadakine kadai bai biya, ba yadda za'ay ma ya amince ma soyayyar Unaisah da Danish! Ko ta halin a sai ya raba su, bama zai ta6a yiwuwa ba, ay bata isa tasa shi zubda girman shi ba, bare aje ga batun bashi kunya. Acikin zuciyarshi yake ta sambatu kamar wani zautattace. Peck ya manna mata akan forehead dinta ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu yana ratsa tsigar jikin ta. numfashi ta anja tare da sauke shi kan kirjin shi iskar ta daki fatar shi. tana kokarin ago da kanta kamar daga sama tajiyo muryoyinsu Batool daga waje suna ambaton sunan Danish a ru e ta raba jikin ta daga nashi tayi saurin komawa bayan curtain ta 6oye tana faman sauke ajiyar zuciya. Bin labulan yayi da kallo baiso suka katse masu hanzarin su ba, murmushi yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba, daga gani yaji dadin faranta masa rai da tayi. Kamar an korosu suka fado dakin ko sallama babu, da karfin suka hada baki gurin furta"Danish"! Juyowa yayi tare da kallonsu, gaba ayan su ne babu wanda babu acikin su. Wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskokinsu, bayin Allah tun da suka dawo daga headquarter tashin hankalin bacewar shi Ya hana su canza uniform din jikinsu ko wanka ba su yi ba. harya motsa lips dinsa zai yi magana bai yi aune ba gaba daya suka nife shi suka fada kan jikinshi kamar zasu kayar da shi kasa, saboda yadda suka baibaye shi kamar udajen zuma, gaba daya sautin kukan su ya cika dakin nashi. dayasan halin da zai jefa su da bai tafi yabarsu ba, a zaton shi sun daina damuwa da shi ashe har yanzu ba abun da ya sauya na daga kaunar da su ke yi ma shi. Dakyar ya samu suka kyale shi cikin shesshekar kuka suka fara korefe korafe akan tafiyar da yayi yabar su. Haris daya fara zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu kowa yana fada masa irin tashin hankalin daya shiga, murmushi yadinga sakar masu kamar zaiyi dariya saboda sun bashi nishadi sun kuma faranta ranshi, ita Batool da tafi su jin jiki pillow ta dauko ta fara buga mashi kan kirjin shi aikuwa kamar jira suke gaba daya suka fara wasa da pillows suka dinga kwala mashi ta ko'ina. tun yana murmushi yana kokarin kare kanshi harya fara ti ar dariya kamar sakarkaru haka suka saki baki suna kallon shi cike da mamakin ganin Dariyar shi. Duk abun da ke faruwa akan idon Unaisah gaba daya ta shagala da kallon fararen hakoranshi masu kyau da tsari sai dariya yakeyi kamar zai sha ba su kyale shi ba har saida ya fa a kan gadon shi yana fadin ya isa haka na kar6i laifi na bazan kara tafiya nabarku ba.." jefar da pillows din su ka yi kan mattress din sai haki suke suna kallon shi sun kewaye gadon shi. "Waya fa a maku na dawo" ya tambaya yana kallon su, Atare suka hada baki gurin furta"daddy Taj" "Banyi zaton kun damu dani har haka ba..." bai kare maganar ba suka fara na e hannayen shirts dinsu alamar zasuyi bugu dabi'arsu ce tun a prison.. "Ku kyale shi ya gane kuskuranshi" muryar Unaisah ce ta dakatar da su, atare suka jiyo tare da kallon ta, tana tsaye atsakiyar dakin duk a tunaninsu daga waje ta shigo ba su san cewa tana la6e jikin labule ba. Haduwa sukayi gaba suka zauna gefen gadon shi, ba zasu iya tuna when last suka nishadantu da Danish irin na yau ba, ya sakar masu fuska sun yi fira cikin raha sunyi nishadi kamar lokacin da suke a prison. Jin shiru Unaisah bata dawo ba, tun da tace ta jira har yanzu bata ji duriyar ta ba, gajiya tayi da zaman dakin shiyasa ta fito don ta neme ta, sai kuma ta taras babu su a falon har zata juya idanunta suka sauka akan taj dake zaune kan sofa ya zabga uban tagumi kamar wanda ya rasa mafa i a duniya, tun daga kan yanayin fuskarshi ta fahimci babu lafiya atare da shi, kamar akwai wani abu na damun shi. Karasawa tayi gaban sofa din da yake ta ambaci sunan shi shiru bai tanka mata ba, har saida ta maimaita kusan sau uku na karshen ne ta aga murya a an firgice ya dago da ido ya kalle ta, murmushi tasakar mashi, da sauri ya fara kokarin danne damuwar shi ya an saki murmushin yake yace"Ummi ya kike, kin wuni lafiya" bata amsa mashi tambayarba sai cewa tay"yalla6ai meke damunka ne? Kusan sau uku ina kiran sunanka baka amsa min ba, anya lafiya" still da murmushi akan fuskarshi ya furta"ummi ba komai lafiyana lou, ba abun da ke damuna" Tunani tayi kodai rashin Danish ne yasa shi shiga halin damuwa hakan yasa tace"Ya mukaji da abun da ya faru na 6atan Danish? Wlh nima azu Batool ke fadamin, Hankalina ya tashi ba ka an ba.." bata kare maganar ba taj yace"oh bakisan An gan shi ba..." waro idanu waje tayi"dagaske"? "Eh, ay yanzu haka su Unaisah suna acan dakin shi" wani irin ihun farin ciki ta saki tare da firta Alhamdulillah kusan sau uku tace"wlh naji dadin ganin shi da akayi, saboda hankalina ya tashi musamman ganin yadda yan uwanshi suka gaza cin abinci saboda rashin shi. "bari naje naganshi" har zata jiya taj ya kira sunan ta tajiyo ta dube shi. "Idan kin shiga dakin, pls ki kirasu, su zo su shirya akwai baki da zasu zo bayan sallar magbrib" amsa mashi tay da toh, zumudin son ganin Danish Ya hana ta tambayi su wanene bakin da sauri ta juya ta nufi upstairs. Bin ta da kallo taj yayi har ta 6ace ma ganin shi, sunkuyar da kan shi asa yai kamar bawan dake neman gafara, abun duniya ya ishe shi tun dazu bakin cikin abunda yagani yake ta nanukarsa, idanunshi sunki daina tariyo mashi abun takaicin daya gani.... Lokacin da takarasa bakin kofar dakin tunkan ta shiga ta fara jin hayaniyarsu yadda kasan gidan biki ko suna sun cika ko'ina da surutun su. knocking kofar tayi almost 3 times ba wanda ya bu e mata, zafin dumi Ya hana su ji bugun kofar, murmushi tasaki tare da tura ofaf ta shiga ciki Tsayawa tayi tare da goya hannayenta kan kirjinta tana kallon ikon Allah
Chapter 163 · 0% Book details