← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 240 OF 247

Sashe 240

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

bai sanya sunan mahaifinsa ba, basu kawo komai aran su ba, saboda sun yi tunanin ba dagangan ya yi ba. Bayan Ya kammala speech dinsa Mc yace"I'm inviting his wife to give a speech on stage" Tunkan Ya kare maganar Hajiya saratu ta aga murya tace"ai har yanzu bashi da aure, tazuru ne" gaba daya hall din suka kama dariya cikin nishadi, sun sa shi jin kunya. Cike da zolaya Mc Yace"Chief what are you waiting for? Me ka nema ka rasa? Zankadedan saurayi kamar ka, burin kowace ya mace uhm? Ya fa a yana kallon sa, kamar baisan yanayi ba, idanunsa na akan wayarsa da yake dannawa.. "Cikin yan matan nan da suke hauka akanka ya kamata aba daya dama mana" dariya suka sanya, Hajiya saratu tace"He has a fiancee, Insha'Allah, we will soon invite you to his wedding celebration" Gaba daya jama'ar dake acikin Hall din suka sanya shewar murna. Daga Bisani Labulan daya Lullube ke6ataccen gurin da aka tanada saboda Chief ya soma agewa sama a hankali gaba daya hankulan mutane ya koma kan shi Wata katafariyar throne Chair ce da aka kawatata saboda shi, daga gaban kujerar wani hadadden table ne anan aka daura katon cake din da akayi domin sa, mai hawa 10 hada sunan shi a jikin Cake din da wani salon rubutu me jan hankali akayi shi, daga saman silin din gurin an kawata shi da navy blue balloons da steamers, wurin Ya burge mutane, friends dinsa ne suka yi mashi rakiya Ya hau kan kujerar Ya zauna tare da daura kafarsa aya kan aya like a King on his Throne. Minti 30 aka ware saboda baki su samu damar Cin abinci, bayan kowa yaci yasha anyi kullu wash rabu hani'an Mc Ya sa Mawaka suka fara wake Cheif Owais, wakar tayi mashi dadi hatta yan uwansa sunji dadin wakar birthday din da akayi masa. Lokacin da Mc Yayi inviting Yan uwa da abokan arziki donsu fito tsakiyar filin su taka rawa, nan fa suka fara hawa kan dancer floor din cike da nishadi suke taka rawar girma, kowa saida Ya taka In ka cire Mutun daya Mai girma sharafudden da ransa yagama 6aci, Jira yake kawai agama shagalin su shiga family meeting don Ya fallasa abun da ke faruwa tsakaninsa da owais, saboda hakurinsa ya are ya wammace kowa ya ji. Lokacin da aka kusa kammala shagalin, Yan uwa da abokansa suka taya shi Yanka cake, ya 6allo cake din Yaba momynsa abaki, bayan taci itama ta debo ta saka mashi abaki yaci. ya bi Uncle in sa daya bayan daya ya gutsuro cake in ya sanya masu abaki suka ci, ko da yazo kan sharafudeen Saida Ya fara aika masa da harara kafin Ya bashi cake din, badan idon mutane ba da ba abun da zaisa ya ci cake din nan, hakanan ya jure ya bude baki Ya sanya mashi cake din kamar anyi masa dole. Bayan ya gama basu Hindu ta debo cake din ta bashi abaki, shima ya bata abaki, Baba Obie Ya ballo Ya tura masa abaki, kowa ka kalla fuskarsa dauke da farin Ciki banda mahaifinsa. Mintuna talatin da suka rage kafin A kammala Birthday din, photographers suka fara daukar su Hotuna da videos, sai da Chief Ya dauki hoto da kowa daya halarta amma banda mahaifin sa, Ko kusa da shi Ya i bari Yazo, balle yasa ran zai yi hoto da shi. Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, Yan uwa da abokan arzi i sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, bayan kammala addu'ar tashi daga taro da Mc ya gabatar tare da yi ma Baki fatan sauka gida lafiya. *HAJJATY Tana akwance kan gadonta, Ta lullube kanta cikin bargo, Jikinta sai makekketa yakeyi saboda zazzabin daya lullu6eta, duk yadda taci burin ta halarci birthday din Owais, Allah bai nufa ba, Tun safe take fama da zazzabin har magani tasha amma ya i sauka, har kiran layin Pravin ta yi don ta fada mashi halin da take aciki amma bai yi picking call din ba, rabon ta da shi tun bayan kammala sallar asubahi daya leko dakin ta bata ara ganin eyarsa ba. Yan aikin gidanne kadai suka san bata da lafiya, Har abinci suka kawo mata amma takasa cin shi, burin ta kawai taga pravin saboda shi kadai ne zai iya kwantar mata da hankali. ________________FAMILY MEETING "Owais meya ha a ka da Mahaifinka? Meyasa kake zarginsa? wani laifine kake tuhumarsa da shi Ya fada min ba yadda bai yi dakai ba akan ka fada masa amma ka i sanar da shi why pls"? Hateem ne Ya fa a Idanunsa a kan Chief owais dake a tsaye yana fuskantarsa, Suna a cikin dakin Baba Obie. Fuskarsa babu walwala ya furta"zanyi maka bayani anjima" girgiza kai Hateem yayi ransa abace yace"No, Yanzu nake son ji Owais, Dole ka amsa min tambayata idan har ba so kake raina Ya baci ba"! Shiru yayi saboda ya rasa ta ina zai fara kora masa jawabi. "Hateem meke faruwa ne? Har an fara shirin Family meeting bangan ku ba, yanzu nake tambayar kuna ina, auta take fadamin taga shigowarku dakin baba " Sir mubarak ne ya yi maganar yayin da ya ke shigowa dakin idanun shi akan su. Kafin wani daga cikin su Ya furta Kalma suka ji an banko kofar dakin gaba daya suka kai dubansu ga mai shigowa. Mai girma sharafuddeen ne Ya shigo dakin fuskarsa kwata kwata babu annuri, sai huci Yake yi kamar mayunwacin zaki, kaitsaye ya nufi Owais yana karasawa gaban shi, Ya dam o Arm dinsa da arfi Ya fusgoshi Ya nufi kofar dakin da shi... Hankali atashe Hateem da Sir Mubarak suka bi bayanshi suna kokarin dakatar da shi. Bai nufi ko'ina ba sai falon, A lokacin Baba Obie tare da sauran Uncles dinsa da Hajiya saratu duk suna a Falon kowan nan su yana azaune kan sofa, shigowar Shafudden ne Ya aga hankulan su a razane suka mimmike tsaye , cike da rudu suke kallon su.. "Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..." "meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"? Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza mi ewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife asa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa. Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya fa a maka" ya fa a yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya aura min karan tsana, yau wata aya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya fa a...." Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta.. Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa. Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"? "Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla. Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba. Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"? Ya fa a yana kallon chief wanda har lokacin bai ago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa. "Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar.. His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"! Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, " ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka," Pravin da ke arin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su. A fusace Owais Ya mi e tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi. Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun ka a jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba. Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci. Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi. Dakyar ya ha iyi ululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi.. Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"? Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..." a kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana aya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ADDARA ...." Aru e Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"? Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya fa a! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa? Hateem har ya bu e baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da
Chapter 240 · 0% Book details