← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 137 OF 247

Sashe 137

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

amsa mata har ta juya zata fuce daga dakin muryar baba obie ta dakatar da ita. "Ya jikin marwa"? "Da sau i baba," "Okey, ubangiji Allah ya bata lafiya" ta amsa mashi da ameen bayan ta fuce daga dakin chief ya dubi baba obie"wacece marwa"? Ba halinsa bane tambayar abunda bai shafe shi ba, just saboda yaji ya ambaci ya jikin ta. aya daga cikin masu aikin gidan nan ce, bata da lafiya" iya abunda ya fada masa kenan saboda baison ya aga mashi hankali, kamar yadda su twins sukai hijra saboda kyamar marwa. "Allah ya bata lafiya" ya amsa mashi da ameen Tea pot baba obie ya dauka ya tsiyaya masu shayi a kananun kofuna suka dauka suna sha "Ka tambaye ni dangane da maganar da nace maka inaso muyi ko" aga mashi kai yai alamar eh "Nasan bazaka ji dadi ba, amma kada ka hanani tafiya" janye cup din hannunsa yai daga kan lips dinsa"tafiya zakayi"! Jinjina mashi kai yayi"lagos nakeson zuwa gurin aminina, kasan na da e ban ziyarce shi ba, kuma shi yana kokarin zuwa akai akai ya dubani har gida" jinjina kai chief yai"yaushe ne zaka tafi"? "Karshen watan nan, 3 weeks zanyi in dawo" aure fuska chief yayi"har sati uku baba, ina laifin one week" murmushi yayi"dama sai da nayi fargaban fada maka nasan da wuya ka kyale ni, indai bazaka barni ba to saidai muje atare" girgiza kai chief yayi"ba zan iya binka ba, naso muje atare amma ayyuka sunyi min yawa, amma fa bazan bari ka tafi kai kadai ba,"! Yamutsa fuska baba obie yai"to ni da wa zan tafi owais? Kowa yana da aikin yi, bana son in takura masu" Shiru yayi jim kafin yace"zanyi magana da pravin, ya auki hutun aiki Ya bika ku tafi, don gaskiya ni bazan bari ka tafi kai kadai ba" "Haba owais kamar wani karamin yaro, sai kace bakasan wanene kakan naka ba, wa annan kafafuwan nawa ba inda basu taka ba, har birnin sin sunje, nafa yi yawan duniya fiye da tunaninka, tun ina matashina nake fita kasashen waje ni kadai abuna." Murmushi chief yayi"da da yanzu ba aya ba, ka manyanta sosai ga tsufa, shiyasa nake tattalinka bana son wani abu ya same ka, duk da nasan Allah ke tsare bawansa." kalaman chief sun kara faranta ranshi murmushi yayi yana kallon fuskar shi"anya akwai wanda yakaini dacen jika a duniyar nan"? chief yace"ni yakamata nayi wannan tunanin, cos bana tunanin akwai wanda yayi dacen kaka irina, ina alfahari dakai," dariyar farin ciki baba obie yasaki idan owais na yabon shi dadi yake ji kamar ya zuba ruwa kasa ya sha. "Owais Mu fara cin abincin nan kada ya huce.." Chief ne yayi serving dinsu atsanake suke cin abinci ya lura duk dagowar da zaiyi sai sun ha a ido da baba obie wani kallon so da kauna yakeyi mashi. "Naga kana kallona, ba zan canza maganata ba, zanyi magana da pravin din atare zaku je nasan zai baka kulawa ta musamman kuma zai dinga sanar dani duk wani motsinka" dariya baba obie yayi"oh an leken asiri zaka hada ni da shi kenan" aga mashi gira chief yayi"bakomai nasan saboda kaunar da kake yi min ne, naji na amince muje atare da shi din" ya fada yayin da yake tura abinci abakin shi. Knocking room door din akay daga waje, baba obie yace shigo ciki" muryar hajiya saratu ce ta katse masu cin abincin nasu, atare suka dago suna kallonta, shugowa tayi jikinta sanye da swiss code lace, idanunta sanye da farin glass, ta aza veil a kafadarta, ta kashe daurin ture kaga tsiya, hannunta na aruke da handbag dinta. Kwata kwata babu annuri akan fuskarta saida taga chief ta an saki fuskarta. "Shalelena barka da safiya, har anyi shirin xuwa office.. " murmushi ta sakar mashi"barka da safiya babana, ina fata ka tashi lafiya" tay maganar tare da samun guri ta zauna tana fuskantar su.. "Lafiyalou auta," "Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"? Yace"Alhamdulillah" "I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi. "She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya" "Masha Allah, naji dadin jin hakan" tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa. gaba aya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya fa a yana kallon su Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba? Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani an arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa" tattausan murmushi sukayi Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta fa a tana kallon shi "Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu. "Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa" A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu. ewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"? "I'm sorry, Grandpa. I'll come back later" ya fa a tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata. Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba. "Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi. "Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan. Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? aure fuska tayi Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara le awa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya fa a da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba. "Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta ha e rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su. "Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. " Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata mi e da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a... Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman ha e rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi. Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba. "Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba" "Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi
Chapter 137 · 0% Book details