← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 198 OF 247

Sashe 198

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

da isa Jan wuya yace"kubar komai a hannuna" tuntsirewa suka kuma yi dariya hahaha _________________________________ Shin Ya Labarin Tsohuwa Khala *Bayan wani lokaci* Farfa owa tayi daga dogon suman da ta yi na tsawon awanni, A hankali ta bu e idanunta wani irin duhu ne ya mamaye ganin ta, tana arin motsa jikinta taji kamar an daddaureta. gumin zufa ne Ya wanke fuskarta, bata gama wartsakewa ba sai nishi take yi tana jan numfashi.. takun tafiyar mutun taji a cikin kunnanta yana tunkaro ta, cikin disasshiyar murya ta furta"wanene"? Kakkausar murya Elder ce ta razanar da ita yayin daya furta"me nayi maki dana cancani cin amana daga gare ki" Shiru tayi bata furta kalma ba, Hankalinta dai idan yai dubu toh ya tashi, zuciyarta sai dakan uku uku take tasan yau sai buzunta, mai kwatarta a hannun Elder sai Allah. A hankali Hasken fitilun dake saman ceilling din akin ya haskaka ko'ina tana a zaune kan Kujerar arfe, a rude take kallon igiyar kacar da suka aure jikinta da ita, ko yatsanta bazata Iya aga wa ba, Da sauri takai dubanta gare shi yana a tsaye Ya juya mata baya, tun da taganta adakin da suke hukunta wanda yaci amanarsu na gidan kurkukun kaddara Ta tsinci kanta da jin matsanancin faduwar gaba, ga wasu karfafan Evil giants data hango tsaye abakin kofar dakin.. "Tun da naga irin makaman da sukai amfani da su gurin kashe giants nasan cewa koma wanene ya basu makamin acikin mu yake, saboda mu kadai keda irinsu acikin gidan kurkukun nan ake era su, bakowa yazo min araina ba face ke dama kin jima kina gaya min zaki dauki fansa akaina" Cike da karfin Hali tace"banyi mamakin abun da kayi min ba Elder, Ni angaya maka bani da zuciya a kirjina ne? Taya kake tunanin bazan ci amanarka ba? Dama akwai amana tsakaninmu? Kaida ka rabani da kowa nawa, har kana da bakin furta naci amanarka? Akwai maci amanar daya wuce kai mugu, Hakanan kawai saboda nasan sirrinka bisa kuskure ka rabani da dangina, ya'yana, Jikokina, ka kafe ni da asirinka cikin kurkukun nan." idanunta jawur ta fa a yayin da hawaye ke shararowa kan kuncin ta..ta daura da cewa "tun lokacin dana nasan sirrinku, a ranar na daukar wa kaina alwashin saina yi silar Tonuwar asirinka, kowa yasan wanene kai, da miyagun ayyukan da kake aikatawa, shiyasa na dinga satar makamanku ina boye su saboda tanadin zuwan wannan ranar" bata are maganar ba, Taji Ya she e da dariya, cike da izza Ya juyo ya fuskance ta, batare daya furta kalma ba, gently yake jujjuya sandar hannun shi. "Dariyarka ta bazance Elder, Ni nasan Ayanzu haka an hanjin cikinka ka awa sukeyi saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya, Na kunsa maka bakin cikin da har abada ba zaka manta ba, naja maku babbar asara, koba komai Yau kaga wadanda suka fi karfinka" ta fada da murmushi akan fuskarta. Wata Yar iskar dariya Ya saki, Kafin Ya furta"dame kike takama ne? Da ido Ta nuna mashi sama tace"Allah, shine abun tin ahona, koken dana da e ina kai mashi akanka Yau ya amsa addu'ata, daga Yanzu ka kasance cikin shiri akowani yanayi mutuwa zata Iya riskarka, zaka wukalanta ka zama kaskantacce, kimarka da darajarka zasu zube a idon duniya....." bata are maganar ba Elder Ya buga sandar hannunsa ta daki asa har saida ura ta tashi, wani irin radadi taji acikin kanta hakan yasa ta dakata da yin maganar. Yana Huci Yace"kina tunanin kinyi nasara akaina ne? Bayan Duk wani shirinki Ya tashi Abanza, wadanda kike takamar zasu ga bayan mu a yanzu haka babu ko daya acikin su, duk sun mutu a hannun giants din mu, suma fursinonin da kika ku6utar basu tsira ba zamu kashe su ne" Wani irin faduwar gaba taji arazane Ta furta"kana nufin Danish da Owais sun mutu su ma" jinjina mata kai yayi" gaba daya sun mutu...Don haka kidaina farin ciki, saboda haryanzu baki kamo hanyar da zaki ga bayana ba, kashe Elder ba abune mai sauki ba, Ita kanta mutuwar tsorona take ji..." a gadarance yai maganar. ta ki ima da jin maganar shi, idanunta cike tab da kwalla ta furta"saboda shafewar basira da jahilci kamanta kafin kai anyi wasu azzaluman da suka gabata yanzu duk suna ina ? Ta jefa mashi tambayar bai furta kalma ba. "mutuwa bata tsoronka Elder Lokacin ka ne baiyi ba, Allah yana sane da duk wani abu da kake aikatawa dama ce ta dan wani lokaci kuma kajira ka gani wlh karshenka bazai kyau ba" ta fa a tana sharar kwalla "kuma karya kake min, Danish dina bai mutu ba, owais dina ma bai mutu ba ina ji araina suna araye..." Fashewa yayi da dariya"ki yarda ko karki yarda matsalarki, Kina kurarin kin tona asirina, bayan Har yanzu asirina arufe yake saboda babu wanda yasan ainihin Elder, ko fuskata basu sani ba, taya zasu iya tona min asirina? Bayan Ko tuhumata basu isa suyi ba saboda basu da wata shaida...." ya fada yana sakin dariyar shakiyanki. ranta a 6ace ta furta"ni zan tona maka asiri..." ta fa a tana huci. Da bu ar bakinsa sai cewa yayi"kin ta6a ganin gawa tayi magana"? Cike da tashin hankali ta zare ido tana kallon shi, matso da fuskarshi yayi saitin tata"Oh wai kina tunanin zan barki araye? Bayan kece kika san su wanene Elders, Ko da can da kika san sirrina nabarki araye nayi danasani da ban kasheki ba, da nasan zaki zamarmin masifa da tuni najima da fille kanki...." gaba daya tabi ta rude da jin maganar shi muryarta nawa ta furta"kada ka kasheni, Kabarni da raina, Ina son naga ya'yana da jikokina, Ina so na koma gurin dangina, ko dan son da kake min da zaman amanar damukayi da juna ka kyaleni da raina.." Girgiza kanshi yayi"ke da ganin su, Sai a lahira, nasoki tamkar raina amma tunda kika nunamun tsantsar kiyayyar da kike min naji nima kin fita araina, Inasonki amma nafi son mutuwarki ayanzu idan nabarki zaki zamarmun annoba" Ya fa a tare da dafe saitin zuciyarshi, batay mamakin ganin hawaye da suka cika idanun shi ba.. "bazan ta6a son wata halitta kamar yadda nasoki ba, nasan zanyi bakin ciki da takaicin rasaki arayuwata, zanyi maraicin rashin ki, zan dawwama da radadin kashe ki da zanyi, Bazan ta6a yafe maki abunda kikai min ba, kece silar komai, Kin Ci amanar kaunar dake atsakaninmu, meyasa tun farko kika tsananta bincike akaina? Meyasa Kika san sirrina? Kinyi silar lalata Farin cikin rayuwarmu, kema kin sani nasoki fiye da yadda nakeson kaina...." zubewa yayi agabanta kan gwiwowinshi...sosai ta fashe da kuka cikin karyayyar murya ta furta"komai ya faru mukaddarine daga Allah, sirrinka dana sani Allah ne Ya kaddara zan sanin, shiyasa har nasan komai, da ace kai musulmine kayi imani da Allah da ka gane abunda nake fa a maka.. "duk yadda na karya maka zuciya bai kaiga yadda ni ka karya min tawa ba, ina farin ciki na auri miji nagari mai sona da bani kulawa ashe mugun mutum na aura, da kanka ka musuluntar dani ashe kai din kasungumin arnene matsafi da baiyi imani da Allah ba, sannan ka ciyar damu haram, wlh ko bayan ba raina sai Allah ya tona asirinka, in sha Allah Elder saika yi kaskantacciyar mutuwa, duniya gaba daya zata juya maka baya, komai daka mallaka zai lalace.." bata kare maganar ba, Ya zabura Ya mike tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki...tuni ta hadiye maganarta, Hankalinta atashe take kallon shi. Giants in dake abayanshi Yaba Umarnin su aure mashi afafuwanta da igiya jikin fankar dake li e saman ceilling din dakin, fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita ita ba mutuwar take tsoro ba, abu biyu take ma bakinci zata mutu bata tona asirin Elder ba, abu na biyu zata mutu bata gana da ya'yanta ba bayan tsawon shekaru ashirin da Ya garkameta akurkukun basu san tana raye ba. tana ji tana Gani, giants din suka kwance igiyoyin da suka daureta a jikin kujerar, daya ya ruketa sai kuka take tana kallon Elder Ya saddar da kanshi kasa don baya son raunin zuciyar shi ya hana shi kashe ta. a jikin fankar Suka aure kafafuwanta gangar jikinta da kanta suna kallon asa, Da ido yayi sihiri Nan take Kasan inda kanta ke kallo ya wawake ya zama katon rami wata irin wuta mai balbali ta kama ci...lokacin da hucin wutar Ya fara ta6a kanta, wani irin azababben kuka ta fashe da shi kamar ana zare ranta, wani irin radadin azabane ke rabar kowani sashe na jikin ta, cikin shesshekar kuka Ta dinga yi mashi magiya akan ya kwance ta, Kada ya kasheta ko dan darajar ya'yan dake tsakaninsu amma saboda rashin imani irin na Elder cikin sauri Ya juya Gints suka rufa take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta. Ita kadai baiwar Allah ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle tace zata kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta. sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar daukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke da alama dai Khala rai yayi halinsa, wutar harta rufe ta....Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un ____________________________________ After One week (bayan sati aya dakai farmaki Gidan Kurkukun addara *DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ~__________________________~ After One week (bayan sati aya dakai farmaki Gidan Kurkukun addara Hankalin Unaisah ba aramin tashi yayi ba, Jin shiru har tsawo sati aya basu dawo ba, lamarin Ya aga hankalin ta ba kadan ba, dauriya kawai takeyi kamar yadda tayi ma su alkawarin zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci. Abu aya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci
Chapter 198 · 0% Book details