Sashe 54
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
tafi gida" atare da zayn suka raka zahra bakin mota bayan ta shiga ta zauna, hajiya saratu tace"surukata, Anya zaki iya driving dinnan kuwa? Ko dai zayn yakai ki" wani irin mugun kallo zayn ya watsama zahra da sauri tace"a'a mommy, wallahi zan iya, ay ba sosai nake jin ciwon kan ba" "Toh zahra Ki kula min da kanki sannan ki gaishe min da mutanan gidan" "In sha Allah ngde ssae" Harara hajiya saratu ta watsa ma zayn"kai bazakai mata bankwanan ba, ahaka zakuyi auren" yana faman yamutsa fuska yace"bye, sai mun yi waya" aran shi ya furta "zakiyi danasani," Bayan ta baro estate din har ta hau kan titi tana driving, zuciyarta bata daina tariyo mata kalaman zayn ba. Uban tagumi aneelerh ta zabga da hannu aya, tana kallon zahara data kammala bata labari "Zahra kinyi kuskure wlh, meyasa baki auki shawararshi ba kin fada mata baki son shi? Zahra ina guje maki auran mutun mara kunya irin shi! Kowace uwa burinta ta sama ma ya'yanta uba nagari wanda zasu koyi da shi su kuma yi alfahari da shi ba irin zayn ba, sam bai dace dake ba" zuciyarta ajagule tafada, kwata kwata zayn bai kwanta mata aranta ba, tun kafin ma ta ganshi. Zahra Tana shesshekar kuka ta ruko hannunta"ki tayani da addu'a, ita nafi bukata, Aunty aneeleeh bawai nakasa fada mata bane, Ina son shi ne" Jinjina kai aneeleeh tayi"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Shikenan, zan tayaki da addu'a Idan alkhairi ne shi agare ki Allah Ya tabbatar mana dashi, idan kuma akasin hakan zan roki Allah Ya shiga tsakaninku, bayan haka dole su mami suji maganar nan" kwantar mata da hankali aneelerh tacigaba dayi saida komai ya lafa tukunna aneelerh tace"Ina alkwarina? Kince zaki aukar min hotunan dinner in gani, Jiya da su na kwana araina, ganin kin kwaso gajiyane yasa ban takura maki ba" Murmushi zahra tasaki tunawa da Unaisah, yarinyar data kwanta mata aran ta. "Aunty aneeelerh, akwai labari, zaki sha kanun labarai, " ta fada tare da janye baby juanid dake langwa6e ajikinta, kamar maijin bacci Yai shiru Yanata sauraronsu. Gado Ta nufa ta dauko purse dinta ta curo wayarta donta nuna ma aneeleeh hotunan da ta dauka tare da unaisah Kwatsam wayar ta fara ringing, da sauri tayi picking ganin sunan abie Barka da safiya abie ina kwana"? "Lafiyou, zahra, Ina aneeleeh ne"? Da sauri tace gatanan adakina "Okey ki fada mata, awarta ta turo min da sako ta layina, ta zo ta same ni a daki ina jiranta!" amsa mashi tayi da toh bayan ya kashe kiran ta dubu Aneelerh dake kallon ta, cike da son jin me abie Ya fa a mata. "Abie ne ya kira, yace in fa a maki Kawarki ta tura mashi da sako ta layin shi kije ki same shi adaki" Da alamun mamaki Aneeleerh ta furta" awata kuma? Anya kuwa abie ya karanta sakon dai dai? In bahaka ba ni wata awace gare ni da zan bata layin abie" "Aunty Aneelerh kije kawai ki gani, bamusan menene aka turo ba" amsawa tayi da toh a hanzarce ta mike ta bar junaid adakin. Ruko hannun shi zahra tayi"zonan In nuna maka hotunan dinner," Gefen gado ta zauna tare da daura shi kan laps dinta, ta bu e gallery tana nuna mashi hotunansu, lokacin data bu e hoton Unaisah, wuff Junaid Ya fusge wayar daga hannunta Yana fadin"Angel! angel! angel"! Har saida gaban zahra Ya fadi, a matukar rude take kallon shi ba tare data fahimci me yake nufi ba. *SALSABEEL Zaune Yake kan sofa hannun shi ruke da wayar shi, Har ya kammala shiryawa, sai faman duba agogo Yake yi, Har ya fara gajiya da jiran su, agowa yai tare da kallon su, suna a zaune tsakar falon suna cin abinci, mutun aya ce ke babu acikin su, Khadeeja dake acan cikin toilet tana wanka, a kalla ta shafe kusan awa aya da rabi har yanzu bata fito ba, gashi har yan uwan ta sun kammala shiyawa. "Dan Allah ku yi sauri ku arasa, kun ga har karfe sha biyu ta buga" amsa mashi sukayi da toh "Yaya salsabeel, Khadeeja fa? Har yanzu bata fito ba, ko ban da ita zamu tafi" rubeena ce tayi maganar. "Bansan ya zanyi da ita ba, so take ta 6ata mana lokaci, bari naje na dubo ta" ya fada tare da mi ewa Ya nufi upstairs. "Wallahi Dama mu tafi mubar ta a gida, kada ta mana hauka, tun da ya salsabeel Yace wurin gasar kyau zamu je kuma in muka ci za'a bamu kyautar wani abu" acewar hibba. rubeena na murmushi tace"ni zan cinye ma gasar saboda nafi ku kyau" harara hawwa ta galla mata"a haka din? Dubi kumatunki, kuma ay cewa yai sun fi son mace doguwa mai gashi, mara jiki, me dogon hanci" daure fuska rubina tayi rai a6ace tace"wlh indai bani zanci ba sai dai kowa ya rasa" ta fada tare dakai hannu ta dauki robar zuma ta dinga watsa masu akan rigunansu, azabure suka mike suna faman zare idanunsu ganin ta 6ata wankan su. "Wallahi baki isa ba, Saina rama mana" sarah ce ta fada da sauri ta fisge zumar ta matsa mata a jikin rigarta, fashewa tayi da kuka tana fadin wayyo Allah ya salsabeel sun 6ata min kayana, shikenan ni bazanci gasar kyau ba, zu unnawa tayi gaban kayan abincin tana haki ta dauki coke da niygar ta watsa masu, dam o hannunta Hawwa tayi nan fa fa a ya kacame a tsakaninsu, daga wadda za'aja ja ma gashin kai sai wadda aka ca6e ma kwalliyar fuskarta, Mubeen dake a zaune yana kallon su sai faman tikar dariya yakeyi Duk wannan budurin da sukeyi salsabeel bai sani ba, Yana atsaye bakin kofar toilet din dakin su khadeeja, ba irin bugun kofar da baiyi mata ba akan ta fito, amma ta i ko tanka mashi. Rai a6ace yace"wallahi idan kika bari nasa kafa nabar dakin nan sai dai ki zauna agida, Babu inda zaki je" muryarta da shesshekar kuka tace"wayyo Allah ya salsabeel ba kaine kace zamuje gasar kyau ba, shine fa nakeso in koma fara" waro ido waje yai jin soki burutsin ta, cike da takaici ya furta"Baki da hankali ne? Tayaya za'ai ki koma fara? Waya fada maki sai farare suke cin gasar kyau? to bari ki ji in fada maki bakake sune suka fi lashe gasar" muryarta da shagwa6a tace"ni dai Allah ba wani nan wayo kakeso kai min don kada inci" Dafe kanshi yai da hannu aya"ke zaki fito ko ba zaki fito ba" shiru tayi bata tanka masa ba, Buga kofar yai da karfi"Khadeeja ranki zai 6ace in baki fito ba" still bata tanka mashi ba Banko kofar dakin akay, Mubeen ne ya fado ciki kamar an wurgo shi, Rigar shi duk ta 6ace da jan bakin su rubina A ru e salsabeel ke kallon shi Yama rasa ta ina zai fara "Yaya salsabeel, Kaga su rubina sun 6ata min kayana da jan bakinsu, kawai saboda nayi masu dariya suna fada" bai karasa sauraren shi ba yai saurin fucewa da sauri mubeen Yabi bayan shi tunkafin Ya sauko down Ya hango su manne da juna, sun kacame kamar irin kifin gwangwanin nan sai ihu suke Yi, Wata irin tsawa mai sauti Ya daka masu a firgice suka saki junansu, suna ganin shi suka fara kokarin bare baki zasuyi kuka Nuna su yai da yatsan hannun shi"kar wadda ta kuskura tayi min kuka" ya fada yana zare masu idanun shi da alama ranshi ya 6aci, Yaji haushin yadda suka 6ata kayan su, abu tun karfe kusan tara na safe ake ta fama yaki ci yaki cinyewa Sam yakasa yi masu fada, baisan meyasa yake jin nauyin ya furta masu kalma mara dadi ba. "Yanzu abun da ku kayi kun kyauta"? Sunnar dakai kasa sukai har suna hada baki wurin fadin"dan Allah ka yi hakuri ba zamu kara ba" ta6e baki yai" a haka zamu tafi,tun da kunfi son aganku a haukacen ku" "Ya salsabeel dan Allah kabari mu canza wasu kayan," harara ya watsa masu, rai a6ace Ya kama hanyar fuce wa daga falon Yana Fadin"ni na tafi sai kun taho" Watsawa su ka yi aguje suka nufi bedrooms dinsu, Jim kadan suka fito har sun canza kayan jikin su.. Salsabeel Yana atsaye gaban motocin da za su shiga,, Jami'in da zaiyi driving din su Har Ya hallara a mazaunin driver, da gudun gaske khadeeja ta fito hannun ta ruke da takalmanta, har tana bangaje Su Yasmin, kamar a filin Yaki, gaba daya hankalin Jami'an dake tsaron gidan sai da ya dawo kanta, wani burgujejen wando tasanya yadda kasan kafafuwan agwagwa, ga wata yar yaloluwar riga mai hannu daya, Ta dambara jan baki akan la66anta har saman kumatuntu, mascara din data sanyawa eye lashes dinta ya zazzago har kasan idanunta, babu wanda bai firgita da ganin ta ba, Jami'an sai faman kunshe dariya suke yi a bakunansu, ko mayafi babu akanta sai wannan guntun gashin kan nata mai an yawa data fake shi da ribbom Ya karkarce gefe aya. Ko ta kansu bata bi, Tana isa bakin motar, ta jefa takalmanta cikin car window, kafin ta daddage ta kama glass din Ta zura kanta aciki ta soma kiciniyar kutsawa ta karfi, dafe kai salsabeel yay da hannu aya tamkar zai fashe da kuka, ya ma rasa me zaiyi, su rubina duk sun bude bakunansu asake suna kallon ta. A hanzarce Ya cafko kafafuwanta, Ya zarota daga tagar, tana ta faman haki ta dube shi idanuwan nan nata kamar na babie sai kyaf kyafta su takeyi _"Ya salsabeel baka ce nayi kyau ba" Cikin sanyi murya yace"kyawun ne ya ru e ni shiyasa nakasa magana" ya fada tare da bude mata murfin motar, ta shiga ciki ta zauna, Bayan kowan nan su Ya shiga, A jere suka fuce daga gidan kai tsaye suka haura kan titi_ *Daga Al alamin Boss Bature Mu Ha u Monday Idan Allah Ya kai mu da rai da Lafiya *Littafin kurkukun addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura* 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Tags Kurkukun Kaddara