← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 135 OF 247

Sashe 135

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

su, Ya shige toilet da su, Allah kadai Yasan meya yi masu, jim ka an Ya fito da robobin a hannun shi yana faman sakin shu'umun murmushi ya aura su kan mirror. Kafin ya fita daga dakin saida ya fara hawa gadon Ya sumbaci la66anta kafin ya sauko shaf shaf ya maida kayan jikin shi ya juya cikin takun tantirai Ya fuce daga dakin. Fitar shi keda wuya hajjaty ta fara mutsu mutsun farkawa daga bacci, wata irin kasalace ta mamaye jikinta dakyar ta lalla6a ta mi e ganin babu sutura ajikinta yasa tayi saurin kai hannu ta janyo towel dinta ta lullu6e jikinta, muryarta adisashe ta fara ambaton sunan shi shiru taji bai amsa mata ba alamar baya adakin, lumshe idanu tayi tare da jingina kanta jikin headboard, A hankali take tariyo abunda ya shiga tsakaninta da pravin wani irin shaukin son shi take ji, dai dai da minti aya bata ta6a gajiya da shi ba, saboda soyayyar gaskiyace a tsakaninsu, bata ta6a ha a son shi da wani ba. Tunawa da marwa yasa tay saurin saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, donta tsarkake jikin ta, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta feshe jikinta da turare, ta yafa mayafi akanta, da sauri ta dauki robobin maganin ta tura su cikin ledar da aka kawo su, ta fito ta nufi dakin marwa, da sallama ta shiga dakin fuskarta dauke da murmushi take kallon marwa dake akwance kan mattress ta rufe idanunta. Zama hajjaty tay gefen katifar ta ajiye jakar agaban marwa. "Sannu marwa ya jikin naki? a hankali ta bu e idanunta wa anda suka ka a jawur ta dubi hajjaty, dakyar ta kakaro murmushi tana kallon ta tayi kyau abunta, azu da safe hajjaty ta taimaka mata tay wanka har kaya ta canza yar doguwar rigace a jikin ta, jikinta sai kamshin turaren da hajjaty ta fesa mata yakeyi. "Sheikh imam ya aiko da maganin ki," ta fada tare da ru o kafadun marwa ta taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta jikin pillow "Kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a, "Dama nasan ba lallai kiji yunwa ba, saboda dazu kin cika cikin ki da abinci" ta fada yayin da take bude murfin robar farko mai auke da sunan zam zam.. "Kiyi bismilla ki sha, kur6a aya zakiyi" aga mata kai tay alamar toh Lokacin data kurbi maganin kiris ya rage ta amayar da shi saboda zaurin da ya buso hancin ta. Lura da yanayin ta yasa hajjaty cewa"am sorry halan maganin bai da dadi? aga mata kai tay alamar eh Saurari Littafin Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. "Eyyah sai kin daure,kinsan yadda magungunan gargajiya suke akwai aci, wani zakiji shi da bauri wani kuma tsami" ta fa a tana yamutsa fuska, bayan ta kammala bata magungunan, tace"wannan ayan daya rage, a cikin ruwan wanka za'a iga maki shi, zuwa anjima in sha Allah zan sake dawowa, sannan pls kada ki manta kiyi evening azhkar" tun da ta fara magana marwa keta kallonta so take ta fa a mata wani abu tarasa taya zatai mata magana daga ta yunkuro zatai magana sai ta kasa saboda muryarta babu dadin ji Hajjaty sam bata lura da hakan ba, bayan ta maida robobin maganin a cikin ledar, ta ajiye gefen katifar marwa"ni zan tafi, da anjima zan shigo kawo maki dinner" ta fada tare da sakar mata murmushi ta mike ta tafara tafiya har ta kusa fita kunnuwanta suka jiyo mata marwa dake ta kokarin yi mata magana. Juyowa tay tare da kallonta da alamun rudani akan fuskarta, da hannu take yi mata alama, hajjaty ta kasa gane me taje nufi, ita dai taga marwa sai nuna mata dunkulallun yatsun hannunta takeyi "Marwa akwai wani abu da kike bukata ne"? aga mata kai tay alamar eh, komawa tayi gaban katifar ta zukunna tana kallonta, ruwan hawaye tagani kwance akan fuskarta"pls ki daina zubda hawayenki dan Allah, ki fadamun abunda kike so zanyi maki" da hannu marwa ta dinga goga floor tana kokarin kwatanta mata abunda take so ta dauko mata sai dai takasa fahimtarta Saurari Littafin Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. "Marwa kiyi hakuri, wallahi bansan me kike nufi ba" bu e baki marwa tayi ta fara mata gura gura.. tsoron maganarta hajjaty take ji nan take ta tuna da maganar pravin dayace mata ita bata tsoron marwa ta goga mata lalurarta, tuna wannan yasa tay saurin mikewa gabanta na faduwa ta fara ambaton sunan Allah acikin zuciyarta. Cikin rawar murya tace"marwa sai anjima zan dawo in sha Allah" da sauri ta fuce daga dakin, marwa ta kifa kanta cikin pillow ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tamkar ranta zai fita ________________________________ *(AFTER 3 DAYS BAYAN KWANA UKU)* A kalla yau kwana uku kenan da zuwansu Anila gidan hajiya adama, har ila yau ba su ara jin duriyar Ana ba, babu ita babu labarin ta, abun ya aga hankulan mutanan gidan sun damu da rashin ta, kusan kullum sai anila da mahboob sun kira layinta a switched off suke samun shi, Lamarin ya aure masu kai, basu da wata hanya da zasu Iya tuntu6ar wani nata, saboda ba su ta6a kar6ar layin yan uwanta dake a joss ba, abu biyu ya ha e ma Aneelerh ga damuwar halin da junaid yake a ciki, kwata kwata baya sakin jiki da kowa ga iwuya bai yarda da kowa na gidan ita kadai yake manne mawa, kuma har yau ya i bu e baki ya tanka mata ya zama kamar kurma sai dai yabi ta da ido ko in yana jin yunwa sometimes yana bude baki ya furta kalmar yunwa, wani abu daya fi daure mata kai idan dare yayi zasuyi bacci ta rungume shi a jikin ta, sai ya dinga firgita yana sambatu kwata kwata bata gane me yake cewa. Har su mami ta sanar ma abunda yakeyi suka ce taci gaba dayi mashi addu'a in sha Allah zaiji sauki, ita dai hankalinta bai kwanta da yanayin shi ba, ranta yana bata wani abu ba dai dai ba agidan dole akwai wani abu daya faru wanda yayi silar guduwar Anah da kuma rikicewar baby junaid! Kwana biyu da baije school ba sai ga kira daga class master din su junaid, bayan sun gaisa da anila ta ta tambayeta meyasa kwana biyu junaid baizo school ba, tace mata baida lafiya ne amma idan yaji sauki zai cigaba da zuwa Saurari Littafin Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. Cikin kwana uku anila duk ta fita hayyacinta har fa awa tayi saboda damuwar rashin Ana da kuma halin da baby junaid yake a ciki, abie har kiranta yayi shi da uncle dan iya da su ummu suka taru akanta suka yi mata nasiha cikin lallami da lallashi donta kwantar da hankali saboda kowa ya fahimci bata acikin nutsuwarta, ko abinci sai zahra tayi dakyar take samu ta ci ta zama abun ban tausayi daga ita har junaid din harma kwara ita akan shi saboda ya takura kan shi ya kuma takura mata ya hanata sukuni ko toilet zata shiga sai ya sanya rigima zai bita, dakyar take samu ta lalla6a shi da wayarta don yayi game kafin ta samu ya kyale ta, idan salla zatayi sai dai ta goya shi abayanta, har yau babu abunda ya canza, yanzu girkin gidan ya dawo hannun mami da ummi saboda rashin Ana, zahra kuma ba azaune take ba, tana zuwa aiki, ita kuma anila kota nemi su bata ta tayasu aiki sai suce taje taji da junaid zasu kula da komai... ________________________ Shin Ya labarin Benazir? Ay tun ranar da suka dawo gida ta kasa ta tsare tana jiran taj da Angel su dawo daga kasuwa, shiru shiru taji basu dawo ba har marece ya nutsa hankali atashe tace ma hajiya layla ta kira mata layin taj awaya taji meya hana su dawo! Hajiya layla tana yan kame kame tace mata ta manta bata da layin taj, kuma dayazo asibitin daukar Angel bata kar6a ba, sai dai ko dr shureim watakil shi yana da layin shi, ko da ta yi ma dr shureim magana akan ya kira mata taj cikin rashin kwanciyar hankali ya kira wrong number da gangan saboda ta tsare shi da ido tana jiran shi ya kira mata mijin ta, a dole yayi pretending ya ci gaba da magana yana fadin pls taj marece yayi ga benazir tana jiran ku, dan Allah ku dawo hakanan okey toh sai anijima Allah ya dawo daku lafiya, bayan ya katse kiran yace mata tayi hakuri ta kara jira suna akan hanya, baiwar Allah jiki asanyaye ta zauna kan sofa tana jiran dawowarsu, hankalinta kwata kwata ba a kwance yake ba, gani take kamar bazata sake ganin angel din ta ba... Abu kamar wasa har dare yayi babu taj ba angel, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, lokacin da zasu yi dinner bayan su tani sun kammala shirya masu abinci a dining hajiya layla tace tazo su ci abinci, tace mata bazata iya ci ba, in har taj bai kawomata Angel din ta ba hankulansu ba karamin tashi yayi ba, gaba aya suka taru akanta suka fara lallashinta suna bata baki duk don su samu su taci abincin amma ta iya, babu wanda baiji tausayinta ba musamman da karfe goma sha aya ta buga na dare, a lokacin ta gama gane karya sukeyi mata, zuciyarta ta karaya a karshe ta fashe da kuka tace su daina boye mata gaskiya, kawai su fada mata ina yarta Angel? Saboda tana ji aranta ba taj bane ya dauke ta, babu wani siyayyar da suka je yi mata duk plan ne .." gaba daya aka rasa wanda zai fa a mata gaskiya saboda fargaban halin da zata shiga, ranta yayi mugun 6aci zuciyarta ta hasala ganin sun zuba mata ido an rasa me magana a cikin su, idanunta suka ka a jawur, zafafan hawaye suka
Chapter 135 · 0% Book details