Sashe 197
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..." Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba. cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?" Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin ha ari, sai kuma mu tafi mu barshi? Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu. "Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon. Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..." da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke wala mashi kira ha i dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba tsammani ginin Kurkukun Ya fara Jijjiga kafin kace me tuni ginin ya fara tsastsagewa, hankalin Su commender ba karamin tashi yayi ba, akan idon su komai ke faruwa yayin da Chief kwata kwata bai lura ba saboda baya acikin hayyacin sa. wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, wasu irin marmarar duwatsun da akayi ginin ne suka fara 6a66akowa daga sama Kaitsaye suke rubzowa asa da wani sauti suka tartwasewa, duk wanda kuwa tsautsayi yasa suka afkwa kanshi tofa Ya tashi aiki. Chief daya rikice bai kaiga isa hall din ba, Wani Gingirimeman dutse Ya yanko mai girman gaske Gaba daya ya zube asa, ya shiga tsakanin chief da hall din, ras gaban shi ya fa i ya zare reddish eyes dinsa sam ya kasa motsawa, Wlh zuciyarshi ta gama karaya ya riga daya fidda rai da Danish. Saboda ya rude kokari yake ya nemi hanyar da zai bi ya karasa ga hall din, wani ginin ne ya zazzago daga saman ceilling din dayake batare daya ankara ba, Cikin zafin nama commender james Ya dam i damtsen hannun shi ya jefar da shi gurin Su captain da sauri Suka rurruke shi Yana kuka Yana kokarin fisge kan shi daga hannunsu ahaka suka sanya karfi gurin ingiza shi. bawan Allah sai waiwayon ginin hall din daya rushe yakeyi..Yana ji Yana gani ahaka suka tafi da shi kamar yayi hauka sai sambatu yakeyi _tun da na fara aiki ban ta6a faduwa ba sai yau da nagaza taimakon ka, Naji kunya Danish, i'm a looser, ka sani ba kai kadai bane danish, Kana da Allah kuma kana da dani, Danish bazan bari ka mutu ba, zan dawo Danish, zan dawo dole na aukar maka fansa.......... (Finally Su Chief Sun yi nasarar fita daga kurkukun kaddara bayan kalubalen da suka fuskanta) *__________________________ELDERS A zazzaune suke kan Sofas cikin wani Daki mai duhu, saika kura ido zaka Iya ganin su da taimakon wutar Candles dake Ci, round table din dake agaban su shake Yake da kwalaben Giya sun sha sun bugu har ta kai masu karo. Idanunsu sun ka a jawur kamar jan gauta, fuskokinsu babu annuri ko miskala zarratin basu taba fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba, sunyi babbar asara ba ka an ba..... "Sune na farko da suka fara kawo mana farmaki! sun latata ginin da nayi wahalar kafawa tsawon shekaru! Sun san komai da muke aikawata, sun san sirrin mu, sun gani da idanunsu, sun kuma kashe rabi da kwata na Giants din mu, bayan irin 6arnar da sukayi mana na, sun 6ata shagalin black Night, sun kashe dubban matsafan da basu ji ba basu gani ba..." ya fa a yana jan numfashi cikin fushi, kafin ya daura da cewa"hakan bai ishe su ba, sai da suka kwashe Fursinoni da muka raina tsawon shekaru don mu amfana da su, sun tarwatsa duk wani shirin mu" "Yaron da muka raina da hannun mu don ya zama garkuwar mu yaci amanar mu ya koma garkuwar su, tsohuwa Tamira da Salsabeel haka suma suka ci amanarmu, abunda yafi karya min zuciyata, wadda na dam a ma yarda ta da amanata, hada ita cikin wa anda suka bada gudummuwar kawo mana farmaki! meke shirin faruwa da mu ne? Meyasa wa anda muka yarda da su suke cin dunduniyar mu"? bai karasa maganar ba Yana huci Ya aga kwalbar giyar dake a hannun shi Ya rotsa ta kan table din gaban shi nan take ta tarwatse. Ran Elder yayi mugun 6aci, a wannan gabar komai zai iya faruwa. Hankulan sauran Elders din ba aramin tashi yayi ba, wata irin kururuwar ihu Ya fasa tare da tallabe kan shi da tafukan sa. Lallashin shi suka fara yi cikin kankan dakai da girmamawa dakyar suka shawo kan shi. Gyaran Murya Jan harshe yai kafin ya furta"Karaya ba tamu bace, Ba'a san elders da rauni ba, har yanzu muna da damar da zamu Iya dawo da ran kurkukun addara...." bai are maganar ba, Elder Yana huci Ya tari numfashin shi da cewa"tayaya zamu iya yin hakan? Bayan sun riga da sunsan komai, sanin ka ne muddin wani yasan sirrin inda muke yin tsafinmu abu na farko da zai faru lalacewar ginin kuma ya riga daya faru, abu na gaba shine karyewar sihirinmu In har hakan ta faru cikin sauki zasu shafen tarihin da muka da e muna kafa shi...."gaba daya sukayi shiru suna sauraranshi, da alama sun kadu sosai. dakatawa yayi da yin maganar wani irin kululun bakin ciki da takaici ne ya tokare makoshin shi"a matsayin mu na mashahuran da duniya tasan da zamammu, abun kunyane asan me muke aikatawa, Ina jin tsoron mu rasa kimarmu da darajarmu fiye da yadda nake jin tsoron mutuwata, mutuncinmu zai zube a idon duniya, girmamamu da mutane suke yi suna ganin martabarmu zai tashi abanza, daga nan basai nayi maku bayanin abun zai faruwa ba, kun riga da kunsan sakamakon bazai ta6a yin kyau ba..." ya fada yana binsu da kallo daya bayan daya. bakowane daga cikin su ya karaya ba, shi dama Elder mutunne mai wata a ida tun fil azal baya son duk wani abu da zaisa mutuncin shi ya zube yana girmama imarsa. muzkutawa Jan le6e yayi kafin da wata irin muryar mai tattare da zafin fusata Yace"garkuwar kurkuku Ya zama garkuwar Fursinoni, addarar kurkuku ta zama mummunar addara agare mu, babban kuskuren da muka tabka shine barin tsohuwa Tamira da ranta, a lokacin da muka kashe Habibulllah, da mun sani mun ha asu duka mun kashe su, shima garkuwarmu da ace bamu kawo addara gidan kurkukun mu ba, nayi imanin bazai ta6a cin amanar mu ba" ya an dakata da yin maganar yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa"ita kuma Khala Elder Kayi hakuri da abunda zan fa a, tunkafin zuwan wannan lokacin saida muka baka shawarar ka kasheta saboda ita din tana da kyakkyawar zuciya kuma tana yamatar abunda muke aikatawa amma saboda kaunar da kake mata, shi yaja har ka gaza Yanke mata hukuncin daya dace" Cike da danasani Elder ya sunkuyar da kan shi asa, tunda suka fara magana, Jan wuya Yana a kishingide Yana binsu da kallo babu alamun ka uwa atare da shi, shi kuwa Jan kunne kamar yafi su shiga damuwa dama duk cikinsu shine mai raunin zuciya. Jan Ido Yace"kada ku bani Kunya, duk wani abu daya faru ya riga daya faru, Mu fa Elders ne, babu wani mahalukin daya isa yaga bayan mu, abun nawa muka aikata bamu ta6a karaya ba sai wannan lokaci don kawai wasu kananun kwari sun kai mana farmaki? Rai nawa muka salwantar? Ya fada cike da gadara. "sai wadannan zasu gagaremu! In har muna so mu dawo da karfin ikonmu dole mu bi abun da allon tsafinmu ya nuna mana, dole mu aiwatar saboda itace dama takarshe da ta rage mana wadda zamuyi amfani da ita gurin dawo da ran kurkukun addara" Ya fa a tare da dan dakatawa yana dubansu"a wannan karon dole mu cire sonkai atsakaninmu, bi'amana mu kashe duk wanda Yasan sirrinmu koda mafi soyuwa ne agaremu..." sarai Elder Ya fahimci da shi yake magana. "ita kuma dama ayan nan data rage mana itace mu cire Zuciyar Yarinyar nan, Mu ba dodon tsafin mu Ya handame ta, sannan mu kashe addarar kurkuku, ta hakane ka ai gidan kurkukun addara zai farfa o...." wata irin mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, ganin har yanzu suna da saura damar da zasu cigaba da aiwatar da shaidancin su. Cike da izza Jan wuya yace"abun farin ciki, Garkuwar da suke ta ama da shi, Ya rasa ranshi saboda shi wawane shashasha, Ya sadaukar da kanshi saboda ya basu kariya, duk da muma munyi babban rashi amma wannan duk ba wata matsala bace da zamu daga hankalinmu akai, Ni ta inda najiye mana dadi gaba dayansu wadanda suka san sirrinmu basu san fuskokin mu ba, tayaya suke tunanin zasu iya yin nasara akanmu? In banda ma sudin dakikai ne iya fa sunayen mu suka sani, sai kuma sirrinmu amma azahirin rayu basu san su wanene Elders Ba...." Maganar Jan Wuya ta faranta masu rai, ganin sun samu mafita... "Yanzu wanene Zai kawo mana Yaran?" Jan harshe ne yayi tambayar, Cike