← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 73 OF 247

Sashe 73

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 4 min read

su mamin"? "Alhamdulillah, muna nan lafiya lou" "Ina jikan nawa ko har anyi bacci" "Yayi bacci tun azu" "Allah sarki nayi missing nashi, Ya maganar zuwan naku? "In sha Allah, cikin week din nan zamu zo" "Allah yakaimu lafiya" ta amsa mata da ameen daga bisani sukayi sallama taso ta fada ma hajiya adama zancen dawowar benazir amma ta bari sai benazir in tazo gidansu sai ta kira ta awaya suyi magana don ta bata mamaki, murmushi tayi tare da ajiye wayar kan nightstand, ta janyo junaid on her chest ta rungume abun ta. _________________________________ _Dare Mahutar bawa, sai dai bakowa ne ke samun kwanciyar hankalin runtsawa a cikin sa ba, saboda akwai wanda ya manta yaushe rabon da idanunsa su runtsa saboda rashin kwanciyar hankali_ GIDAN KURKUKUN ADDARA Daki ne madaidaici mai fadi da tsayin gaske, irin ginin dutsen nan ne dayai shekara aru aru, daga saman dakin fitilun kwai ne guda uku masu haske idan ka kalli bangon dakin ta ko'ina jirwayen jinine da ya daskare, kai harta iskar dakin ta gauraya da karnin jini da warin jikin mutanan dake rayuwa a cikin sa. Matasan an matane zazzaune kan gadajen arfe, kowaccen su tana asanye da guntuwar riga launin ja wadda bata rufe gwiwar afarsu ba sun rame sun anjame fatar jikinsu duk sahun yakushi da kurajen fata kai gaba dayansu sun ko e baka gane fari acikin su saboda duhun da fatarsu tayi wanda bakomai ne yajawo hakan ba face u ubar da suke fuskanta, wadannan bayin Allahn babu irin tashin hankalin da ba su gani ba sunga bala'e da masifa tsirararsa, gaba daya an salwantar da rayuwarsu, tun lokacin da aka kaddara masu rayuwa agidan kurkukun addara amfani ake da su kamar injina, babu wani sassauci. gaba ayansu babu wacce ta haura shekara sha bakwai dukansu matasan an matane gwanin ban tausayi, dukkan gabban jikinsu sun raunata, ko tafiya ba su iyayi sai dai adauke su akai su inda za'a yi amfani da su in angama a dawo da su zuciyarsu da fargaba take bugawa, numfashin su da tashin hankali suke buso shi, idanunsu sun kumbura suntum sun afe saboda tsabar kukan da suke sha wanda tun sunayi hawaye na zuba har takaiga ruwan hawayen sun daina fitowa sai dai kukan zuciya mai acin gaske, basu da wani burin dayawuce Allah Ya dauki ransu su huta. Biyo bayan da Garkuwa Ya gudu tare da wasu daga cikin prison ha a ran Elders yayi mugun 6aci matu a sun harzu a evil heart dinsu ta hasala, wanda silar hakan Yaja suka fara azabtar da sauran prisoners dake agidan kurkukun addara, babu imani ko miskala zarratin yanzu ko abinci mai dadi babu a gidan kurkukun addara babu wani jin dadi ko na da a sai ba ar izayar rayuwa, Allah ne kadai Yasan adadin jinin da suka zubda na yaran da suke raino, da kuma Yaran da suka gur6ata ma rayuwa, wani shiri suka fara yiwa kansu saboda suna hasashen akowani lokaci za'a iya kawo masu farmakin bazata, kuma suna da tabbacin asirin su yana dab da tonuwa, basu ta6a fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba!! _Zaman tattaunawa sukayi a karo na biyu a dakin sirrinsu wanda a lokacin suka yanke shawarar za su ba aya daga cikin Evil giant in da suke da su horon zama prison shield saboda asamu wanda zai maye masu gurbin Garkuwar su da suka rasa saboda sun fahimci yayi masu nisan kiwon da ba zasu iya tan wara shi ba, da bu atar su samu wanda zai zamanto abokin karawar Garkuwa, saboda a halin Yanzu Idan aka kawo masu farmaki tare da shi to kuwa tabbas za'a ci galaba a kansu tun da babu wani giant da zai Iya karawa da shi idan ba su elders din ba, amma Idan suka gurfanar da sabon Giant din su mai ru e da mukamin prison shield zai yi wuya a iya rusa su in ba wani iko na Allah ba, sannan shi wannan giant din zai iya aikata duk wani rashin imani da suke so, ba a halicci zuciyarsa da imani acikin ta ba, ba in mugune kuma azzalumin mutun ne shu'umi mai hadarin gaske, baisan menene tausayi ba, kurma ne sannan makahone bayaji baya gani in ba umarnin ubayen gidansa ba wato Elders, Shi fa wannan giant din baida mararraba da bakin shaidanin Aljani saboda sune suka rinjayi halittarsa ta an adam_
Chapter 73 · 0% Book details