Sashe 79
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature Chief na waje ya ji yo sautin fashewar wani abu daga dakin danish, a hanzarce ya tura kofar ya shiga kwatsam ya taras da abun da banyi tsammani ba Gaba aya ya fasa laptop din, ya raba ta gida hu u, hakan bai masa ba sai da Ya zu unna a gaban pieces in Ya sa hannu Yana tatta6a su kamar wani zararre komai ya kwance masa Chief Ya jinjina ma lamarin, abun ya aure masa kai tamau, ta inda ya gode ma Allah laptop ba wadda ya ke aiki da ita ba ce, da kuwa yaja masa babbar asara. "Meyasa ka fasa ta? why pls ? Ko kallo bai ishe shi ba, damuwarsa akan Hateem ne da bai gani ba bayan yasha wahalar balla abun Girgiza kai chief yayi"da ita ne zaka iya amfani wurin yin magana da shi saboda baya a Nigeria" agowa danish yayi fuskarsa a yamutse gaba aya ya rasa sukuninsa, shi fa ya fasa ne da niyar ya bu e ma prime minister hanyar da zai iso gare sa. "It is okey, koma ka zauna kan gadon ka, a hankali Ya koma kan gadon yana faman bin laptop din da kallo arasawa chief yai tare da kwashe pieces din ya fuce daga dakin Ya koma bedroom dinsa Yana shiga wayarsa ta fara ringing Da sauri Ya aura laptop pieces din kan couch kafin Ya auki wayar yai picking "Owais meya faru ne? Muna cikin yin magama da shi naji uff ya katse kiran" "Uncle mai kuke tattaunawa ne da shi"? "Cewa yai yana son ganina in fito daga laptop din, nace masa bayadda za'ay amma ya matsamin shi ne fa naji shiru kiran ya katse" "Uncle Ya 6alla laptop in, gaba aya ta tashi aiki, Allah Yaso ma ba wadda nake amfani da ita bane ay dayaja min asara" Muryar Hateem da mamaki Ya furta"what? Ya fasata? Amma meyasa yayi haka"? "Saboda ka i fitowa, may be yana nema maka hanyar da zaka fito daga cikin ta ne" Kusan atare suka fashe da dariya daga hateem din har chief din saboda abun Ya basu mamaki da al'ajabi...... Dakatawa sukai da yin dariyar, kowan nan su yayi shiru na an wani lokaci, kwatsam sautin shesshe ar kukan prime minister hateem Ya kara e kunnansa lokaci aya zuciyarsa ta buga saboda jin abun da bai zata ba, aru e ya furta"uncle? Kuka kake yi? Ko dai kunne na ne suka ji min badai dai ba"? Muryarsa araunace Ya furta"Ina tausayin rayuwarsa owais, ya karya min zuciyata yau, mutum har mutun baisan komai ba, da ace ya taso cikin kulawar iyayensa koda ba dan masu hali bane zai samu ilmin addini dana zamani dai dai gwargwado....." yana magana sautin na fita da alamun kuka maitsuma zuciya. Lumshe ido chief yai kafin Ya furta"pls ka kwantar da hankalin ka uncle, zanyi iyakar bakin kokarina don ganin ya samu ilmi akansa, kamar yadda nayi maka al awarin bashi kyakkyawar kulawa..." "Owais idan zai yiwu ku sanya shi makaranta, Ni zan auki nauyin karatunsa because I want him to be like everyone else. ni wallahi da zaka bani dama zansa akawo min shi nan canada" Cikin kwantar da murya owais yace"Uncle zuwansa canada bazai yiwu ba, akwai abun da ban fada maka dangane da rayuwar su ba, amma dan Allah kayi min Uziri uncle nan badajimawa ba zan sanar da kai komai....." Yana jiyo sautin ajiyar zuciyarsa"Toh zan jira har zuwa lokacin, Allah yasa inji alkhairi, yanzu sai yaushe zan sake yin magana da shi saboda bangaji da ganin sa ba" "Ka bani lokaci uncle, zanyi kokarin fahimtar da shi yadda zaiyi amfani da laptop din" "Okey, nagode my son, sannan ina mai baka hakuri amadadinsa" "Kada ka damu uncle, ay ba yin kansa bane rashin sani ne" kwantar masa da hankali Yaci gaba da yi har ya samu ya shawo kanshi kafin daga bisani su ka yi sallama zama yai gefen gadonsa zuciyarsa cike fal da tunanin abun da ya faru. _________________________ "Deeja! Deeja" kamar daga sama taji ana wala mata kira, firgigit ta ware idanunta masu auke da bacci ta sauke su kan ceilling da alama batasan daga ina ake kiran ta ba sai faman yafta yafta idanu ta ke Yi, fuskarta ta ca6e da jan bakin ta "gani anan tsaye ina kallon ki" wurga ido tai kan Unaisah da ke yi mata magana, tana a tsaye ta ru e qugu da hannu aya, wata hadaddiyar riga doguwa ta sanya a jikin ta black colour tabi shape dinta ba karamin kyau tayi mata ba, hada light make up akan face dinta, tayi rolling veil ga wani dadda an fragrance dake tashi Zumbur khadeeja ta mi e zaune fuskar a jagule take kallon ta "Sorry na katse maki baccin ki, safiya tayi tun azu, ga shi ko sallar asuba bakiyi ba, yakamata kije kiyi sannan ki yi wanka ko kin ji dadin jikin ki" Yamutsa fuska Khadeeja tay"to ke din wacece ne? Kin cika ni da surutu Ina yaya salsabeel da su rubina"? Murmushi unaisah tayi"Yar uwarki ce unaisah baki gane ni ba"? Harara ta jefa mata"ni bansan ki ba Allah, ki fadamin ina yan uwana suke"? Zuba mata ido unaisah tayi da alama zatai kafiya, don ma tasan halin kayan ta. "Yan uwanki suna nan a cikin gidan nan, amma waye ya kawoki akin mu jiya"? Sosa eya tayi kafin tace"harisuna, shine Ya rakoni in kwanta" "Okey yanzu ki tashi ki shiga ga toilet can" ta fada tare da an juyawa ta nuna mata kofar da hannu, saukowa tayi daga kan gadon tana mi a tare da hamma ta nufi toilet ta shige, unaisah nata bin ta da kallo har ta shige. "kin canzamin kamar ba deejana ba, naso ace kina acikin hayyacinki komai Ya faru nasan zakiyi farin cikin saurayin rayuwar da muka samu, Allah Ya baki lafiya my sister" Bakomai take tunawa ba, face ranar da giant ya tafi da khadeeja da kuma lokacin da aka dawo masu da ita taje gaban gadon ta tana shesshe ar kuka ta tada ta daga bacci taja ta suka shiga toilet har take fada mata abun da akayi mata bayan an auke ta Tuni taji jikinta yayi sanyi lakwas rayuwa kenan, babu wanda yayi tsammanin zasu kai wannan lokacin araye sai gashi Allah ya raya abun shi, dama ance wuya bata kisa sai in kwana sun kare. owa Dakin Haris Yayi, fuskarsa dauke da tsantsar farin ciki sai faman sakin murmushi Yake yi, ba don komai ba sai don zumudin ganin deejansa jiya da ita Ya kwana Aransa yanzu haka yazo ne don Ya ara ganinta ya kuma tabbatarwa kansa ba mafarki bane abun da Ya faru Jiya. Unaisah Na ganinsa Tace"ba sallama? Me ma Ya kawoka dakinmu da sassafe"? Shafa sumar kansa yai"ina deejana"? A an ru e tay pretending"deeja kuma? Kayi mafarki da ita ne"! Hankali atashe Yace"bangane me kike nufi ba, wani irin mafarki bayan jiya sun zo gidan nan har mu ka yi shagali, da kaina ma na rakota dakin ku da tace min tana jin bacci. Fuska adaure tace"haris? Ko dai ka fara samun ta6in hankali ne? Meya kawo maganar deeja? Bayan ta riga da ta rasu tun a prison"? Yanayin yadda tayi magamar ba karamin kayar masa da gaba tayi ba jikin shi yai sanyi gwiwarsa ta sage "Kina nufin mafarki nayi jiya" aga masa gira tay"zai iya yiwuwa" shiru yayi zuciyarsa ajagule yake kallon unaisah gaba daya so take ta rikita lissafin walwarsa .. "Lafiya ka tsaya kana kallona? Meke damunka ne"? walla ce ta ciko idanunsa muryarsa na rawa ya furta"deeja na ta mutu? mafarki nayi jiya sunzo? har ta bu e baki zata bashi amsa Kwatsam Deeja Ta banko kofar toilet din kamar an wurgo ta da karfi ta furta"Laahh! Haris kaine? Yana jin muryarta a ru e Yakai dubansa gareta lokaci aya ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, da gudu Deeja Ta nufe sa ta ame shi tana fadin"wallahi jiya har mafarkinka nayi harisuna" "Deejana Kin tashi lafiya"? Tana faman Washe Baki tace"lafiyalou wlh, nima muryarka najiyo ina ga daga Cikin toilet, Har na fara alwala na katse ta" Unaisah dake kallonsu tana dariya gaba daya mamakin aunarsu ya gama cikata, wani abu daya aure mata kai yadda deeja Ta yarda dashi bayan jiya sukai ta fama da ita akan ta tuna shi amma ta iya sai gashi da yake kaunar tasu a jini take har sun sha u jiya izuwa yau "Sister kada ki sake yi min irin wannan wasan, zuciyata zata Iya bugawa Allah" Yai maganar idonsa akan Unasah "Naji romeo, bazan araba, Yanzu sai kabarta ta koma ta karasa alwalar ko fa salla batai ba" Harara deeja ta watsa mata"waike ina ruwanki dani in ma banyi sallar ba, ay ni ba kullum nakeyi ba sai na ga dama, Ko su hawwa basu min dole balle ma ke da bansan wacece ba' muryarta da shagwa6a take magana hakan bakaramin dariya ya basu ba Lalla6ata haris yayi"rabu da ita, kishi takeyi da take don taga kinfi ta kyau, " washe baki tayi jin Yana yabonta "Yanzu ki koma ki karasa alwalar in kin gama ki yi wanka sai ki fito muje muyi breakfast" amsa mashi tayi da toh da gudu ta juya tana fadin Kada ka tafi harisuna ka jira ni in fito Yana murmushi ya amsa mata da toh har ta shige bai daina kallon ta ba Da zolaya unaisah tace"Hankali Ya kwanta Haris, deeja Ta dawo, No more heartbreak " dariyar farin Ciki Ya saki" ba zaki gane ba, wlh daren jiya bayan na rakota dakin ku ta kwanta dana koma dakinmu har nafila nayi saboda in nuna godiya ga Allah daya sake hadani da ita, Ina son deeja Allah Yabar mun ita har abada, in ma mutuwa zata dauke ni ta dauke mu atare" idanu abude Unaisah ke kallon shi aranta tunani take tsakanin deeja da haris da kuma ita da danish suwaye sukafi son juna tsakani da Allah? anya idan danish Ya rasata zaiyi ciwon zuciya kamar yadda haris yayi akan deeja? Ko kuwa ita idan tarasa shi zatai hauka? tabbas A yanzu bata iya