Sashe 24
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
(Mu hadu monday idan Allah ya kai mu da rai da lafiya in sha Allah) *Daga Al alamin Boss Bature Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 12 Complete Novels Elite Admin May 28, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~ BOSSLADIESWRITERS ~Takun arshe An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ Gently ya dira afarsa kan Polished marble floor din wurin A matu ar ru e suka kai idanunsu kan mai shigowa yayin da zuciyoyinsu ke harbawa da arfi arfi. Lokacin daya arasa shigowa ciki, Gaba aya Suke bin shi da kallo mai cike da tsantsar ru ani, idanun kowa akan zazzafar surar jikin shi, kasancewar ya sanya face mask hakan ya 6oye ainihin suffar fuskarsa, wato wata hadaddiyar Emirati thobe ce a jikin shi yar ubansu launin Black gold, yadda kasan a jikin shi aka inka ta saboda yadda ta bi shape nasa, ta baiyanar da surar shi mai matu ar jan hankali, Musamman sick packs din kirjinsa ya fito 6aro 6aro, da mur an damtsensa, abun ka ga dogon namiji komai nashi is exraordinary, farar fatarsa kuwa har wani sal i take tana walwali, yadda kasan namijin hurul aini tsabar kyau da daukar ido, wrist din hannun sa na asanye da agogo irar Rolex sai yalli take, face mask din dake lullu6e da fuskarshi dai dai asan idanunsa ya rufe kyawawan sexy eyes dinsa wa anda ke a kewaye da lallausan long eye lashes dark brown sun ara awata kyawun idanunsa, yalwatacciyar sumar kanshi kuwa tasha gyara har yalli take, gaba aya gashin an tattare shi an aure yasauka har kan gadon bayan sa, Wani irin sanyayyan amshin turare ne ke fita daga jikin shi mai narkar da zuciya, Hankali fa gaba aya ya tashi da ganin an tahalikin nan, tun kafin ma ya bu e fuskarshi sun gama girgiza da kyawun shi, kowannansu sake sake yake a zuciyarsa wanene wannan? Daga ina Yake? Zuciyoyinsu ba su gama ki ima ba, sai da su ka yi tozali da kyakkyawar matashiyar dake shigowa hall in ta bayan shi, wohoho zo ka ga yadda idanu suka koma kanta, from head to toe suke kallon ta, ta auki wankan Embroidery Open front baya, launin black anyi mata adon gold stone works da zanan Red flowers, rigar tayi masifar yi mata kyau, ta yi rolling mayafi akanta, itama fuskarta asanye da face mask take, afafuwanta kuwa Highhills ne jigunanu, Tsabar ru ani Ya hana kowa na hall din furta magana sai dai su bi da idanu kamar kurame, ko da shigowarta daga gefen shi ta tsaya, Jim kadan suka cigaba da shugowa kowan nan su da face mask, matan cikin shiga ta abaya mazan kuma Emirati thobe ne a jikin su, sai da suka cika su goma sha aya cuff tukunna suka dakata suna kallon kallo atsakanin su da mutanan hall din, ga dukkan alamu bakin su ya mutu, saboda babu alamun zasu furta magana, lamarin ya ru ar da su, mamakin su ina aka samu wadannan matasan yan matan da samari? Daga gani dai ba yan nahiyar su bane saboda komai nasu is exraordinary, dai dai da yanayin tsayuwarsu abun kallo ne kamar a shirin drama. alla an shafe tsawon Mintuna ana jifar juna da kallon urulla, da yar Hajiya saratu ta samu warin giwar bu e baki ta furta"Su wanene ku"? Ta jefa masu tambayar tana mai zare idanu "Bayin Allah daga ina ku ke? Wanene Ya gayyace ku dinner din nan? Meyasa ku ka rufe fuskokin ku da face masks? Hajiya Madina ce tayi maganar a agare da son jin amsarsu Gaba aya mutanan hall din suka matso gab da su, kamar sunga sabbin halittu daga wata duniyar "To ko dai mutanan boye ne? Wai ba zakuyi mana magana ba, kuntsaya kuna kallon mu kun bar mu a cikin duhu"! Da tsiwa hajiya laurat ta fa a tana tada jijiyoyin wuya. "Anya kuwa wa annan ba mutanan 6oye bane? Nifa wlh hankali na bai kwanta da su ba, akan me zaku fa owa mutane akin taro babu sallama? mun tambaye ku su wanene ku kun yi shiru ba ku tanka mana ba, ko dai turo ku akayi ne don ku tarwatsa mana taron mu"! A fa a ce Hajiya saratu ta kuma yin magana, Hankalin fa kowa Ya tashi wasu sun harzu a, su kan su tsabar fargaba ne ya hana su bu e baki suyi masu sallama, duk sun sha jinin jikin su. Baba obie da Manyan mutanan canada sunyi kasa ai Suna Kallon su tamkar a shirin drama, sam babu alamun sun tsorata da ganinsu saboda sun san akwai jami'an dake tsaron gurin dole akwai wanda ya gayyace su, sai dai zallar mamakin dake shimfi e a kan fuskokin su. an matasan family din maza da matansu sunyi cirko curko suna kallon su, cike da son sanin su wanene wadannan bakuwar fuskan da suka fa o masu a hall!!! Mc da ke atsaye ya ru e mic sai mazurai yake yana fadin"ga dukkan alamu mun samu ba i daga jinsin aljanu, suma sunzo taya mu jimamin tafiyar prime minister Hateem, wannan abun mamaki ne da al'ajabi, lallai prime minister ba karamin mai farin jini ba ne......." sai sambatu mc yake yi yana dubansu babu alamun wasa akan fuskarshi, bilhakki dagaske yake koro jawabi, su sir mubarak kuwa jira kawai suke suga iya gudun ruwan wadannan bayin Allahn da suka fa o masu bagatantan babu sanarwa. Sannu A hankali sautin takalman prime minister ya kara e tsakar filin, babu fargaba ko ka an Ya nufi inda suke har ya arasa gaban matashin nan daya fara shigowa kafin yaci burki yana bin shi da kallo tun daga sama har asa, hakanan ranshi ya dinga bashi cewar yaron daya jima yana kwa ayin sanyawa a idanun shi ne, zuciyarshi ce ta soma azalzalar shi da son tabbatar da abun da yake hasashe, a hankali Ya juyo baya ya dubi chief owais dake a can gefe aya ya goya hannayensa bisa ga kirjinsa tamkar baisan meke wakana ba Ha a ido su kayi da prime minister, cikin sanyin murya ya furta"shi ne...? *WAIWAYE A DON TAFIYA* Abun da ya faru, lokacin da Chief ya dawo gidan bai samu kowa a falon ba,, har su naufal da suka zauna sun koma daku nan su, direct Ya nufi bedroom dinsa bayan shigar shi, tsayawa yayi agaban mirror zuciyarsa a cike fal da tunanin ta wace hanya zai iya taimaka ma Uncle dinsa! Saboda yaji tsantsar tausayinsa ganin irin halin da ya shiga na kaunar yaron, bai da burin daya wuce danish ya farka ko dan Ya faranta Ma daddy hateem kafin yabar nigeria.... Yayin da ya ke wannan tunanin Yana safa da marwa a tsakar akin sa Ya shafe kusan Mintuna ashirin, Batare daya samu mafita ba, Yanke shawarar kiran layin aya cikin drs dinsu yayi don azo aduba lafiyarshi wata'kil adace, duk da shiekh Imam Ya ce basai sun kira likita ba saboda rashin lafiyar tasa bata asibiti bace, kawai a lokaci Ya osane daya farkan shiyasa ya yi deciding kiran likita. A firgice ta farka daga gajeran baccin da yayi awon gaba da ita tun bayan kammala sallar azhar, Hannun ta dafe da saitin zuciyarta dake yi mata wani irin bugu tamkar ana dakan sakwara, wani irin fa uwar gaba ta soma ji, Hankalin ta sam ba'a kwance yake ba, tarasa gane dalilin jin bugun da zuciyarta take yi mata da rana tsaka, kuma ita ba mafarki tayi ba, saukkowa tayi daga kan gadon su, batool dake a kwance babu alamun zata farka, Cikin sauri ta fito daga room dinsu zuciyarta na azalzalarta da taje ta ara duba danish dinsu don tana ji aranta wani abu ne ke faruwa da daya daga cikin su shiyasa taji wannan faduwar gaban, kuma bakowa ne ya fara fado mata aranta ba face shi din dama da tunanin shi ta wuni. Gudu gudu sauri sauri ta nufi second floor, ko da ta shiga falon babu kowa. Tana arasawa bakin ofar ta sanya hannu biyu ta dafe ta da karfi har sai da ta bu e kafin ta fa a a fujajen shigarta keda wuya, idanun ta su kayi mata tozali da abun da Ya figitar da ita, da wani irin faduwar gaba take kallon shimfidar shi. Wata irin zuface take tsastsafo mashi tun daga cikin sumar kanshi take gangarowa har izuwa saman fatar wuyan shi, kyakkyawar fuskarshi ta ji e sharkaf da gumi, hatta jallabiyar jikin shi ta manne ma fatarshi saboda ruwan zufar daya ji e ta, muryart na kerma ta soma kokarin ambaton sunan shi. "Dad...da..nish" bata are maganar ba, ganin yadda yatsun hannayensa dana afafuwansa suka fara kerma tamkar na wanda sanyi ya kama. Kasa samun nutsuwa tayi, har batasan sa'adda ta haura saman gadon nashi da rarrafe ta arasa saitin inda kanshi ya ke, ta zuba mashi ido tana kallon shi da tsananin firgi ci. Cikin lokaci ani, Ilahirin Jikinsa Ya ji e sharkaf da gumin zufa, lamarin yayi matu aure mata kai. Tsabar Yadda Jikinsa ke kakarwa Har gadon kerma yake yi ita kanta jikinta ya kama kakarwa, tun zuciyarshi na bugawa a hankali har ta fara bugawa da matsanancin arfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito waje, sautin numfashinsa mai ha e da gurnani ya gauraye bedroom dinsa, da karfi Yake Jan shi tamkar babu wadatacciyar iskar da zai sha Ko wani sashe na jikin shi tuni ya soma motsawa, Unaisah dake kallon shi idanunta azazzare duk tabi ta rude ta firgice Lokaci aya tsoro Ya cika ta, Zabura tayi da niyar ta watsa aguje gudun kada Ya cutar da ita don ta fahimci kamar baya hayyacin sa ... Sai dai kafin tayi wani yunkuri juyawa yayi wani kwakkwaran juyi tamkar mayunwacin zaki haka Ya dam o sumar kan nan nata daya sha gyara gaba aya ya dawo da ita jikin sa, Yana huci ya matseta kamar zai tsinkata biyu, Ji tayi tamkar an daureta da igiyoyin kaca, hucin zafin jikinsa har anata jikin take jin shi, Zuciyarta ce ta bata shawarar ta hanka e shi ta gudu, kafin yai yun urin cutar da ita, Cikin arfin Hali ta daddage ta fusge kanta daga ru on da yayi mata,