← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 179 OF 247

Sashe 179

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

idanun shi" Wa'iyazubillah, Tunkan Ya karasa labarta mashi, chief Ya runtse idanun shi saboda fusatar da zuciyarshi tayi tamkar zata tarwatse tsabar bacin rai, bakomai yafi karya mashi zuciya ba face irin azabtarwar da suke yi masu kafin su mayar da su Giant, matasan yaran da basu ji ba basu gani ba, abu mafi muni rashin imanin da suke sanyawa su aikata abun ya munana sosai. wani irin tsantsar tausayin Danish Ne ya ara ninkuwa cikin zuciyarshi, abun ya aga hankalinshi matu la66anshi na rawa ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ya ambaci hakan Yafi sau talatin.. Danish dake kallon shi Ya fahimci matsanancin tashin hankalin da ya ke a ciki. Numfashi ya anja yayin da siraran hawaye suka fara zarya kan kuncin shi.. Cikin raunanniyar murya ya furta"I can't describe the pain I felt in my heart, it saddened me hakika sun cutar da rayuwarku, yanzu da kananun shekarun ka, ahaka suka sanyaka ka aikata duk wadannan abubuwan, Wa'iyazubillah, what kind of disaster is that?" Jinjina kai ya yi "Allah baya barin hakkin wani akan wani, akwai sakayya, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara gir6ar abun da suka shuka kafin su fuskanci mutuwar su.." Danish yayi shiru yana sauraron shi, bawan Allah Ya zama kamar sa ago jikinshi duk babu karsashi shi kadai yasan damuwar dake adabbarsa.. "ka fa amin gaskiya dagaskene bakasan fuskokin su ba? Abun ya tsaya min araina tsawon shekara 20 tun kana jariri harka mallaki hankalinka amma baka ta6a ganin fuskar su ba"? Ya fa a fuskarsa ayamutse yana mai dubashi. "ba sanin su ke banyi ba, nasan fuskokin su amma bazan ta6a iya shaida su ba acikin mutane, saboda suna amfani da karfin sihirinsu gurin canza kamanninsu dama halittar jikinsu shiyasa nace maka bansan fuskokin su ba" gya a kai chief yayi na yarda dakai amma miye sunayen su daka san suna amfani da shi"? "Elder, shine shugaban kurkukun addara, Da iznin sa komai ke faruwa, bayan shi sai mataimakinsa Jan harshe shine mai zartawarwa, na ukun su Jan Wuya shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon Giant, na hudun su Jan Ido shike kula da bangaren safarar yaran da ake kaiwa gidan kurkukun addara.........." Tun daya fara magana Chief Ya nutsu yana sauraron shi har sai da yakai aya kafin yace mashi"Alfarmar da zan nema agurinka, kafin mu kai farmakin Inaso ka dinga bin mu zuwa headquarter donka taimaka ma Isod soldiers din mu da horon yadda zasu yi fa a da Giants.." Amsa mashi yayi da toh sannan ya fa a masa date din daya kamata su je, kamar yadda tsohuwa Khala ta shawarce shi da su kai farmaki adaren ranar, amma bai sanar da shi daren menene ba. Da tsantsar farin ciki Chief Ya ru o hannayen Danish a cikin nashi ya ruke su gam. "Bansan taya zanyi maka godiya ba, kalmomi sunyi kadan Danish, Ka fa amin duk wani buri da kake son cimmawa, Ni kuma na maka al awarin In har baifi karfina ba zan cika maka shi" ya fa a da an murmushi kan fuskarshi, Danish bai furta komai ba, sai faman lumshe idanun shi yakeyi kamar gyangya in bacci ya ke yi. Lura da hakan yasa Chief ya ru o hannayen shi Ya taimaka mashi Ya kwanta kan gadon, wani irin bacci ne mai nauyin gaske yayi awon gaba da shi. (Lallai Gadon Chief Yayi albarka, Unaisah ta kwanta, Ga Danish ma Yayi bacci akan shi saura ni ma zan ana) _________________________________ Da yammacin Ranar, Chief Ya kira Meeting din gaggawa wanda su kayi A headquarter din su tare da Manyan jami'an Isod dana Sojoji, da kuma U.s army, gaba ayan su suka hallara a meeting room insu, bayan Chief ya kunna masu audio in daya dauka na tattaunawar shi da Danish, sunyi matu ar yin mamakin amincewar shi, musamman big guy, sun kuma ji dadin yadda ya basu hadin kai cikin sauki batare da sun sha wahala ba, ba tare da 6ata lokaci ba, kowa Ya fara kawo shawarar shi dangane da yadda zasu kai farmakin, babu wanda bai tofa albarkacin bakin shi ba, basu suka tashi meeting din ba, har saida suka tsayar da kwanan watan da Danish Ya fa a ma chief amatsayin Ranar da zasu kai farmaki. Tun daga ranar su ka fara shirye shiryen tafiya Ya i babu kama hannun yaro, basu da wani hutu, gagarimin shiri suke na musamman kuma komai nasu cikin sirri suke yin shi saboda tsaro ba don tsoro ba, sun tanadi Miyagun Makamai da zasu yi amfani da su agurun gabzawar. Tawagar Dakarun sojoji Uku ne zasu je kai farmakin, tawaga ta farko Isod Soldiers ne, bayan su sai Tawagar Sojojin Nigeria, Tawaga ta uku ta U.s Soldiers ce. a bangaren Unaisah Da Danish tun ranar da ta tursasa mashi akan ya amsa zai basu hadin kai, basu ara ha uwa da juna ba, walwalarsu ta ragu, rayuwarsu ta untata saboda tsantsar damuwar da suka shiga na fargaban kada su rasa junan su, bayin Allah ta ko'ina ba sau i, kokari sukeyi su saba ma kansu rayuwa batare da juna ba don su saukaka ma kansu radadin son juna da suke ji a zukatansu, sai dai abun yaci tura, abun sai ya zamana kamar suna kara rura wutar son da suke ma junansu ne. Ba karamin maraicin shi takeyi ba, saboda shirya shiryen da sukeyi na tafiya ya i yasa baya zama gidan, atare da chief suke zuwa headquater saboda taimakon da yakeyi masu gurin ara wayar masu da kai game da kurkukun addara, Saida takaiga idan Chief yaje da shi headquarter din su jami'ansu ji suke da shi suna masa biyayya kamar dai chief din, wani irin farin jini gare shi, abunda yafi burge su da shi karfin da Allah yayi mashi, ga kaifin basira da Allah ya bashi, har jaraba shi sukayi ta hanyar ha a shi da arfafan Isod soldiers don suyi wrestling da shi, saboda su tabbatar idan giant basa jin bugu aikuwa sun sha ruwan mamaki, Isod Soldiers din da suka hada shi da su gurin damben su kusan hamsin saida Ya sumar da su, a hakan ma baiyi masu bugun da zasu raunata ba saboda baison yai masu illa shiko ko kwarzane ba su yi ma shi. Idan suka tafi Basu tashi dawowo gida, sai marece idan ya dawo agajiye daya samu yayi wanka ko abinci bai nema bacci yake yin awon gaba da shi, baya tashi farkawa sai lokacin da dare ya tsala kowa yayi bacci tukunna ya ke tashi yaci Dinner din shi. dauriya kawai yakeyi amma kewarta na neman tayi mashi illa, haka itama ko abincin kirki bata ci, ta rame tayi haske sosai kamar babu jini a jikinta, kullum a bedroom insu take killace kanta bata son kowa ya ra6e ta, tafi son kadaici duk da ba karamin azabtuwa takeyi ba na rashin ganin shi, tun tana 6oye abun da ke damunta idan yan uwansu suka matsa mata musamman auntyn umminsu har takaiga sun gano da kansu saboda kauracewa junan da sukayi ita da Danish, nema take ta zauce kullum ciwo ba koshin lafiya, abinci sai aunty ummi tayi mata dole take cin shi akarshe ma ta amayar da shi a toilet ba tare da sanin su ba, bacci Ya kaurace ma idanunta idan dare yayi haka zatay ta juyi kan gado rungume da pillow a kirjinta, idan abun ya isheta nafilfili take tashi tayi kuma duk akansu takeyin sallar, wani lokacin akan prayer mat baccin ya ke yin Awon gaba da ita. wannan wani irin Azababben So ne Gaba daya abunda ke faruwa Taj baisani ba, saboda shima ba zaune ya ke ba, ummi har yunkurin kiranshi tayi don ta fada mashi halin da Unaisah take a ciki na rashin Lafiya amma Unaisah ta dinga rokonta akan kada ta sanar da shi saboda gudun fa an da zaiyi mata, dakyar ta samu Ummi ta fasa kiranshi bayan ta gindaya mata sharadi akan bazata ara fashin cin abinci ba, tace mata eh ta amince ahaka ummi ta samu ta an shawo kanta. Kamar yadda boyayyan mutumin nan Ya ba Chief shawarar su sanya manyan Malaman addini suyi masu addu'a, bai yi asa a gwiwa ba, ya tuntu6i shiekh Imam malik awaya, Ya nemi alfarmar yana son su ha u anan gidan shi. Shiekh imam yace mashi in sha Allah zai shigo gidan. After Magbrib Bayan sun kammala yin dinner din su, ba suje sun kwanta ba, gaba ayan su suna zaune a falo, sunyi shiru babu mai magana acikinsu, kwata kwata babu annuri akan fuskokin su, gashi dai sun sanya kayan baccin sai dai baccin Ya kauracewa idanunsu saboda damuwar da zuciyoyin su suka shiga, babban tashin hankalinsu jin za'a tafi da Garkuwarsu, babu irin magiyar da basuyi ba akan suma atafi da su amma Salsabeel yace bazai yiwu ba, suyi hakuri su biyu sun isa suyi ma Sojojin jagora. Unaisah ta wallafa rai akan son aje da ita kuma har yanzu tana akan bakanta don bazata bari su tafi da Danish batare da ita ba, abun daya daure masu kai har yau babu wanda ya fa a masu date din da zasu je kai farmakin, duk in suka tambayi Taj ko big guy sai suce masu basu fidda lokaci ba, haka shima Danish yake fada masu, gaba daya sun yarda da maganarsu, Unaisah ce kadai hankalinta bai kwanta da zancen in bayyana masu kwanan watan ba, ta fahimci sun ha a baki ne, ranta yana bata tafiyar bazata zasuyi batare da sanin su ba shiyasa suka shirya hakan, tun da ta fahimci hakan kusan kullum sai ta addabi daddynta da Salsabeel akan su fa a mata date in amma suka iya, tayi magiyar tayi rigimar duk abanza, harta hakura tadaina tambayar su, ta dai zuba ma sarautar Allah ido. Fitowa Ummi tayi daga Bedroom dinta, jikinta sanye da doguwar rigar bacci, ta zuba hannayenta cikin aljihun rigar, Daga inda take ta hango su zazzaune kan sofas na falo, sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki. Girgiza kai tayi tare da zaro waya daga aljihu ta kira Layin Boss. Bayan yayi picking suka gaisa cikin girmamawa kafin tace"yalla6ai akwai matsala fa, Yaran nan sun i zuwa su kwanta ga su
Chapter 179 · 0% Book details